" Are you sure you did it right? " ya jefo mata tambayar fuska a d'aure.

Nodding kanta tayi alamar Eh, saukar Marin dataji ne yasa ta remembering ba'a yi masa talk da body language, " yes am sure " ta fad'a tana tears dan sosai marin ya shige ta, gurin daya mare ta kuwa tuni yatsun sa suka fito rud'u_rud'u kasancewar ta fara.

Duba littafin yayi ya cilla mata a fuska, cikin d'aga murya yace " What kind of nonsense is this? Is this how I teach you huh? "

Shiru tayi jikin ta sai rawa yake hawaye kuwa kamar an bud'e lalataccen tap, ita dai tasan yarda ya koya musu tayi sai dai in he is up to something.

" Answer me is this how I teach you? " ya sake tambayar ta harshly.

Da sauri tace " No please sorry Ya Suwayd, don't beat me I will correct it ".

" Oh no wonder,  kina sane kikai min  wannan haukan kenan?  Good you must answer me ".

Hango Kuwaysah yayi sai kuka take, ai kuwa ya dawo kanta " Ubanki nayi miki kike min kuka? "

Shiru tayi not ready to talk, hakan kuwa ba k'aramin hasala shi ya sakeyi ba,  " yau zanga k'arshen iskancin ki, koma can side d'in " yayi mata pointing kusa da Safwah.

Kallon Lubna yayi da take shirin yin kuka yace " Wallahi karki yarda Kimin kuka if not saina lahira yafi ki jin dad'i ", tuni ta had'iye kukan ta, ita dama ba komai yasa take shirin yin kukan ba sai ganin Safwah ma tayi solving yace ba dai_dai ba, to sufa!!  Suda they are not fans of mathematics, ai kawai su shirya wa kabarin su.

" Uwarki kike kallo a fuskata? " ya watsowa Samha tambayar a tsawace, kawar da kanta tayi dan ita sam yanzu bawani tsoron shi take ba tunda ba shekaru da yawa ya bata ba, kamar yarda ya bawa su Safwah ba.

" Banza dak'ik'iya tun kina k'aramar ki kin iya kallon cikin idon namiji ko?  Zaki gane kuran ki lunatic kawai " Samha daurewa kawai take dan da halin tane rashin kunya da saita nunawa ya Suwayd ba tsoron shi take ji ba, dan sosai kalaman sa suka tab'a mata zuciya.

" Time up duk wadda ta k'ara koda one word sai ranta ya b'aci, ku bani books d'in " ya fad'a with burning face.

Jiki na rawa suka mimmik'a masa, dubawa ya shiga yi ya d'ago yana binsu da kallan takaici.

" Innah lillahi wa'innah ilaihir raji'un " yayi exclaiming da k'arfi, suko ko wacce banda zare ido babu abinda take.

" Ashe mahaukata na tara a gaba na bansani ba, tab wallahi zaku gane kuren ku, ashe asarar school fees kawai ake amma ace common solving maths kun kasa " a fusace ya shige bedroo d'in su ya d'auko wani belt mai kyau da tsada na company'n Gucci.

Takan Samha ya fara sai da yayi mata lilis sannan ya jefa mata book d'inta, cikin daka tsawa yace " kuma kafin na k'irga uku kibar d'akin nan ", aiko rufe baki bata bari yayi ba ta kwasa ana kare.

Then back to Lubnah itama ta daku ba k'arya d'an da dafa bango tabar d'akin.

Maido da kallon sa yayi kan Kadsah dake ta faman zare idanu yace " tashi ki tafi ki bani guri, kin wani tsare ni da ido kamar mayya ", jiki na rawa ta kwashi books d'inta ta gudu.


Allah sarki Safwah da Kuwaysah kallo d'aya zakai musu su baka tausayi, amma dan rashin tausayi irin na Suwayd ya zane musu jiki and again ya sasu kneel down.

Ko ajikin sa yaja system d'in shi  ya shiga danne_danne, Safwah jiri takeji yana neman kada ta dan zazzab'i harya rufe ta, ahankali tace " Ya Suwayd please we are sorry ".

" +15 minutes " shine amsar da ya bata batare da ya d'ago ba.

Ahankali taga duhu ya gifta mata kawai ta sulale a gurin , ihu Kuwaysah ta kwalla tana kiran sunan  Safwah, jin bata bata amsa ba ya sata takai hannu ta tab'a ta, sai dai me sam bata numfashi.

Ihun ne ya jawo hankalin Suwayd, cikin daka tsawa yace " dallah can Mahaukaciya rufemin baki,  tashi ki fita kafin na karya ki, idiot bastard kawai ".

Jiki a sanyaye ta mik'e ta fita tana kuka mai ban tausayi, tana fita ya nufi dispenser da sauri ya d'ebo ruwa yazo ya yayya fa mata.

Doguwar ajiyar zuciya tayi sannan ta ruk'un k'ume shi " Ya Suwayd please don't beat me, am very sorry  I will never do it again ".

Tausayin tane yayi bala'in kama shi jin yadda jikin ta ya d'au zafi kuma sai rawa yake amma ya dake yace " dallah malama cika ni, banza Aljana kawai " sannan ya murd'a kunnen ta cike da mugunta yace " next time idan na baki solving maths kimin hauka, zakiga abinda zan miki, kuma kafin na k'irga uku ki fice min a d'aki ".

Allah sarki Safwah she knows his last statement is impossible to her, haka ta samu da rarrafe ta tafi tana saka hannun ta a waje yana gama k'irgan sa.

" Come back idan kika sake ko taku d'aya kika k'ara sai ranki ya b'aci ", da jan jiki ta dawo tana kuka tana bashi hak'uri amma mugun sai da ya sake dukan ta sannan ya barta ta fita.

A hanyar shiga Babban falour ta fad'i dan bata da sauran k'arfin da zai k'arasa da ita, tana kwance helpless hannun ta dafe da kanta saiga..............

*'Yar Gatan Mhiss_B_Hal ce*💞

MAKAHON SO _Blinded Love_Where stories live. Discover now