111~115

1.4K 74 0
                                    

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                          (NWA)



                1⃣1⃣1⃣➖1⃣1⃣5⃣

WAYE FU'AD?
   
    Alh Sani d'an k'auyen katsina ne jibiya, yana da mata guda mai suna Zulaihat auren zumunci akama Alh sani da Zulaihat saboda ta kasance d'iyar yayan babanshi, Alh Sani d'an kasuwa ne kuma katsina yake zaune da matarshi, Allah yabashi dukia mai tarin yawa, Alh Sani da Hajiya Zulaihat suna da yara shida Aisha itace farko sai Asma'au sai Ramlah sai maryam sai Amina, tun daga kan Amina Hajia Zulaihat bata sake haihuwa ba sai da ta shekara biyar kana Allah yabata ciki murna Alh Sani yayishi, cikin na shiga wata tara ta haifo d'anta mai kama da ita, murna wurin Alh Sani ba'a magana, ranan suna yaro yaci suna Fu'ad..
   Haka Fu'ad ya taso cikin so da k'aunar iyayenshi da yayyenshi komi suka samo Fu'ad, amma duk da irin sanda ake mashi bai hana aka bashi ingattancen tarbiya da ilimi ba...
   Yana girma kyanshi na k'ara fitowa, Fu'ad miskiline na k'arshe hayaniya bata dameshi ba shiyasa ko tarkacen abokai bai dasu abokinshi d'aya Habeeb, kuma halinsu d'aya shima miskiline saidai bai kai Fu'ad ba..

   Fu'ad na aji d'aya jami'a anan Alqalam University katsina Allah yama mahaifinshi rasuwa, bak'aramin tashin hankali wannan family suka shigaba amma daga k'arshe suka dangana sun san duk mai rai mamaci ne..
   Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har ya k'are jami'a, kuma duk yayyenshi sunyi aure dan haka dagashi sai Ammi cikin gida..
   Ammi ta d'auki san duniya ta d'orama Fu'ad ko kad'an batasan taga abinda zai b'ata mashi rai, kuma duk abinda yakeso tana k'ok'arin taga ta bashi...

   Tunda Fu'ad ya shiga jami'ah yan mata ke kawo kansu amma ko kad'an basa gabanshi bai ko kulasu saboda miskilanci irin nashi...
   Fu'ad na k'are degree d'inshi ya jona masters cikin ikon Allah bai tab'a samun matsala ba har ya k'are yana k'arewa yasamu aiki dawani company..

   Fu'ad handsome guy ne ajin farko yana da cute pink lips yana da tsawo yana da bud'edd'en k'irji ga 6 packs, muryarshi irin lion voice d'in nan ne ga sanyi ga dad'in sauraro in fact Fu'ad ya had'u namiji ne to d core..
   Shiyasa mata idan sun ganshi suke rud'ewa, amma sam basu gabanshi dan ko kallon inda suke baiyi bare har ya yabasu..
   Shekararshi talatin amma babu maganar aure gabanshi duk wanda yamashi maganan aure ranan yini zasuyi suna fad'a dan shi yace baida lokacin mata. Kuma Ammi ta sakamashi ido saboda d'an lelenta ne, kuma tace lokacine aure idan lokacinshi yayi zaiyi
   Shiyasa koda yazoma Ammi da maganan yaga wata, abun yabata mamaki saboda itace rana ta farko daya kawo maganan wata da sunan yanaso, tayi murna sosai sai fatan Allah yasa matarshi ce..

   Nidai yar_ficika murmushi nayi dan nasan Lady bazata tab'a sanshi ba saboda yanda ta tsani maza..hmm mudai je zuwa..
            **********************

   Aflan dan Allah tashi muje jifatu inasan nayi siyayya, tab'e baki yayi yace "yanzu daga dawowa na zaki fara jana yawo?" Hararshi tayi tace "barshi idan iskanci zakaman, dama kayan gida ne zansiyo komai yakusa k'arewa gasu Yaya zasu dawo gobe.."
   Tashi yayi yace "niba surutu na tambayeki ba muje" duka ta d'aka mashi tace "ka rainani dayawa wlhi", harararta yayi yace "Allah zan fasa inga idan kina iya fita ke kad'ai ga Deeyerh bata nan" kunne ta kama tace "yi hak'uri please" dariya yayi yace "muje matsoraciya"...

