SHAFI NA GOMA SHA BIYU

156 15 0
                                    

BAKAR ZUCIYA

TRUE LIFE STORY

NA

Basira Sabo Nadabo



Shafi Na Goma Sha Biyu

Inta tuna da ƙanƙantar yarinyar data mare ta saita kara fashewa da kuka

"Haba zinariyata don Allah kisawa ranki dan gana zanyiwa tufkar hanci amma ki bari mu haye tukunna duk abinda kike sonyi musu kiyi amma yanzu kinayin wani abu zai iyayin sanadiyyar faɗuwar mu, kinga kenan gwara ki bari muci tukunna koh Hajiyata?" ya karashe maganar cikin sigar rarrashi

"Wallahi Alh zan barta ne kawai badan na hakura ba amma kasani duk randa mukaye mulki a wannan ranar zan ɗauki mummunar mataki akan ƴan iskan yaranka masu gadon halin tsiya, ni na rasa ma me kagani ajikin matsiyaciyar uwar su da har ka aure ta"

"Kaddara ne wallahi kuma babu yadda zanyi da kaddarar data sauko min"

Haka dai suka maganganu marasa kan gado


GIDAN MAMA KAKA

Rarrashin duniyar nan Mama Kaka da Oppa sunyiwa Amatul'Kareem amma takiyin shuru, har saida Mama Kaka ta fusata tace

"Haba kuwa ke kuwa wani irin BAKAR ZUCIYA ce dake da za'ace miki kiyi hakuri kiyi shuru amma kinki to me kike son ayi miki ne Ama?"

"Dole nayi kuka Mama Kaka dole nayi kuka wai ace uban daya haifeni shine yake neman hallakani da hannun sa yake son kashe ni kuma kice bazanyi kuka ba me nayi masa ha me nayi masa?"

"Kiyi hakuri kanwata abinda kikayi masa ma kaɗai ya isheshi don bazai kara gigin tunanin tako kafarsu cikin gidan nan ba"

"Oppa Abbana fa yake son kashe ni shifa da kanshi bawai ɗan aike ya turo ba haba mana" ta kara fashewa da kuka

"Amatul'Kareem don Allah kiyi shuru kibar maganar kar zuciyar ki ta tun zura don Allah"

"Tun zura kuma na nawa Mama Kaka, wani irin ubane wannan me nayi masa ne haka me nayi masa ne don Allah, Ya Allah Ya Ubangijin halittan sammai da kassai, Ya Allah kasa Abbana a linkaya ta azaba, Ya Allah kayi masa duk nau'ikan azabarka, Ya Allah karkayi masa sassauci Allah kayi sanadin karayar sa ka hasa duk abinda yake nema, Ya Allah kayi masa mugun kamu hammu da gammu da huznu da guznu da kurnu dukka zuba a cikin sa Ya Kareemu ka hasa sukuni, Ya Allah duk wanda ya wayi gari a cikin wuta cen kasa, kasa karsu kaishe talaucin jahannama Ya Allah ka amsa min addu'ata Ya Allah" ta kara fashewa da kuka

Mama Kaka da Oppa ƙamewa sukayi saboda irin mugayen addu'oin dake futowa a bakinta, Mama Kaka ta sauke wani gwaron numfashi tare da cewa

"Ayyan Amatul'Kareem babu shafin aljanu a tattare dake, kinko san abinda kike faɗawa Abban ki wannan wani irin mugayen addu'a ne Ama"

"Ama kece kike yiwa Abba wannan addu'oin? koda yake hakkinki kike nema"

Taja hanci tare da cewa

"Nasan duk abinda nakeyi kuma wallahi Mama Kaka a shirye nake nayi wanda sukafi wannan muni"

Ta juya ta shige ɗaki tana kuka wanda inda hawaye yana karewa da tuntuni nata ya ƙare, ta faɗa kan gado tana kuka a haka bacci yayi gaba da ita, sai bayan da tayi mai isarta sannan ta tashi tare da wani irin ciwon kai mai sarawa, haka ta lallaɓa har zuwa banɗaki tayi wanka tare da ɗauro alwala tazo ta sallaci la'asar nan ma ta kara ɗaga hannu gurin neman bukatunta a gurin mai duka tanayi tana kuka

Amatul'Kareem dama tuntuni haka kikeyi da tuni kin manta da damuwar dake damunki, Ni Basiratu saida na zubar da hawaye

(Yake ƴar uwa kema ku gwada kuka gurin neman bukatunki gurin mai dukkan komai amma ki sani kiyi da zuciya ɗaya, an fisoma ki tashi tsakiyar dare sannan gurin da kike babu haske gudun karya jawo hankalin wani gurinki harya gane kuka kikeyi a gaban Ubangijinki, ƴar uwa kiyi kuka gurin neman gafarar ki, kiyi kuka gurin neman bukatunki ko wani abu mutun yake nema ya gwada da yardan Allah zaiga biyan bukata amma mu tabbata munsan ladubban addu'a Allah biya mana bukatun mu na alkhairi. Amin Ya Allah)

Bata tashi agurin ba har sai da aka idar da sallar isha'i

Dedicated to all my watpad readers and fans Basira tana sonku sosai

Vote 🌟

Karamar Su Babban Suce Ni Wato Ƴar Mutan KD Ce


Basira Sabo Nadabo


Follow nd Vote On Watpad @ Basira-Nadabo

BAKAR ZUCIYA Where stories live. Discover now