SHAFI NA TAKWAS

216 15 0
                                    

BAKAR ZUCIYA

TRUE LIFE STORY

NA


Basira Sabo Nadabo



Shafi Na Takwas

Duk suka ɗunguma zuwa gurin alwala tun kafin su kara gurin duk yan matan dake gurin suka jiwo suna kallon mu har nunani sukeyi da hannun, H. Hasheem ce ta tamka musu daman yadda na lura kamar ita bata ɗaukan iskanci har gwara F. Ahmad saboda tun gurin hirar su da khairat na lura da ita, tana girgiza dauke da hannu a kugu muka karasa tare da cewa

"Toh ƴan bani na iya me kuma ake tsegunta muku akanmu don tun daga nesa naga kuna kallon mu ko munyi muku kama da masu satan samari ne?" ta karasa maganar da isgilanci

Ɗaya daga cikin ƴan matan ne ta amsa mata don daga gani itama duk kanwar jace

"Bakuyi mana kama da masu satan samari ke koma ance ki satar min saurayi zaki iyane saboda baki zama cikakkiyar budurwar data tara wasu abubuwan da zaija ra'ayin saurayina balle harki fara tunanin satar min saurayi ba, kuma kallo aiko kuke da abin kallo tunda kike tare da wacce take ɗauke da abin kunya kunga kenan kune abin kallo"

"Ke ki iya bakinki inba haka ba wallahi zamu kwashe ƴan kallo a makarantar nan, yanzu ke don Allah har kina kiranki mace ina macen take?"

"Gani nan kalleni sama da kasa" ta faɗa tare da jujjuya jiki

Hehehehehe "Ikon Allah na zaune baiga gari ba yanzu ke ahakan ne kike kiran kanki budurwa, wallahi kina ruɗan kanki domin ke idan mukaje gasar kyawu na duniya faɗuwa zakiyi kuma da kike cewa muna tare da wacce take ɗauke da abin kunya in baki sani ba bari na faɗa miki, ai tsohone yake zagawa don yaga ubanta nada kuɗi shi yasa har yasamu daman yi mata cikin dake jikinta, sannan ko ban faɗa ba kunsan waye ubanta, wawaye kawai kuma wallahi duk wacce ta kara magana anan sai mun kwashe ƴan kallo, duk wacce take ganin ƙarya ne ta tanka don Allah" karasa maganar da nuna yatsa akan wannan yarinyar data tanka mata

"Ni bazanyi faɗa dake ba to waima innayi faɗa dake ace nayi dawa?"

"Kinyi da Hajara, niba wannan bama kiyi maganar dazai kara ɓata min rai dan girman Allah"

"Allah ya kiyaye ni haɗa kashi dake dallah kutaso muje don tsayawa cacan baki da waɗannan ɓata lokaci ne" duk suka tashi suka bita a baya tare da yan makarantar da suka taru don bawa idanun su abinci kun san makaranta yadda take dai

"Ashe madai keɗin ba kowa bace da har kika gujewa jimgata don wallahi mai kwatanki a gurin nan Allah ne kawai yan iska kawai, ke kuma ki cigaba da zama suna zaginki karki dinga ramawa don bai zama lallai kullun nice zan dinga tare miki faɗa ba, ku kuma me abinda kuke kallo magulmata kawai, duk duka fara watsewa" ta juya kan Amatul'kareem da yan makaranta, sai banbami takeyi

"Haba Hajara ya isa mana tunda kin amsa na yau ai shikenan ashema faɗa yana da rana da ake cewa ki daina a gida gashi faɗan naki ya kwace mu"cewar F. Ahmad

"Hmmmm nagode H. Hasheem kuma In Shaa Allahu hakan bazai kara faruwa ba kuma nagode da kika kwatar min ƴanci na yau Allah yabar mu tare kawata"

"Niba wannan ba muje muyi alwala muyi sallah lokaci yana wucewa" duk suka karasa gurin alwalar

GIDAN ALH ALI

"Alhaji kaji abinda nakeji kuwa a gari?" cewar Aunty Salima

"Me kikaji a gari gudaliya ta?"

"Hmmmm kadai Alhaji abar kaza cikin gashinta don inhar aka fige to an mata mummunar tonar asiri amma kan zanso kaji wannan lamari, kai duniya ina zaki damu ne ni Salimatu"

"Amma dadai zaifi da kin faɗa min saboda inma wani abunne nakeyi saina gyara ko hajiyata?"

"Hmmm to shikenan Alhaji daman ji nayi agari wai kana zaune da girmanka da matsayinka a kasar nan tamu amma kabar ƴarka har yanzu ɗauke da ciki, sannan suka kara cewa inhar daiko hakane bazasu iyaba baka ƙuru'un suba saboda a yadda suke cewa shugaba tun daga gida ake gane shugabancinsa amma kai kuma gaka ƴarka tana ɗauke da ciki kuma bakayi yunkurin zubar dashi ba, ni kuwa nace ai aje zubarwa yaki fita ne sai matar tace laifinka ne don babin na ƴar za'ayi ba da karfi da yaji za'ayi kuma dole ya fita kuma ƴarka tayi rai inma itane kake tunanin mutuwar ta"

A zabure ya mike tare da cewa "Wannan shashashar ne zanyi tunanin mutuwar ta nida zata mutun ma danafi kowa farin ciki wallahi don wannan yarinyar baraza ce ga kujerata kuma wallahi kinji na rantse ko zan iyayin komai domin cikin nan ya fita donni bazan lamunta cin mutunci daga kuru'un jama'ata ba"

"Yau Alhaji na yanzu dai kasan yadda zakayi nidai tarabu da ɗan shegen dake jikin ta shegiya mai halayyar uwarta ɗan first lady ɗin da mutane zasu kirani take bakin ciki saboda ba uwarta bane"

"Kedai gudaliya kiyi shuru zanyiwa tumkar hanci don wallahi dole na ɗare kujerar da takemin bakin cikin sa, kai duniya wai yau nine na haifi ɗan da yake min bakin ciki a siyasa na toko bazan lamunta ba wallahi, zanje cen gidan uwar uwar nasu kuma dole ta zubar da cikin nan" sai sababi yakeyi kamar Amatul'kareem ɗince zaune a gaban sa

"Yauwa Alhaji na shiyasa bana shayin faɗa maka abinda naji a gari saboda kai nawa ne kuna baka bincike kake hawa magana mai gidana na kaina ni kaɗai daga ni babu kowa"

"Kedai sha kurumin ki zinariyata, yo wani bincike zanyi tunda nasan bazaki faɗa min karya ba"

Haka Aunty Salima ta dinga tun zura shi har saida taga ya tun zuru sosai sannan tayi shuru

Ni Basiratu na kuma cewa uhmmmmm

Karamar Su Babban Suce Ni Wato Ƴar Mutan KD Ce

Basira Sabo Nadabo

Follow nd Vote On Watpad @ Basira-Nadabo

BAKAR ZUCIYA Where stories live. Discover now