Yana shiga ya hango ta zaune kan gadon bayan ta jingine da fuskan gadon ta d'aura kanta kan gwiwowin k'afan ta da alama kuka take, tausayin ta ne yayi bala'in kamasa amma ya moze.
     K'arasawa jikin gadon yayi ya tsaya yana Kallon ta, ganin har lokacin batayi noticing shigowan sa ba ya kai hannu ahankali ya tab'o ta, a firgice ta d'ago jin saukan lallausan hannu a kafad'an ta ganin shine ta sake ajiyan zuciya feeling safe and relieved.
Ganin fuskan sa babu annuri tayi saurin kawar da kanta tana mamakin laushin hannu irin tasa wane na jariri.
        " Amsa kije ki sanya, kuma karki yarda kisa ruwan sanyi ajikin ki " yayi maganan yana kallon wrist watch nasa.
       Mik'a Hannu tayi ahankali zata karb'a, mistakenly hannu su ta had'e na sosai hakan tayi affecting su amma kowa bai bari d'an uwan sa ya fuskanci halin daya shiga ba, ajiye mata yayi yai saurin zaro hanky yana wiping inda hannun ta ya tab'a cike da kyankyami.
Ji tayi wane ta had'iye zuciya saboda takaici dan ta k'ona masa rai itama ta mik'e dan yaga yadda tayi staining dan sosai ganin jini ke d'aga masa hankali, da sauri kuwa ya d'auke kan sa zuciyan sa na some tashi.
       Ahankali ta shiga takawa kaman hawainiya saboda neman tsokana, ganin hakan Suwayd ya buga mata wani shegen tsawan da ba shiri ta tsinci kanta acikin toilet d'in.      
Warm wata tayi using ta gasa kanta sannan ta d'auka pant d'aya cike da mamakin yadda akayi yasan size d'inta ta had'a da pad ta saka, rigan ta d'auko ta sanya taje gaban k'aton mirror dake toilet d'in tana jujjuyawa happily yanda rigan ya kamata ta sama ya bud'e ta k'asa yafi komai burge ta, nan take k'aunan rigan ya shige ta.
      Kayan ta data rasa yadda zatayi dasu ta soma d'auraye wa, gajiya yayi da jiranta ya k'araso bakin toilet d'in a masife yace " wai uban me kikeyi aciki ne? "
" Ina zuwa Ya Suwayd na kusa gamawa " ta fad'a da d'an ihu yadda zai jiyo ta.
       " Ba wannan na tambaye ki ba stupid girl just answer my question ".
" Kayan dana cire nake wankewa " ta fad'a finally.
      " What? ke wai baki da hankali ne? Wait ma kina tunanin zaki sake sanya wannan najasassun kayan? Gaskiya da kin tabbata Miss world k'azama, dallacan fito kafin na shigo na b'ab'b'ala ki banza good for nothing kawai ".
Fitowa tayi rik'e da ledan ragowan kayan daya siyo kanta a k'asa saboda kunya, kallon ta ya tsaya yi totally out of word ganin yadda tayi masifan kyau, nan take jarababben kishin sa ya motsa ganin mayafin rigan d'an k'arami, d'agowa take son yi dan jikin ta yabata kallon ta yake yi amma ta kasa. 
       Wawan tsaki yaja yace ta wuce su tafi, ba tayi musu ba ta shige yana binta a baya suka fice daga office d'in.
Cillawa Dr key d'insa yayi yace " thankyu and make sure an Yasar da kayan dake toilet please ". 
       Dirty glares ya masa sending cike da takaici ya bud'e office d'in sa ya shige.
Duk inda suka gifta sai an kalle su dan yadda suka yi mugun dacewa har suka isa parking space, da sauri ya bud'e musu suka shiga ya bawa motan wuta, yayi niyyan mata shopping amma kalle masa ita da akayi yasa ya fasa yayi leading nasu gida.
     Horn yayi gate man ya bud'e musu suka shiga, yana gama parking ya jingina da kujeran sa ya lumshe ido.
Bud'e k'ofan ta tayi ta zura k'afafun ta har zata fice sai ta juyo kai a k'asa cike da kunya tace " nagode " daga haka ta fice tayi cikin gida.
      Like a fool ya rik'a nanata nagode shi kad'an sa yana murmusawa,,ganin ba mahalicci sai Allah ya fito shima ya wuce part d'in su, yana shiga toilet ya wuce yayi wanka ya d'auro alwalan magrib dan lokaci yayi.
   Na sosai tasha tsokana gurin su Kadsah wai sai tayi musu bayani ya akayi yasan size d'in ta,,,koda lokacin dinner yayi k'in zuwa tayi saboda kunyan sa yayin da shikuma yake can duk ya damu bai ganta ba yana tunanin ko ciwon ne, bai wani ci abincin kirki ba ya tashi ya wuce part d'in su ya d'auko alluran ta ya wuce part d'in Granny.

Tana gama cin abinci ta shige d'akin su ya shigo, ganin bata falour'n kai tsaye ya wuce bedroom d'in su, nanma bata nan amma jiyo k'aran ruwa da yayi a toilet ya shaida masa tana nan.   
     Gefen gadon ya nema ya zauna yana jiran ta, bata wani b'ata lokaci ba ta fito inda tayi turus ganin sa zaune yana daddanna waya, Allah yaso ta this time around da hijab ajikin ta data sha wani wulak'ancin.
       Sunkuyar da kai tayi tana wasa da 'yan yatsunta lokacin daya d'ago ya kafeta da ido, sai da ya gama k'are mata kallo yayi faking tarin munafinci irin ganin ta da yayi ahaka disgust him, " kin san lokaci na bana b'atawa akan shashashu irin ki bane dan haka kizo na miki na tafi inada abinyi ".
K'in motsawa tayi gano allura a hannun sa dama haryanzu ma bata gama warkewa daga na d'azu ba, " dake fa nake magana " ta sake tsinkayo voice nasa.
    A shagwab'e tace " Ya Suwayd Allah na warke a barshi haka banaso ".
" Sai akace miki dan bakyaso zan kyale ki? To bari kiji wallahi tunda na shigo ko zaki mutu sai nayi miki ".
    Tunda taji ya rantse ta soma neman mafita, ganin da 'yar tazara a tsakanin su tayi saurin juyawa zata koma toilet d'in dan harga Allah tsoron alluran take, murmushin gefen baki ya saki dan ya fuskanci what she is capable of doing, taku d'aya yayi ya damk'o ta, du kalan magiyan da rok'on da take masa baisa ya sake ta ba sai da yayi mata, k'ank'ame sa tayi tana kuka sosai kaman wadda aka zarewa rai yayi saurin tureta ya fice dan shi kad'ai yasan mai yake ji .
    Dakyar ta mik'e ta sanya kayan baccin ta tabi lafiyan gado, batare da b'ata lokaci ba kuwa tayi falling into a beautiful sleep.

MAKAHON SO _Blinded Love_Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt