Kallon Sadeeyq  Mammy tayi tace yaje ya shigo dasu Mummy, with nod ya amsa ta ya fice.

A reception ya iske ilahirin Alhaji Muhammad Ibrahim Agadez family members ko wannen su d'auke da d'umbin damuwa Suwayd ne kawai babu aciki directing  nasu yayi zuwa d'akin.

Da sallama suka shiga d'agowa Mammy tayi tana kallon su d'aya bayan d'aya totally out of word dan ganin babu Suwayd.

" Lallai dole ta dage da addu'a dan tana tantama in babu shafan aljanu ajikin sa, amma ta yane zaiwa yarinya irin wannan aika_aikar ya kasa zuwa duban ta tabbas he must pay for all what he has been doing ta k'arashe kalamun zucin nata sannan ta shiga welcoming su Granny.

Ana kiran sallan magrib Safwah ta farka, a time d'in harsu Granny sun tafi kasantuwar hospital d'in basa son tara mutane.

Tunda ta farka ta gaza furta ko wani kalma dan yadda hannun ta ke tsananin zugi da ido kawai take bin Mammy dake sallah.

Tana k'aunar Mammy har cikin ranta, yayin da kuma gobaran tsanan d'anta ke sake ruruwa a zuciyan ta, wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo mata sakamakon wani irin sharp pain da yayi hitting nata.

Tun tana daurewa har ta gaza ta fashe da wani irin masifaffen kuka, wanda hakan ya sanya Mammy saurin idar da sallan ta ko addu'a bata samu tayi  ba.

Na sosai ta tausayawa Safwah dan ganin yadda take murza kanta kan pillow'n da take, d'ayan hannun ta kuma sai yarfa shi take hakan ne zai tabbatar maka ba k'aramin azaba takeji ba. 

K'arasawa tayi jikin gadon ta zauna sannan ta jawo kan Safwah ta d'aura akan cinyar ta sannan ta shiga aikin rarrashi which dakyar ta samu ta shawo kanta tayi shiru.

" Where is my Ummy? I really want to see her Mammy call her for me " ta fad'a da muryan kuka.

" Am sorry Baby sunzo kina bacci ki bari gobe zata zo " Mammy ta fad'a da muryan rarrashi.

" No Mammy am dying please call her right now, jikina na bani bazan kai go..."

Da sauri Mammy ta taushe mata baki tana girgiza mata kai " No Baby cuta ai ba mutuwa bane stop saying such word " Mammy ta fad'a a d'an kid'ime dan seta ke gani kaman abinda Safwah ke fad'a ne zai faru.

Sayyid daya shigo ne yasa su kallon k'ofan atare, murmushin k'arfin hali ya sakar wa Safwah sannan ya k'araso ciki, har k'asa ya duk'a ya gaida Mamy sannan ya ajiye ledojin daya shigo dasu a gefe.

Ringing wayan Mammy ne yasa Sayyid kai duban sa kan dadduman da ta tashi, Sweetheart shine sunan da tayi appearing a screen d'in murmusawa yayi dan yasan Abbah ke k'ira sannan ya d'auko ya mik'a mata.

Kwantar da Safwah tayi sannan ta fita a d'akin, Sayyid mai jiran k'iris tana fita yayi replacing position nata.

K'in kallon sa Safwah tayi ta juyar da kanta d'ayan side d'in, juyin duniya amma tak'i juyowa sai kuka take hakan kuma ba k'aramin tada masa hankali yake ba.

Kaman zaiyi kuka ya shiga rok'on ta inda ta sake fashe wa da wani matsanancin kula.

Ahankali ya d'ago kanta daga kan   pillow'n ya aza akan cinyar sa sannan ya fara magana ahankali.

" Love is always patient and kind. It is never jealous. Love is never boastful or conceited. It is never rude or selfish. It does not take offence and is not resentful. Love takes no pleasure in other people’s sins, but delights in the truth. It is always ready to excuse, to trust, to hope, and to endure whatever comes, Safwah my heart only beats for you,  about such words you said to Mammy earlier bana so in k'araji ko kin manta promise namu sai munyi aure mun haifi princess mai kama dake munyi rising nata sannan mutuwan zai d'auke mu a tare, ko kin manta da promise namu na living together till death, please Baby ki dena irin maganan nan banso ".

Tunda ya fara magana take kallon sa with so much adoration duk da kasancewar bata san mene so ba amma tasan irin matsanancin son da Ya Sayyid yake mata, itama kuma tana sonsa don batajin zata iya rayuwa idan babu shi.

*, *, *,     *, *, *,     *, *, *,     *, *, *,

Suwayd zaune a reception ya had'a kai da gwiwa yana tunanin hanyan da zaibi yaga halin da Safwah take ciki, dan yasan ko sama da k'asa zasu had'e Mammy bara ta barsa ya shiga ba.

Gashi ya riga yayi promising kansa no matter how difficult it takes sai yaga Safwah.

Kaman an mintsine shi ya d'ago inda yayi kyakkyawan gani dan a lokacin ne Mammy ta fita. 

Jikin sa har rawa yake saboda tsananin farin ciki, batare da b'ata lokaci ba ya nufi d'akin sannan ya rik'e handle d'in ahankali ya tura.

Abinda kunnen sa ya jiye masa ne ya hanasa k'arasawa ciki, tuni zuciyan sa ya shiga wani irin suya yayin da wani bala'in kishi ya tokare shi.

Tuni numfashin sa ya shiga kai komo, " I Love you so much Ya Sayyid , When I tell you “I love you” I don’t say it out of habit or to make conversation. I say it to remind you that you’re the best thing that has ever happened to me and insha Allah our dream will come true dearie na".

" Iyeeee ashe haka Baby na take lover girl " Sayyid ya fad'a cike da neman tsokana.

Rufe idanun ta tayi cike da kunya sannan ta turo masa d'an k'aramin bakin ta tace " Allah bana so ".

Dariya suka sake cike da burgewa, " BAMMMMMM!!! " sukaji anyi banging k'ofa da k'arfi...........

MAKAHON SO ~Blinded Love~
#MS

*'Yar Gatan Miss_B_Hal ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now