page 1~5

6K 260 9
                                    

JARABAWA TACE

yar_ficika

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


BASED ON TRUE LIFE STORY

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

         1⃣➖5⃣

NOTE:
Assalamu Alaikum my beautiful people muna mai baku hakuri akan rashin posting na MATATA GIMBIYATA wannan yafaru ne na sanadiyar sace wayar yar uwarmu Jiddah Ja'o da akayi amma in shaa Allah takusa dawowa, data dawo zakujimu akai akai, ina fatan zaku kasance tare damu... Mungode sosai❤

Shimfid'a
      Garin katsina gari ne dake cike da Jinsi iri iri, Gari ne dake da tarin ni'ima, garin Katsina gari ne da yake da karamci duk wanda yazauna garin dole yaso garin saboda irin karamcin mutan garin. Shiyasa Hausawa ke ma garin kirari da Katsinawan dikko d'akin kara kunya garesu ba dai tsoro ba, Katsina garin malamai duk in kaga Jahili bak'one....

      Kwance take tayi rub da ciki da alamun kuka takeyi, da sallama aka shigo d'akin sauri tayi ta goge hawayen da suka gangaro mata, murmushi matar da tayi sallama tayi tace "idan kuka na maganin matsalan da kike ciki ai saikije kitayi" nasha gaya maki adua zaki yi bawai kuka ba amma kin kasa ganewa, kowane bawa da kika gani akwai irin jarabawan da Allah kemashi, ki gode ma Allah ki karb'i jarabawanki ki fatan Allah yasa ki cinye jarabawanki, kika rasa ma iyayenki kika hak'ura bare abinda kikasan in shaa Allah Alkairi na gaba..
      Hawayen da suke mak'ale kuncinta suka gangaro mata tace "kiyi hak'uri yaya wlhi bansan ina kukan bane ba" dan Allah ki cigaba da tayani da adua, amma nikam wannan jarabawan taman tsauri, tsawa ta daka mata baki da hankali komi? Kisan irin abinda kike fad'a shin kanki farau wata ma ta shanye abinda yafi naki kuma ta hak'ura bare ke..

       Zama tayi ta dafata murya k'asa tace "nasan abin akwai ciwo amma kiyi hak'uri ki cigaba da adua" in shaa Allah everything will be fine kinji my Lady Kin manta abinda doctor yace maki? zaki iya rasa ranki idan har kika cigaba da saka damuwa a zuciyarki kinaso na rasaki ne? girgiza kanta tayi Alamar "Ah Ah" toh dan Allah na rok'eki ki daina saka damuwa a zuciyarki, ki tunafa ke kad'ai gareni, fad'awa tayi jikinta tace "zan kiyaye duk abinda bakiso namaki Alk'awarin zan rage damuwa amma nasan ba zan daina ba kwata kwata..           
      D'agota tayi hawayenta ta share mata tace "namanta kinyi bak'uwa fa" da sauri tace "zainab right?" Girgiza kai tayi tace "yeah shez d one" tana ina? K'ofa ta gwada mata, tsaye take ta hard'e hannuwa tana tausayin halin da k'awarta tashiga dode tak'i gaya mata amma yau ya zama tilas ta san miye damuwar k'awarta..

      Da gudu ta tashi taje ta rungume Zainab tureta tayi tace "baruwana dake" da sauri ta d'ago kai tace "mikuma na maki?" Murmushi tayi tace "tun yaushe nake binki kigayaman damuwanki amma kink'iya saiki ceman bakomai ko ban kai nasan miye damuwarki ba?" Ai na d'auka yanzu mun wuce k'awaye mun zama yan uwa, dafata tayi tace "karki damu Zee in shaa Allah zan gaya maki damuwata" yaushe? Murmushi tayi tace  "gobe in shaa Allah" rungume juna sukayi...

      Yaya tace "Zainab inafatan idan kikaji labarinta zaki dinga bata shawara ta kwantar da hankalinta, ita kad'ai ta rageman gashi itama ta kamu da ciwon zuciya bansan na rasata.." Zainab tace "in shaa Allah yaya l''ll try my best naga na bata shawaran kirki" godia Yaya tayima Zainab kana tafita tabar masu d'akin....

      Tashi tayi ta kawo ma Zainab drink, zuba mata tayi ta mik'a mata karb'a tayi ta kurb'a.. aje cup d'in tayi ta kalleta gobe around which time zanzo? Murmushi tayi tace "duk sanda kika samu time dama yaya zasuje KD ita da uncle kinga saikizo da wuri"...
      Fira suka dingayi sai marece Zee ta tafi gida da Alk'awarin gobe zata dawo domin jin labarin K'awarta...

      Mai aiki ce ta shigo mata da abinci, kafin ta aje tace mata karki aje na k'oshi, juyawa tayi da abinci komi ta tuna oho kiranta tayi tace "ta aje abincin"...
      Bawani da yawa taci abincin ba ta koma ta kwanta, yarinyar ce ta sake shigowa da sallama, Anty kizo inji Uncle yana kira, tashi tayi jiki sake ta d'auki mayafi ta nufi hanyar falo da murmushi ta isa falon zama tayi kusa dashi tace "Uncle sannu da dawowa" cikin sakin fuska yace "sannu Lady hope kinci abinci?" D'aga kai tayi tace "eh" Yaya tace "wani abinci takeci?" Tadai tsakura murmushi yayi yace "koma dai yane tunda taci shikenan.."
      Lady rufe idonki ki mik'oman hannunki, ba musu tayi yanda yace kwali ya aza mata ga hannu kana yace ta bud'e a hankali ta fara bud'e idonta bata ajesu ko ina ba sai kan kwalin ido ta zaro ganin abinda ta gani, da sauri ta kalleshi Uncle Iphone7 murmushi yayi yace "taki kumace" tashi tayi ta fad'a jikin Yaya tana hawaye d'agota tayi ta share mata hawaye tace "to miye na kuka?" Murya k'asa tace "bansan da bakin da zan maku godiya ba ko iyayena da suna da rai iyakar abinda zasuyiman kenan" Ucle na gode Allah ya k'ara arzik'i, yace "AMIN LADY"  kedai ki daina saka damuwa a ranki in shaa Allah zamuyi maki duk abinda kikeso indai baifi k'arfinmu ba kinji Lady? D'aga kanta tayi, kallonta Yaya tayi tace "toh aje asaka wayan chargy ko?" Tashi tayi ta nufi d'akinta da gudu tana murna....

© FEEDOH DEEDOH

JARABAWA TACE Where stories live. Discover now