CHAPTER TWO

609 42 0
                                    


   A wani babban plaza Haydar yayi parking, Farooq ya juya ya kalle sa yace
"Ya ka tsaya anan kuma?"
D'an guntun tsaki yaja yace
  "Akwai abubuwan da ban siya ba wanda nake so na tafi dasu"
Khaleal dake bayan motan yaja dogon tsaki yace
"Fisabillah kunyi shopping na abun da zaku tafi dashi yafi sau goma, naga ba abunda baku siya ba, uban meye kuma yanzu baka siya ba?"
  "Idan zaku sauk'o toh idan kuma baza ku sauk'o ba nayi shigewata ni kad'ai". Ya fad'a yana mai danna wayarsa.
Farooq neh ya fito a motar, sai shima Haydar ya fita sai can daga baya Khaleal ya fito. Jerawa sukayi suna tako kamar zaki, ni dai tsayawa nayi ina kallon su dan idan ance na zab'a d'aya daga cikin su bansan wa zan zab'a ba.
  Bayan sun shiga Haydar tissue paper kawai ya d'auka, yace
"Shikenan guys daman abunda ban siya ba kenan"
Girgiza kansu duk sukayi, Farooq ya fita a mall d'in Haydar yana biye dashi a baya, Khaleal kuma wajen fruits yaje ya d'iba yazo ya biya kud'in ya fita.

  Suna cikin tafiya suka ga wata mota corolla-S maroon tana ta danna musu horn, duk sunga motar amma kowa yayi banza ba wanda yace uffan. Haka motar ta ringa binsu har suka kai wani babban gida a cikin anguwar zoo road, Haydar sai wani danna horn yake ba tsayawa har mota corolla-S d'in tayi parking, wata yarinya ce chocolate colour ba laifi tana da kyau tafito a motar tazo wajen motar su, knocking glass na motar take wajen driver seat dan bata san ma waye yake gaba ba  sabida super tint neh glass d'in amma tasan tabbas sune dan ta haddace number'n duk wani motan da suke fita dashi a kanta.

  Haydar neh ya b'ata rai ya juya yana kallon Farooq yace
"Ai sai ka sauk'a ai tunda kai take nema"
  Koh kulashi Farooq baiyi ba ya k'ara volume na music dake tashiwa a motar, ganin haka Haydar yaja bakin sa yayi shuru yacigaba da danna wa mai gadi horn, Khaleal kuma wanda kamar baisan what's going on ba sai game yake a wayar sa.. Mai gadi na bud'e gate d'in da gudu ya shiga cikin gidan yayi parking motar yabar yarinyan nan tsaye. Wani irin bak'in ciki taji haka ta shiga motar ta ta tafi..

Wani babban mansion parlour suka shiga, wata dattijuwa ce take ta goge-goge a parlour'n, tana ganin su tayi murmushi tace
"Manyan maza sannu da zuwa"
Kamar wanda bakin su yana ciwo suka amsa ciki-ciki da "Yawwa" wanda ita bataji muryan kowa ba sai na Khaleal, Haydar neh yace
"Ammm dan Allah kiyiwa Mummy magana mana Marka"
Ajiye tsumman hannun ta tayi tace "Toh ba matsala"
    Zama duk sukayi akan kujera sukayi crossing leg kowa sai danne-danne yake da wayar sa, sallaman wata mata wanda ak'alla bazata haura arba'in ba, chocolate colour kyakkyawan gaske da k'aton cikin a jikinta, ganin ta da sukayi  yasa duk suka sauk'o k'asa kan carpet suka gaishe ta, fara'a kwance akan fuskan ta tace
"Yara na ya kuke?"
Duk suka amsa da "Lafiya kalau Mummy"
  Murmushi tayi tace "Haydar ni kam yanzu yaushe tafiyan ka?"
Kanshi a k'asa yace "Jibi In Shaa Allah Umma"
Farooq da Khaleal sukayi dariya, Mummy tace
"Ku kuma lafiya kuke dariya?"
Khaleal yace "Umma wallahi har wani tausayin sa nake ji,  da yayi three weaks a camp  kinga yadda yayi bak'i kuwa?"
Dariya tayi tace "Kunji ka, akan wani dalili zaka tausaya mishi?  Kuma ba wani bak'in da yayi. Wallahi kar kayi baki idan ka gama Houseman ship naka suyi posting  naka Anambara koh wani Imo State"
"Haba Umma irin bakin da zaki min kenan?"
"Ni ba baki na maka ba amma ku daina wa Haydar dariya"
Murmushi Haydar yayi yace "Mummy ki barsu idan sun gaji zasu daina"
Haka nan suka ta hiran su, Farooq ya yanka musu fruits d'in suka sha, basu bar wajen Umma ba sai kusan k'arfe goma da rabi.
 
