Murmushi yayi yace " as you can see am fine buh busy with my books ".

" you such a goodboi keep it up ehen " ya fad'a yana nufan d'akin Ummy, ahankali ya murd'a handle na k'ofan yayi sallama Sai da tamasa izini sannan ya k'arisa ciki hugging ta yayi ta baya yana mata sannu da gida then ya shiga tayata shirya kayan da take acikin cupboard, sunayi suna Hiran su irin na d'a da uwa cike da nishad'i har suka kammala.

Sai sannan Ummy tace yaje ya huta mik'ewa yayi cike da k'aunar ta ya tafi ya nufa site nasu.

*******
" Sis yau bakisan abinda guy na yamin a school ba " Zee ta karisa kalamun ta tana cire uniform nata.

Mik'ewa MieMie tayi tace " mai kuma ya miki? "

Allah sarki Zee she has no option than ta fayyace wa 'yar uwar ta duk abinda ya faru and a yarda take nuna ma MieMie bataji wani haushi ba saima farin cikin da take ta samu albarkaci ya tab'a handkerchief nata wanda scent of perfume na Suwayd take mak'ale ajiki.

A masife MieMie ta mik'e daga kwanciyar da take idon ta ya cika da b'acin rai cikin rawan murya tace " Sis for heaven's sake yau shane zaki dena wahalar da kanki dama zuciyan ki baki d'aya since when kika zama low class haka ban sani ba? Wait ma kina nufin bawani action da kika d'auka? "

Murmusawa tayi tace " MieMie kenan you will never understand, how on earth will you even think of nama Suwayd kallon banza bare something makamancin haka, you know ko wani naga zai masa sai inda k'arfi na ya k'are and you here saying wani action na d'auka, wani action kuwa zan d'auka bayan sansa da k'aunar sa da ya sake linkuwa acikin raina and please idan baraki na fad'ar good about him ba let's not even talk about him if not I might end of doing something stupid which at end we will all regret it ".

Wasu zafafan hawaye ne suka kwarinyo wa MieMie da gaske take tausaya mawa 'yar uwar ta a kullum addu'an ta bai wuce Allah ya yaye mawa yayar ta wannan *MAKAHON SO'n* da take wa Suwayd ba, dakyar ta numfasa tace " but Sis at least you have to show him what he did is isn't good, kinga nan gaba he might not think of doing such crazy act of his ".

" Kema dai kinsan that is impossible, dama dai ace kene yayi wa da I will gather all mah strange and talk to him buh ni ya yiwa I don't see the reason why miji yayi ma matar sa hukunci ya zama big deal " ta karisa kalamun ta tana kallon MieMie da ta sake baki da hanci tana kallon ta.

" Miji! Miji fa kika ce you bastard better go back to your normal sense cause har idan Ina raye haka bazata tab'a sab'uwa ba " MieMie ta fayyace mata iya gaskiyan ta tamik'e dan matuk'ar ta cigaba da sauraron 'yar uwar tata they might end of doing crazy act's.

Mummy da duk conversation d'insu a kunnen ta ya k'are ta share 'yar kwallan daya tara mata a ido na tausayin Baby'n ta tajuya ta tafi, ta sani Zee tun bata san kanta ba Allah ya jarabce ta da son Suwayd to why not shima ya tausayawa d'iyar ta ya sota ko kad'anne? gashi tun tana abu na hankali ta fara wanda dole mutum yaji lallae ya fara tunanin she don't have common sense.

" Ya Allah ka dubamun rayuwar 'yata " ta fad'a a zuciyan ta.

Aranar kam saida ya kai ya kawo Zee da MieMie sun daina magana dan Zee ta kasa lamuntar tsanar da MieMie ke nunawa freely akan Suwayd.

******
Ummy ce ta fito ta tarad da Safwah na shiriri tanta data saba ta ajiye teddy nata akan kujera ta d'aura mata littafi da biro a cinyan ta she is just acting as how Ya Suwayd act idan sunje assignment earpiece ce mekyan gaske a hannun ta sai tsule teddy'n take ita bata yarda ba tana mata hukunci a bisa ta kasa assignment d'in, sai tayi using voice nata tana apologizing sai kuma tayi copying na Ya Suwayd tana kalan masifan sa da yake musu.

Juyowan da zatayi blue eyes nata ya sauka acikin na Ummy wanda ta kasa fassara a wani hali Ummy'n nata take, k'arisowa tayi gurin Ummy'n ta tsuguna ta kama kunnen ta dan inhar tayi laifi wannan hanyan take bi tayi apologizing koma waye ta b'atawa rai, ganin Ummy'n still ita take kallo kuma ta k'iyi mata magana yasa hawaye suka fara kwarinyo a kyawawan blue eye nata wanda zuwa lokacin suka fara chanza launi saboda tsabar rud'u, ahankali tasa hannu ta d'ago ta wanda har a lokacin ta Gaza furta ko wani irin kalamu sai kallon da take mata sending.

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now