SHAFI NA ƊAYA

811 51 5
                                    

BAKAR ZUCIYA

TRUE LIFE STORY

Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

            NA

           Basira Sabo Nadabo


        SHEKARAR RUBUTU

             2018

      GARGAƊI

           BAN YARDA WANI KO WATA SU JUYA MIN LABARI NA BA DOMIN WANNAN LABARIN BA ƘAGAGGEN LABARI BANE, LABARI NE DAYA FARU A GASKE, DON HAKA A KIYAYE, DUK WANDA YA JUYA KUMA SHIDA ALLAH KODA  HARAFIN A, AKA JUYA MIN, ALLAH YA ISA

      GODIYA
       
          Ga ALLAH madaukakin Sarki, wanda raina da rayuwa ta suke hannunsa. Ina gode maka, ina neman taimakon ka. Ya Allah ina rokonka, ka kare ni da dukkan abin ki. Ya Allah ka tsare ni ga magauta, Allah kada kabar makiya suyi nasara a kaina da kungiya ta, ALLAH bani da niyyar cutar kowa, ALLAH kada kabar makiyi yayi nasara a kaina da kungiya ta domin abarkar Annabi Muhammad (S.A.W).


      DOMIN KU
       
     Iyaye na abin alfaharina, wanda na dauki so da kauna na dora muku. Margayi Alhaji Sabo Nadabo da Alhaji Nuhu Abdullahi, tare da Hajiya Fatima Sabo Nadabo da Zulaihat Sabo Nadabo, tare da Zainab Nuhu Abdullahi da Aisha Nuhu Abdullahi da sauran al'umman Annabi Muhammad (S.A.W), ina rokon Allah da ya yalwata haske tare da rahamarsa a kabarbarunku, Ya Allah ka kara gafara a gare su damu baki daya Amin. Mahaifiyata farin cikin rayuwata nagode da kulawarki a gare ni nagode da shawarwarinki akan wannan labarin nawa Allah Ya kara tsare min ke Ubangiji yaja kwana. Amin Ya Allah.



       JINJINA GARE KU

      Yayye na muradina nagode da kulawarku a kaina ALLAH ya kara hada kanmu ya kauda shaidan a tsakanin mu. Amin Ya Allah

         AUTA SHALELE

      Fa'ieza Sabo Nadabo, ina sonki sosai a raina dake da takwara na Bashier Sabo Nadabo, tare da Muzeenat Rajeev kune ni, idan nace ni ina nufin ku, idan nace ku ina nufin ni, Allahu ya raya mana ku musha biki. Amin Ya Allah


     SADAUKARWA

       Na sadaukar da wannan littafin ga Family na gaba daya.

   
       KAWAYE NA

       Ramaluv yar kasar Niger republic ina sonki a cikin raina.

Aisha Habeeb Tall Gaskiya keta daban ce domin kalmar ana tare yana aiki a tsakanin mu kano zuwa kd ba abu bane mai sauki amma nagode da kauna sweetat.

Baby Nurse Mom Anielurv, ina sonki dake da yarinya ta ALLAH ya kauda fituna a cikin gidanki. Amin Ya Allah

My Saqueenceey mom unborn baby, Allah ya nuna mana ranar zuwan babyn mu duniya, limamin matan bana zamu kira ya wake mana unborn child.

Yayata SophiaG ina ♥ dinki like sosai fa

          JINIE NAH

Rukaiya Nuhu Abdullahi, Rukiee baby mai dadin murya in tana magana kamar ana busa algaita, Ina sonki sosai tun daga qalbie zuwa baki na. Lallai Ana Mugun Taren Tare.

             GAISUWAR BAN GIRMA GARE KI

    MY NAMECY CUTIE PIE AKA BASIRA MUTANAN LONDON WALLAHI DUK DUNIYAR WHATSAPP BABU KAMARKI A GARE NIY, SAI DAI NACE ALHAMDULILLAH, ALLAH KUMA YA KAUDA SHAIDAN A TSAKANIN MU. AMIN YA ALLAH
                 KI RIKE A RANKI BASIRA SABO NADABO TANA SONKI SOSAI

Bismillarhir-Rahmanir-Rahiim

Ya Allah. Ina farawa da sunan ka kuma In Shaa Allah zan gama da Hamdan, wannan labarin *BAKAR ZUCIYA* labari ne daya faru a gaske, babu abinda na kara kona rage sai dai na canja sunayen dake ciki da kuma garin da abin yafaru amma kam *TRUE LIFE STORY* ne, Allahu kasa na gama lafiya alfarmar Manzon Allah, Habibullah, Shafi'ullah, Ya Mahabubullah Ya Sayyadi Ya Muhammadur-Rasulullahi Sallalahu Aalihi Wa Sallam.



