SHAFI NA UKU

293 19 4
                                    

BAKAR ZUCIYA

TRUE LIFE STORY

               NA

Basira Sabo Nadabo


Readers don Allah kumin afuwa zanyi tafiya gobe zuwa my side wato birni na Taraba bikin bro ɗina, kuyi hakuri ba kullun zaku dinga samun update ba amma In Shaa Allahu zanyi kokari inga na baku karku damu, kusa ni a addu'a plz

INA TAYAKA MURNAR KUSA ZAMA ANGO YAYA NA ABUBAKAR SABO NADABO , ABUy NAMU WAI AKACE MAGANIN A KWABEMU, ALLAH DAI YA KAIMU LOKACI LAFIYA. AMIN YA ALLAH

Shafi Na Uku

Daga cikin ɗaki mama kaka tajiyo muryar Amatul'kareem ta fito da sauri ta shiga falon ta hau oppa da faɗa tare da cewa "haka mukayi da kai bance karkasa Ama kuka ba? toh bazaka ƙara zuwa gidan nan ba indai kuka zaka dinga sata, ya za'ayi ina gyara kana lalatawa gaskiya bazan lamunta ba, ke kuma ya isa haka kiyi shuru ko kina mantawa da akwai Allah ne, ki mikawa Allah lamuranki sannan kiɓkoma gefe ki zubawa sarautar Allah ido kiga irin hukuncin dazai zartar ga bawan da aka zalunta kinji ko, tashi mu shiga ciki, kai kuma ka tashi ka fita zan neme ka, kaima don Allah ka cire komai a ranka mubarwa Allah" haka suka tafi Ama ta juyo domin ganin halinda oppan ta yake ciki

Ya tashi jiki babu lakka tamkar wanda aka zarewa kuzari baiki shima a rarrashe shiba, yana fita masallaci ya nufa yayi alwala tare da gabatar da sallah raka'a biyu a sujaddar karshe ne ya fashe da kuka a lokacin da yake faɗawa Ubangiji damuwarsa, yakai kukansa gurin mai dukkan komai har saida yagaji don kansa ya ɗago daga sujaddar idanun sa sunyi ja, sai da yayi kukan sannan ya samu kwanciyar hankali

      "Ni Basiratu nace lallai kuka ma babban rahama ne"

A ɓan garen gidan alhaji Ali kuwa kamar babu abinda yake damun ƴan gidan domin shi uban gayyar bai damu da halinda yaransa suke ba balle yasan damuwar su, bayan shine dalilin tagayyatar rayuwar ƴaƴansa saboda korar da yayi wa Amatul'kareem tare da Abdul'kareem (oppa)

Aunty salima macece wacce bata damu da rayuwar kowa ba sai kanta, zan iya cewa tana ɗaya daga cikin shaiɗanan da zuka gurɓatar da rayuwar Amatul'kareem domin Aunty salima dukiyar Alhaji Ali ne kawai a gabanta, tana neman hanyar da zai faɗi ya mutu domin taci gado ko a yanzu kasuwata watse ɗan koli yaci riba, don kuwa tana da manya-manyan plaza a cikin gari dama wasu garuruwan, gashi tana saro kaya daga wajen ƙasar mu zuwa cikin ƙasar mu tana sai dawa manyan matan ƙusosin najeriya

Alhaji Ali mutun ne wanda addini bai dame saba tun wasu shekarun baya da suka wuce ya baida addinin sa gaura hamma kuma yasan hukunce-hukuncensa yasan farillai da sunnoni da mustahabbancinsa amma yasa duniya a gaba harkokin kuɗinsa yasa a gaba shine komai nasa na rayuwa domin a nashi tunanin babu abinda kuɗi bazai siyama masa ba sai dai inko babu abin a doron duniya kuma sai dai inbai kyalla ido ya hango abinba

          Ni Basiratu nace ƙarya ne akwai wani abu ƙwara ɗaya wanda kuɗi bazai siya maka ba Alhaji Ali, na ƙara cewa hmmm

Ada kafin mutuwar Ammin mu ana ƙoƙarin ganin sa a sahun sallah amma tun bayan rasuwarta aka daina ganinsa a masallaci, tun ana ganinsa a sahun gaba ya dawo sahun baya, ya kasance ma baya samun cikakkiyar jam'i kai har yazo sai sallah asuba ake ganinsa, wani babban malami yasa mesa yayi masa nasiha kamar abin arziki ya fara yin sallar cikakkiya, abin bai ƙara taɓarɓarewa ba saidabya auri Aunty Salima, ɗan sallar asuba ɗinma ya daina zuwa sai dai yayi a gida, a gidan na ta gagara sai dai ya haɗasu, wani lokacin ma inya gaji gurin jero sallolin hakura yakeyi a cewarsa watarana zai ramosu duka wanda suka kuɓce masa

        Niko nace hmmn, ina rayuwa zayyiwa bawa kyau yabar hanyar Allah, Allah kasa kasa muyi galaba akan shaiɗan gurin biyayya da dokokinka Ya Allah, duk muka amsa da Amin

Watarana Aunty Salima ta samu Alhaji Ali yana shirya ta amsa domin tayashi tare da cewa "nace Alhaji niko ina yaran nan ne?"

"Wasu yara kenan hajiyata?" ya tambaya cikin sakin fuska

Tayi wanu ƙayataccen dariya tare da cewa "Alhaji kana sha'aninka wallahi, lallai na ƙara yarda da kalamanka na kai duniya shine a gabana kuma zanyi komai koma menene domin na sameta, yanzu Alhaji yaran naka ne ka manta dasu har kake tambayata wasu yara, bayan waɗan nan mugun irin ƙwara biyu kana da wasu yaran ne?, aini wallahi an cuceni don BAKAR ZUCIYA da maman yaran nan zata mutu saita kwashe sauran yaran ta tafi dasu don kawai yaranta su cinye ɗan abinda ka bari ni kuma ko oho, ta fashe da kukan munafurci

Nan da nan yayi kicin-kicin da fuska tamkar wanda bai taba dariya ba yace "haba ke kuwa nifa bani da wasu yara a duniyar nan sai wanda zaki haifa min, tuni na sallame wa'ancen yan iskan yaran, na haifi yarinya ta kawo min abin kunya gidana bazai yuba tuni na barsu da duniya ta musu riga da wando, kuma ai nasha faɗa miki babu uban da zaici gadona saike ƴar gwal ɗina zinariyar zuciyata, don Allah kibar kukan nan ya isa haka, ɗigar hawayen ki yana ƙona min zuciya inba so kike nina kiga ina kukan ba" ya karashe maganar da damuwa a fuskarsa

Ta share hawayen tare da cewa "shikenan Alhaji nayi shuru bazan ƙara kukan ba mijina, amma Alhaji mai zai hana tun yanzu karaba gadonka da kanka kaga saika bani nawa da hannunka ko"

"Eh karki damu indai wannan ne zan duba lamarin, ni zan fita saina dawo ki kularmin da kanki harna dawo zinariyata"  yayi maganar yana mai fita

Tayi dariya tare da cewa "ai dolema na kula da daina ko dan kanka mai gida na" ta karashe maganar cikin jin daɗi domin hakarta ya cinma ruwa

         Ni Basiratu nace babu In Shaa Allah ma sai dole saboda rayuwarta da lafiyarta suna hannunta, nakara cewa unhhmmnmm


Karamar Su Babban Suce Ni Wato Ƴar Mutan KD Ce

            Basira Sabo Nadabo

Follow nd Vote On Watpad @ Basira-Nadabo

BAKAR ZUCIYA जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें