D'ayan hannun sa ya had'e da d'ayan nata yayi wearing sad face sannan in a husky like voice nasa ya soma magana " God forbid Ummy dan Allah ki daina ma kawo wannan jakan yarinyar i 'ave nothing to do with her, she is just like a piece of trash to me and nothing else, ni yarinyan ma da nake so batama san inayi ba and duk sanda na kalla cikin idanun ta bana hango komai sai tsananin tsanata da take, Ummy Allah in bansame ta ba mutuwa zanyi kuma zan iyayin komai just naga na mallake ta kota halin k'ak'a saboda dani kad'ai ta dace, amma abin haushin shine yadda ta tsane ni haka ta tsani mutuwan ta ni kad'ai nasan yadda nake ji Ummy ki taimaka min " ya k'arasa maganan yana tears.

Sosai hankalin Ummy ya tashi ganin yana tears tasan duk duniya mawuyacin abu ke Sanya sa kuka lallai ba k'aramin so yake wa yarinyan ba tunda harya zubar da hawayen sa akan ta.

Ahankali ta sa hannu tana wiping mar tears d'in sannan ta soma magana " amma Son sai nake ganin kaman alhakin Zee d'in can ke bibiyar ka just kwatanta kai namiji so na wahalar dakai haka balle ita na mace, du kalan abinda kakeji ta linka ka tunda kai namiji ne zaka iya trying as much as possible ka danne ita fa? Do you think is easy for her?  Now just assume Safwah ce tayi falling ma wani yake wulak'anta ta haka will you feel good, nasan baraka tab'ajin dad'i b..... "

Ganin yadda duk wani annurin fuskan sa ta kau yasa ta yin sai sannan ta tuna sunan mak'iyar sa ta ambata, shikam bak'in kishi ce ta tokare sa jin Ummy tayi comparing *Flower Queen* tasa da wani bashi ba.

Saurin changing musu topic tayi " karka damu Son nasan itama tana son ka kawai dai tana ja maka ajine, but believe da kanta zata ce tana son ka ".

Kansa ya shiga kad'awa yace " no Ummy barata tab'a cewa tana so na ba, gashi duk yanda naso nayi confessing mata feelings d'ina na kasa ".

" Worry not dear ni jikina ma yana bani ita d'in taka ce za kuma ka same ta, kai dai ka dage da addu'a sannan ka rage abinda kake yiwa Zee saboda itama ba laifin ta bane and yanda kake suffering d'in nan na tabbata ta fika ".

Shiru yayi dan shi baya son zancen Zee d'in nan da Ummy keyi, duk conversations nan tasu a kunnen Granny dan ta shigo taji suna maganan ta kuma san wa Suwayd yake nufi.

Murmusawa tayi a zuciyan ta tace " wato dan iskanci yazo ya samu maman yarinya ya linke ta bai_bai " sannan tayi musu sallama ta shiga.

Gaida ta Ummy tayi sannan Suwayd ma ko answering batayi ba ta soma yiwa Ummy fad'a ganin haryau d'in tak'i zuwa ta duba jikin Safwah.

Rai a b'ace ya mik'e daga cinyan Ummy yace " yanzu dan Allah saboda wannan yarinyar za'a zo a d'aga mana hankali ni wallahi harkin sa Kaina ma ya soma ciwo ".

Ya mik'e ya fice ita Granny  ma dariya yake bata sometimes in yana d'an iskan pretending nasan.

Duk yadda Ummy taso Granny ta kyaleta tak'i dole ta mik'e suka tafi tare.

*****
Lokacin da Zee ta farfad'o k'in kula kowa tayi sai binsu da ido, duk yanda suka so tayi magana tak'i dole suka kyale ta dan in aka takura mata kuka take sanya wa.

Sai da tayi kwana uku ahaka a kwana na hud'un ne ta tada hankalin kowa sai an sallema ta, ganin abinda take bana hankali bane yasa akayi discharging nasu.

Kaman ba ita ba duk ta rame suna isa gida wayan ta tasoma d'auka ta shiga turawa Suwayd sweet love masaages masu tafiya da imani.

Abinci kam tunda ta kwanta jinya ta yayewa kanta cin sa sai yau da Mummy ta Sanya ta agaba tana kuka sannan taci kad'an.