   Tafe suke suna fira har suka isa Jifatu, cikin kwanciyar hankali tagama siyayya tana gamawa ta biya kud'i aka saka masu kaya mota..

   Waya yake sam hankalinshi bai tare dashi k'ana nan kayane jikinshi na company tomy hilfiger farare dayake ma'abocin fararen kayane ba k'aramin kyau kayan suka mashi ba kayan sun k'ara fito da kyanshi, duk wanda ya kalleshi sai ya k'ara kallonshi saboda yanda kayan suka karb'i jikinshi, ji tayi tayi karo da wani abu har wayar hannunta ta fad'i tayi ratsa ratsa, da masifa ta d'ago amma ta kasa cewa komai sakamakon kallon da yatsareta dashi...
   Duk'awa yayi ya d'auki wayar yace "pls kiyi hak'uri ba dagangan bane ba wlh ban ganki ba" issokay abinda tace kenan..
   Mik'a hannu tayi zata karb'a wayan, yak'i mik'a mata ido ta zaro tace "mi hakan yake nufi?" Dan ya fara bata haushi, kibari zan kawo maki wata pls, wata harara ta wurgamashi tace "angayama ka ina buk'ata ne?" Da sauri yace "ah ah"..

   Kallon raini tamashi tace "to bana buk'ata bani wayana.."

   Jiki mace ya mik'a mata, gefe d'aya Aflan ya koma yana kallon dirama  shi burgeshi ma sukayi..
   Fizge wayanta tayi ta wuce, dan Allah ki tsaya kiji cak ta tsaya bata kuma juyo ba, "zan iya samun number d'inki?" Abinda yace kenan "bazaka samu ba" tana kaiwa nan tayi gaba...

   Dafashi Aflan yayi yace "kayi hak'uri da abinda ta maka" murmushi yayi yace "bakomai, amma dan Allah ya kake da ita?" Anty nace Aflan yabashi amsa..
   Miyasa Anty d'inka take da zafi haka? Allah inasanta san da zan iya rasa komai saboda in zauna da ita, inamata san da ko Naufal baima Hudah ba, ka taimakeni ina k'aunarta kamar yadda Hamza ke k'aunar Dijah, zan mata hallaci sama da wanda Moh yayima Nafeesah. Binshi da ido Aflan yayi tabbas yabashi tausai amma yasan kafin ashawo kan Lady sai an shirya. Kuma tabbas ya yarda da san da yake mata..
   Kafad'arshi ya buga yace " bata da zafi asalima bata da masifa sanyi hali gareta, akwai abinda ke damunta ne "miyeshi?" Da sauri ya tambaya karkadamu zaka sani a hankali, kuma inaji araina zata soka, amma saika daure" da sauri yace "zan iya daure komiye indai zan sameta.."

  Toh yanzu kaban number d'inka daga yanzu kazama abokina, ba musu Fu'ad yaba Aflan number d'inshi, miye sunan? FU'AD nikuma AFLAN, bankwana sukayi Aflan yawuce..

   Aflan ya kira sunanshi, tsayawa Aflan yayi ya juyo tare da murmushi, k'arasowa yayi yace "miye sunanta? Koshi ya rageman rad'ad'in danakeji" murmushi yayi yace "NAFEESA amma muna kiranta da Lady," masha Allah na gode, nan sukayi bankwana kowa ya wuce..
   Yana isa mota ya bud'e shiga tayi ta rufo k'ofar da k'arfi, yana shigowa ta wurga mashi harara tace "wlh kayi sa'a key d'in na hannunka dana tafiyata"..
   Sai me? Zan fasa komawa gida dan kin tafi? Wlh Lady abinda kike baki kyautawa ke shikenan abu bai wucewa wurinki, shi wannan bawan Allah miye laifinshi, baiface yana sanki ba amma kiga yanda kika mashi gaskia banji dad'i ba, karkaji dad'in mana aidama bance kaji ba, kuma komi namashi bai shafeka ba.. fizgar mota yayi ya nufi gida, ba wanda ya k'ara cema wani k'ala har suka iso gida...


©FEEDOD DEEDOH

JARABAWA TACE Where stories live. Discover now