Sai bayan sallah'n isha suka dawo Sayyid ya dafa musu had'ad'd'iyar jalof ta spaghetti suka ci, basu wani zauna hira ba saboda monday gobe suka wuce suka kwanta.

*The following day*
Zee ta matuk'ar yin kyau sai dai kallo d'aya zaka mata Kasan tana cikin damuwa, lectures nata na ranar ma kawai sai imani dan bata fuskanci komai ba.

And same goes to Ammar dan gaba d'aya attention nasa na kanta, Allah_Allah yake luctures su k'are ya tambaye ta damuwan ta duk da yasan ko mutuwa zaiyi barata fad'a ba.

Haka dai har suka k'are lectures d'in su na ranar, ahankali cike da nutsuwa da kamala take tafiya tana k'ok'arin gujewa Ammar dan haka kawai ta tsinci kanta da son bin umarnin Suwayd, dan sam batason abinda zai b'ata masa rai.

Cikin sand'a ya k'araso bayan ta without any noticeable sound, ahankali ya mik'a hannu ya zame littafin dake hannun ta chak ta tsaya ta jiyo ahankali cike da tsananin b'acin rai, hannu ta d'aga da niyyar wanke sa da mari ta hango Suwayd yana nufo su.

Gyara hannun tayi saurin yi tayi kaman ta shammaci Ammar d'in ne tanaso ta kwace, sama ya d'aga dan yasan barata iya kwata ba.

Bubbuga k'afa ta somayi a shagwab'e tace " please ka bani na tafi ".
    Mak'ale kafad'a yayi ya sake d'age littafin sama, d'an tsalle ta somayi tana son kwacewa amma sam ta kasa shikuma sai dariya yake mata, sai da ta gaji sannan ta tsaya tana maida numfashi ta rik'e k'unk'umin ta dan sosai ta gaji, ba kuma komai yasa tayi hakan ba sai son tabbatar wa da take shin Suwayd kishin ta yake ko kuma bayason ayi dumping inta kamar yadda ya fad'a wancan ranan.
     
    Cike da tsananin azababben bala'in kishin da ya kasa b'oyuwa Suwayd ya k'araso gurin, zuciyan sa banda tsananin tafasa da zugin bak'in ciki ba abinda take, fizge littafin yayi with all that he got ya cilla mata.
   
Juyowa Ammar yayi dan ganin wanda ke k'ok'arin ruining musu happy moment, Suwayd daya tsani ganin fuskan sa nan take yaci kwalan sa ya bashi wasu kyawawan punch aciki, na sosai suka shigesa amma sam baiyi attempting ramawa ba dan bayason hurting ta sai ma wani kyakkyawan murmushi daya sake dan bazai iya ramawa ba tunda ta nuna rashin amincewar ta a wancen lokacin, shikuma duk abinda bataso yana kiyaye wa saboda sonta da yake.

Murmushin da yake ne yasa ke k'ular da Suwayd ya sake basa wasu azababbun punch d'in gaba d'aya idon sa ya rufe baijin akwai wanda zai hanasa illata wannan bloody bastard d'in, punch kawai yake sake masa amma bayida niyyar ramawa sai kallon Zee dake wani irin kuka mai tsuma zuciyan mai sauraro.

Runtse ido yayi dan bazai iya jure ganin kukan da take ba, sam bayajin zafin dukan Suwayd kaman yadda yake jin zafin zuban hawayen ta a dalilin sa.

Ba kalan magiyan da batayi wa Suwayd ya bari ba amma yak'i da tayi k'ok'arin rik'esa ma tura ta yayi har saida ta fad'i ta saki k'ara dan sosai ta bugu a k'unk'umin ta, alokacin ne Ammar yayi wa Suwayd had'ad'd'iyar punch daga ita kuma bai sake samun dama ba dan yadda Suwayd yayi masa jina_jina.

Sosai student suka taru kallo amma dan yadda suke shakkan Suwayd sun kasa aiwatar da komai, ganin Suwayd na k'ok'arin kashe d'an mutane tayi saurin rik'e hannun sa na dama da both hannayen ta.

Juyowa yayi kanta a masife ya fusge hannun sa ya wanke ta da jarababben marukan da saida jin ta ya gushe na d'an lokaci.

Fincikota yayi ya mik'ar ya kalli students d'in da suka taru cikin k'unan zuciya ya nuna ta yace " gata nan Allah ya bawa mai rabo sa'a wallahi, wallahi ko a matsayin friend nagan ka da ita I won't spare you dan i will make sure ka kwanta jinyan da ko uwarka da ubanka bara ka shaida ba, duk kuma d'an shegiyar da zai gwada ya gwada ke kuma kinga kad'an daga cikin abinda na tanadarwa duk wanda yayi ganganci ko kuskuren rab'an ki, sai ki shiryawa tarban tashin hankali matuk'ar baki kiyaye abinda na fad'a miki ba stupid bitch kawai " ya finciki hannun ta tana turjewa tana komai yabar wajen da ita.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now