Washe gari tunda asuba ta soma shirin school duk da bata gama dawowa dai_dai ba.

Sam kuwa Daddy'n ta yace babu inda zataje dan yasan akan Suwayd ne take rawan k'afan taje school d'in.

Bore ta shiga yi musu ganin hakan ya sanya ya barta cike da tausayin ta, shi da yasan asibitin da zai kaita a cire son daya kaita sai dai shi so *MAKAHON* abune sauk'in shiga gare sa wurin fita kam sai anci wuya.

Ganin ta fita da wuri yasa tace da driver'n ta ya fara kaita *SAHAD STORE*, had'ad'd'un love cards ta siyo da Flowers masu mugun kyau sannan suka wuce school d'in.

Lokacin da go slow ya tare su kaman zatayi kuka dan tasan duty'n Suwayd ne zai iya mata fiye da abinda ya Mata ranan da taje gidan su.

Acan school kuwa tunda Suwayd yaga 7:50 am k'awar Zee bata zo ba ya fito daga class ya tsaya a gate dan yau yad'au niyyan koya mata hankalin da bara ta sake masa kallon banza ba balle har akai tsaki.

8:00 am kuwa ta shigo da alama ba asan ranta ta makara ba, idon ta bai sauka ko ina ba sai kan Suwayd dake tsaye ya sanya hannayen sa cikin aljihun wandon sa fuskan nan sam babu annuri.

Wuce sa tayi niyyan yi yayi stopping nata sannan ya nuna mata wani garbage da yasa yara suka tara meaning ta gyara.

Kallon rainin hankali ta bisa dashi tayi gaba abinta, sai ji tayi ya fusgo hannun ta yana waina wa cike da mugun ta duk yadda taso kwatan hannun nata ta kasa ga attention na juniors nasu da sukayi late duk ya dawo kansu.

Sai da yaga idon ta ya ciko da kwalla sannan ya sake mata hannun ya sake nuna mata abinda zatayi amma taurin kai ya hana ta yi.

Saukan mari Kawai ta jiyo a fuskanta, cike da k'in yardan abinda ya faru ta d'ago tana kallon sa, ganin yana k'ok'arin cire belt tasa yasa tayi abinda yasa ta tayin tana ji wane ta mutu dan tak'aici.

Juniors nasu sai dariya suke dan ba laifi ita ma tana d'ana discipline.

Zee da komai a idon ta ya faru tuni jikin ta ya soma rawa dan tasan ita ma nata na nan yana jiran ta.

Dakyar ta iya ta k'araso inda suke, wani makirin murmushi Suwayd ya sake yace da Zee " *Sweetheart* why are you late? "

Jin saukan kalman tayi har tsakar ka da sauri ta d'ago tana kallan sa du da tasan ba har zuciyan sa yake fad'a ba har lokacin kuma murmushin bata b'ace daga fuskan sa ba, dakyar ta samu ta nemo excuse ta basa ta dau ma bazai yarda ba amma sai taga akasin haka.

Hanyan class ya nuna mata ta wuce sannan shima yayi joining nata suka jera a tare dan ya gama abinda ya kawo sa gurin.

With so much adoration suka nufa class yayin da Zee keji wane an tsunduma ta a aljanna, wani mugun so da k'aunar sa ne suka sake huda zuciyan ta suka shige, har aka tashi tana cikin farin ciki duk wani rashin lafiya ta neme sa ta rasa.

Sosai 'yan gidan su ma suka sha mamakin ganin ta dan sun d'au ganin akasin hakan.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har lokacin exams nasu yazo.

Alhamdlillah sun fara lafiya sun kuma k'are lafiya sai shirye_shiryen party da zasuyi ake.

Ta fannin muguntan Suwayd wa Safwah sai abinda ya dad'u haka ma Zee wataran ya Mata kirki wataran kuma ko kare ya fita daraja a gurin sa.

Safwah taji sauk'i sosai dan yanzu babu abinda batayi da hannun ta school kuma tun Suwayd na *WAEC* ta koma.........

  _kuyi hak'uri da wannan guys bana jin dad'i ne amma innaji comments zan muku wani post d'in to nyt, much love angels_

MAKAHON SO ~Blinded Love~
#MS

*'Yar Gatan Miss_B_Hal Ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now