SHAFI NA ƊAYA

"Haba ƴan nan wannan kukan babu inda zai kaiki sai ƙarin bakin ciki da kuncin rayuwa kullun ina kara nasiha a gareki ki zama mai tawakkali da godiya ga Allah" cewar tsohuwar dake tsaye a kanta

"Wayyo Allah na, wani irin laifi nayi wa rayuwata ne me nayi, me nayi ne Don Allah, me yasa Abbana zai min haka me yasa ya zaɓi rayuwata ta zama abar kwatancen kowa, me naye masa ne haba rayuwa, wayyo oppa, oppa na," duk cikin kuka take magana

Hmmm "shikenan kiyi yadda kike so, wallahi Amatul'kareem idan bakiyiwa zuciyarki sassauci ba zaki faɗa ga halaka, tun wuri kiyiwa kanki da kanki hisabin rayuwarki kafin rayuwa tayi miki juyin masa"

"Haba mama kaka me nayi masa wani irin BAKAR ZUCIYA ce haka, wallahi bazan taɓa yafe masa ba"

Toh sai kiyi tayi tunda ke babu wanda ya isa ya hanaki, saiki cigiba da tonawa kanki asiri, wai ance miki kanki farau ne ko kuma daga kanki za'a daina, wallahi Annabin Allah gaskiya ne kuma duk abinda ya fito daga bakin sa mai tsarki gaskiya ne, kuma duk abinda ya faɗa gashi yana faruwa, don haka Amatul'kareem ki share hawayenki kina zaune Allah zai azabtar da duk wanda yake da hannu a cikin al'amuranki kinji koh"

"Ya Allah ka wulakanta Abbana, Allah ka haɗa shi da dukkanin nau'ikan azabanka, Ya Allah ka hanashi rahamarka, Allah ina rokon ka da fiyayyen sunan daka haɗa da naka, ka tozarta shi, Ya Allah ka duba raunannayar zuciyar da aka zalinta kasa Abbana kasan su Abujahal, Ya Allah kasa shi a....," da gudu mama kaka ta rufe min baki tare da cewa

"Haba Amatul'kareem, haba Ama wannan wani irin nugayen adduo'ine kikeyi wa mahaifinki aiko ba komai ubanki ne, kuma ina kara baki hakuri don nasan an cuceki amma ki yafe masa, ko kin manta Allah yana gaggawan amsar addu'an wanda aka zalunta"

"Wallahi mama kaka zanfi kowa murna idan Allah ya amsa addu'ata a yanzun nan saboda bazan taɓa yafe masa ma, idan har giyan kuɗi ne yake ɗiban sa ya Allah ka tozarta shi kasa ya zama faƙiri, Ya Allah ka amsa min addu'ata Ya Allah"

Hmm "wallahi Amatul'kareem ina jiye miki faɗawa ga halaka saboda irin mugayen adduo'in da kullun kike aikawa babanki yau in Ammin ki tana duniya zataji daɗin irin wannan adduo'in, karfa Allah yayi gaggawan amsar addu'arki Ama" ta karashe maganar cikin rarrashi

"wallahi mama kaka zanso Allah yayi gaggawan amsar addu'a ta, inaso Allah yaji kuma ya duba zuciyar da aka zalinta yabi min hakkina, wallahi mama kaka bazan taɓa yafema Abbana ba saboda abinda ya faru kina gani dangin Abbana sun tsaneni, masoyina ya guje ni duniya tana min tofin Allah tsine, duniya tana zagina abinda ke cikinta suna gudu na hatta ga dabbobi da tsirrai suna tsine min, ki gaya min da wanne zanji ina zan dafa naji daɗi, a hakanne zan yafe masa? toh wallahi bazan yafe masa ba, oppa nane kawai bangon da nake jingina naji sanyi, mama kaka saboda ni an hana oppana aure sun kyamaci zuri'ar mu, me nayiwa Abbana haka me nayi masa me nayi masa ne mama kaka, saboda BAKAR ZUCIYAR sa yasa tawa zuciyar cikin garari" ta karashe maganar cikin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro


Karamar Su Babban suce ni wato yar mutan KD ce.

   Basira Sabo Nadabo


Follow Me On Watpad @Basira-Nadabo.

BAKAR ZUCIYA जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें