page 166~170

1.2K 76 0
                                    

JARABAWA TACE



yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



              1⃣6⃣6⃣➖1⃣7⃣0⃣

    Sanye take cikin red super kallon Lady tayi tace "Anty Lady nayi kyau?" D'aga mata kai tayi, zumb'ure baki tayi tana buga k'afa tace "pls Anty say someting mana" kinyi kyau shikenan? Ihu tayi wanda sai da yasa Lady ta razana, tsoki tayi tace "waike yaushe zaki daina ihu? Bakisan kin girma ba?" Dariya tayi kafin ta bata amsa taji sallamar su Yaya da gudu tabar d'akin tana oyoyo Mummy, tab'e baki Lady tayi ta tashi ta fita...
   Da gudu ta isa gaban Yaya mak'alk'aleta tayi tana dariya, murmushi Uncle yayi yace "Intee karki karyaman mata" dariya tayi tace "Daddy nayi missing d'inta da yawa fa" toh ai gatanan yanzu kinganta, dariya Yaya tayi tace "ka kyaleman Baby yaushe rabon mu had'u" yehhh datz my Mummy..
   Hannunta Mummy taja suka zauna, "yasu Maamma?" Suna nan Lapia lau suna gaidaki, Daddy ma yace "yana gaidaku sosai"
   Shafa kuncinta tayi tace "muna amsawa" daidai su Lady da Aflan sun k'araso parlour..

    Kallonta Lady tayi tace "wai ni Intee yaushe zaki daina ihu?" Aflan yace "tayani tambayarta dai tunda tazo ta cika mu da ihu har yanzu yarinya tak'i natsuwa wai kuma an shiga university kenan"..
   K'afa ta fara bubbugawa tace "Mummy Daddy kuna jinsu?"..
   Dariya Uncle yayi yace "ku kyaleta mana ina ruwanku ku miye bakuyi ba?" tab'e baki Lady tayi tace "wallahi Uncle ta girma yarinyar nan" ku kyaleman Baby hakanan mana kun sa mata ido, Yaya ta fad'i haka, tashi Lady tayi tace "mun daina" tana fad'ar haka ta wuce, gwalo Intee ta masu ta k'ara shigewa jikin Yaya..

            *wacece Inteesar*
   Inteesar d'iyace ga k'anwar Uncle ita kad'ai garesu, iyayenta sun bata gata saboda duk abinda takeso suna mata, amma duk da gatan da aka bata bai hana su bata ilimi ingatacce ba, last yr ta k'are secondry school yanzu haka tana jami'a, Alqalam University tana aji d'aya...
   Ba k'aramin shak'uwa ke tsakanin Intee da Yaya ba Inteesar nasan Yaya sosai haka itama Yaya tana santa sosai, yawancin  hutun ta gidan Yaya take yinshi..
   Yanzu haka wani hutun ta samu ta tazo...

    "Bruh dan Allah tashi muje gidansu Charming guy d'innan wlh shi kawai nakesan gani" shiru yayi kamar bai jita ba, ihu ta mashi cikin kunne da hanzari ya d'ago d'aga hannu yayi zai duketa ta matsa tana dariya..
   B'ata fuska tayi tace "dan Allah katashi muje Allah shina kesan gani" wai idan kin ganshi mi zaki ce mashi? Dariya tayi tace "kai dai kaini kawai zaka gani" tsoki yayi ya mik'e yace wlh kin cika fitina" dariya tayi tace "naji dai mutafi" haka suka fita suka bar gidan..
   Wuri ta samu ta zauna tana hawaye dan duk abinda yafaru gaban idon tane, miyasa Intee ke shige ma Fu'ad haka? Mitake nema wurinshi? Miyasa duk idan zatayi magana sai ta sako Fu'ad, tambayoyin da takema kanta wanda ita kanta bata san amsarsu ba...
   Wata zuciya tace mata miye na damun kanki akan abinda bai shafeki ba idan ma sanshi takeyi miye ruwanki ke ai ba sanshi kikeyi ba, "No" tafad'a da k'arfi tashi tayi tabar parlourn ta nufi d'aki tana kuka..

  Basu dawo gida ba sai gab magrib, shigowa sukayi suna dariya, Intee tace "bruh charming guy fa ya had'u dayawa kaga yanda yake magana" dariya yayi yace "yarinya bakima ga komi ba sai nan gaba guy d'in classy man ne duk abinda zai sa maki to designer ne zai saka" ihu tayi tace "wlh haka nakesan guy muryanshi kad'ai abin sauraro ce nifa da yana magana da lion voice d'inshi bansan yadaina" dariya Aflan ya kwashe da ita yace "kuma saurin sabonku yau yaban mamaki" wani shu'umin dariya tayi, daidai ta zauna...
   Duk abin nan da suke fad'a Lady na kallonsu takaici yasa ta kasa furta koda kalma d'ayane..
   "Bari na shiga d'aki nayi wanka" Aflan ya fad'i haka, "olryt bruh saika fito"..
   Kallon Lady tayi tace "Anty Lady na gaji dayawa fa yau munsha yawo da Charming guy harda turare ya siyaman designer" daidai tana fito da turaren da yabata..
   Hararta Lady tayi ta bar parlourn, tab'e baki Intee tayi ta kwashi kayanta tayi gaba..

   Tana shiga d'aki ta wurgar da ledar hannunta kan gado, wash nagaji wallahi dayawa, juyawa tayi ta kalli Lady tace "waini Anty Lady miyasa idan na maki magana saiki harareni?" Shiru tayi kamar bata jita ba, marairaice Fuska tayi tace "pls Anty Lady dake fa nake" kallonta tayi tace "rawar kanki ke had'ani dake" dasauri tace "zan rage to" dariya Lady sosai tayi tace "bama dainawa zaki ba ragewa zakiyi?" Eh mana, girgiza kai tayi tace "Allah ya shiryaki, ni bari nayi alwalla" dariya Intee tayi..

©FEEDOH DEEDOH

JARABAWA TACE Where stories live. Discover now