SHAFI NA GOMA

242 37 0
                                    

​BAKAR ZUCIYA​

​​​TRUE LIFE STORY​​​


​​​NA​​​

​​​Basira Sabo Nadabo​​​


Shafi Na Goma

Da sauri Mama Kaka ta taso daga gurin zaman ta tare da share hawayen tausayin ƴar jikan ta, ta rungumo kan Amatul'Kareem tare da cewa

"Nasani da zafi kuma bani da ikon hanaki sannan bazan taɓa hanaki kukan kiba jikata, nasan an zalunce ki an ruguza miki tsadaddan rayuwar ki tare da duk wani farin cikin da yayi saura a rayuwar ki Ama, amma ina son kisa hakuri a ranki ki koyawa kanki hakuri tare da dangana da mikawa Allah al'amuranki sannan ki koma gefe ki zubawa sarautar Allah ido kigani ko Allah bazai isar miki ba, Amatul'Kareem don Allah ki fawwalawa Allah lamuranki da sannu zai saka miki bisa zalincin da aka miki, haba da wanne zanji ne ki duba halin da ɗan uwanki ya ɗaurawa kansa duk saboda halinda ke kika tsinci kanki aciki tare da zugan muggan abokai ya fara shaye-shaye duk don ya manta da bakin cikin da kike ciki ne, don Allah ina rokonki da girman Allah kiyi shuru ki daina kuka domin kukan nan da kikeyi kamar kina zubamin garwashin wuta ne a zuciyata, kuma ki tashi muje asibiti kodan kujerar da mahaifinki yake nema kuma kin san koda wannan abokan gaba zasuyi galaba akansa don Allah Ama ki tash...."

Da sauri ta tashi a jikin Mama Kaka wanda ya hana Mama Kaka Karasa abinda zata faɗa, ta share hawayen dake zubo mata tare da cewa

"Kujera fa kika ce Mama Kaka?"

Ta fashe da dariya kamar sabuwar kamu, haka Mama Kaka ta tsaya tana kallonta har saida tayi mai isarta gashi hawayen yaki tsayawa

Ni kaina Basiratu da take bani labarin na rasa kuka da dariyar me takeyi, nasan dai dariyar bana farin ciki bane hakama kukan dai

Ta cigaba da cewa

"Hmm daman saboda kujera Abba yake son zubar min da ciki wata biyar zunubi biyu? toh wallahi yayi kaɗan don bai isaba kuma wallahi Mama Kaka ko kofar falon nan bazani ba da sunan zubar da ciki wannan karan kuwa bai isaba don bashi da iko akaina da abinda yake cikina kuma In Shaa Allahu abinda yake gudu saiya taka dorar kasa da yardan Allah"

"Karkice haka Ama ai ana barin halas don kunya kuma ma ai mahaifinki ne yana da iko akanki da abinda kike ɗauke dashi tunda shine uban daya haifeki"

"Mama Kaka don Allah mubar maganar don babu inda zani kuma maganar iko ada kenan yake da iko akaina amma banda yanzu don dashi da banza duk ɗaya duke agurina, kuma duk randa ya tareni da maganar zubar da ciki saina wulakantashi kuma naje gidajen yaɗa labarai na faɗama duniya shi wani irin ubane dan susan irin shigaban da suke nemawa kansu"

"Amma Amma ki duba lamarin nan"

"Mama Kaka mubar maganar nan don bazai taɓa yuwuwa ba" ta wuce ɗaki don ragewa jikinta kaya

​GIDAN ALH ALI

"Ai hajiya ta in kinga yadda na haukace musu dole ma wannan tsohuwar najadun tasa ta a zubar da ciki, kuma tuni nayiwa doc magana yana gamawa ya kawo min ɗan don ganin jikana daya bar duniya" ya karashe maganar da dariya daga ganin sa kasan yana cikin farin ciki

"Hmm Alhajina kenan kana zamanin kafa, kuma ina ganin har munci zaɓe an gama saboda harna fara jiyo ƙamshin kujerar mulki"

"Toh zamanin nawa ne yanzu kuma dole nacita da tsinken tsire, wai waya hango min hajiyata kan kujerar first lady amma zakiyi mulki sosai don koni kece zaki mulke ni sai yadda kikayi dani zinariyata" duk cikin dariya yake magana

"Amma fa Alhaji wani hanzari ba gudu ba yanzu idar yarinyar cen taki yarda a zubar da cikin fa ya zakayi kasanta da shegiyar taurin kai ga kafiya kamar kafiran farko" tayi maganar cikin damuwa

"Haba mana hajiyata ya muna cikin farin ciki zaki kawo mana abinda ma kila yanzu anyi an gama, ke dolema ta yarda inba haka ba zan koya mata hankali wallahi"

"Uh'uhn Alhaji kadai bi komai a hankali"

"Kamar yaya nabi komai a hankali anki abi ɗin ke barima na kira doc ɗin kiji dakunnen ki donki tabbatar da yanzu haka ma an gama komai" ya faɗa tare da ciro wayar sa dake gaban aljihun rigarsa ya latsa numbar doctor ɗin bugu biyu ana uku ne ya ɗauka tare da sallama

"Assalamu Alaikum Alhaji barka da wannan lokacin"

"Yauwa barka doctor ya aikin ne ya jama'a"

"Alhamdulillahi Alhaji"

"Nace maganar da mukayin nan kuwa an gama kuwa"

"A'a yallaɓai har yanzu basu zoba kuma Alhaji da za'a hakura da zubar da cikin nan da yafi saboda za'a iyayin asarar rayuka biyu, saboda cikin yayi kwari sosai yallaɓai indan muka matsa itama zata rasa ranta kaga kenan anyi biyu babu ko ɗaya kuma Alhaji da zaka bari tah...."

"Rufe min baki kafini sanin abinda nakeyi ne kome koko kaine zaka koya min abinda zanyiwa ƴar cikina, taje ta ɗauko min abin kunya kuma kace na bari, to nagane nufinka kaima kana bakin ciki da kujerata kenan ko? dakai nake magana" ya karasa maganar cikin tsawa

"A'a yallaɓai kawai naga dai Amatul'Kareem zata iya rasa ranta ne kuma gashi itace ƴar lelenka kar rashinta ya haifar maka da matsala"

"Ta mutu mana ruwan waye toh bari kaji inhar bazaka iyaba ka faɗa min akwai asibitoci wanda suka fika kwarewa akan harkar kuma suyi min yadda nake so" ya karasa maganar tare da kace wayar

Hmmmm Allah sarki duniya gidan kashe ahu, Allah kasa mufi karfin zukatan mu, wannan dame ma zan kirasa uba ko me, wanda bai damu da damuwar ƴarsa ba sai damuwar sa ta duniya, taɓ ni Basiratu na kuma cewa uhmmmm

Har yanzu banga votes ba sai dan kadan anya kuna son labarin nan kuwa, Ko kuma kuna son na tsaya a haka ne? Inhar kuna son labarin toh naga votes na muku alkawarin jin labarin Amatul'Kareem da Irin kuncin da Abbanta ya sata.

Kuma karku manta kuma zaku iya gayyato friends and family duk suzo suji labarin BAKAR ZUCIYA amma dai Ku tuna da zungurin orange din 🌟 din nan

Nagode

Karamar Su Babban Suce Ni Wato Ƴar Mutan KD Ce

Basira Sabo Nadabo

Follow nd Vote On Watpad @ Basira-Nadabo

BAKAR ZUCIYA Where stories live. Discover now