    Wani B'angaren naga sukayi, babban parlour neh a tsakiya da d'aki gudu uku a koh wani angle duk naga kowa yayi hanyan d'akin sa suna sai da safe....

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

   *Aliyu Haydar* Badamasi da *Usman Khaleal Badamasi* tagwaye neh a wajen Alhaji Badamasi Abdullahi. Alhaji Badamasi Abdullahi bahaushen kano neh, babban d'an kasuwa neh yana da gidajen man fetur a gari daban-daban, yana da companies a cikin gida Nigeria har ma a k'asan waje, wannan dalilin neh yasa baya cikikken sati uku a nigeria. Yana da yara uku, biyu sune tagwayen da autar su Yesmin. Matar sa Hajiya Farida Abubakar Jimeta 'yar asalin garin yola ce bafulatana usul, ba k'aramin so da k'auna take nunawa 'ya'yan ta ba. KHALEAL ya karanta Medicine and Surgery a India ya gama yanzu yana housemanship nashi, HAYDAR kuma ya gama a Business Administration a England, Yesmin kuma yanzu take Part one a Bayaro University,Kano (B.U.K) tana karanta Computer Science.

    ♤♡♤♤♡♤♤♤

  *UMAR FAROOQ MUHAMMAD* d'a neh a wajen Alhaji Muhammadu Iliyasu Lamid'o minister of petroleum, haifaffen d'an garin gombe neh fulanin usul, matar sa kuma Hajiya Fauziya Yusuf 'yar asalin garin Jimeta neh a yola. Yaron su d'aya wato Farooq, tunda ta haife shi haihuwa ya tsaya mata cak, ba inda basu zagaya a fad'in duniyan nan ba dan ganin manya manyan likitoci amma gaba d'ayan su amsa d'aya suke bata wato lafiyan ta lau. Har sun cire rai da haihuwa kwatsam sai ranar da Farooq ya gama school ya dawo daga England  ya tarar da mahaifiyar sa kwance lik'is ba lafiya, kiran family doctor'n su yayi, gwaji d'aya ya tabbatar tana d'auke da juna biyu. Abun gani suke kamar a mafarki, Hajiya Fauziya sanda ta zubar da hawaye dan farin ciki, shi kanshi Farooq wani irin farin ciki mara misaltuwa yakeji after a very long time shima yanzu zai samu k'ani. A kullum yana sha'awan Yesmin, idan yaga su Haydar da Khaleal suna tsawatar mata yata lallashin ta yana bata hak'uri, a ko wani tafiyan da zaiyi sai ya siyowa Yesmin tsaraba, duk inda suka shiga sai yayi maganar k'anwar sa Yesmin, idan baka san su ba sai ka rantse Yesmin k'anwar Farooq ce bana tagwayen maza ba... Ba k'aramin farin ciki Alhaji Muhammadu yayi ba da Farooq ya masa da wannan albishir d'in, take ya bawa Farooq kyautan babban gidan sa dake cikin abuja....

   Hajiya Fauziya da Hajiya Farida aminan juna neh tun suna yara k'anana, tare sukayi wasan k'asa tare suka girma har Allah yasa duk kansu sukayi aure, haka ma 'ya'yan su Farooq da tagwayen maza suka tashi suka girma tare kuma aminan juna neh, sai dai Haydar da Farooq sunfi kusanci dalilin makarantan da aka tura su d'aya a England  kuma suna karanta course d'aya,  shi kuma Khaleal a India.    
    Farooq da Haydar suna da farin jini sosai a wajen jama'a, mata na mutuwar son su suna binsu har a England. Su basu tab'a bud'e baki sunce suna son mace ba, sai dai shi Haydar a cikin matan da suke bibiyar sa zai zab'a d'aya daga cikin su had'add'iya yana kwanciya da ita, wannan shine ke kawo sab'ani tsakanin shi da Farooq akan yana kawo 'yan matan sa gidan. Shi kuma Khaleal karatu kawai yake a India ba kama hannun yaro bare yana karanta medicine ai ba wasa, shi kuma ba  ruwan sa da 'yan mata balle ya yaudare su duk yadda 'yan mata masu class suke binsa.

Miskilai neh su na gaske, sai suna tare su uku-uku zakaji suna hira suna dariya, amma a waje sai ka rantse basu tab'a  dariya ba dan magana ma da k'yar suke amsawa, wanda a cikin su gwara-gwara shi Khaleal wata rana yana d'an sake fuska....

  Wannan Kenan

*Nana Fa'ad* ce

NIDA TAGWAYEN MAZA Место, где живут истории. Откройте их для себя