page 61~65

1.4K 89 0
                                    

JARABAWA TACE


yar_ficika



NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
                     (NWA)



THIS PAGE IS FOR YOU MY AUNTIES

ANTY MAIJIDDA MUSA
ANTY AMINA KAURA
ANTY SADEEYA JEGAL



                    6⃣1⃣➖6⃣5⃣

      Tunda Aflan yadawo na rage damuwa, kullum sai ya tsareni naci abinci haka zanci ko inaso ko banso, haka da mungama abinda muke zamu fita yawo. Zan iya ce maki kashi tamanin da tara na damuwa ta ya rage, saboda iya gwargwado Aflan na kula dani.
      Saida Aflan yaga na warware babu wata matsala tare dani kana ya koma makaranta, randa zai tafi da kyar aka rabamu dan abinda ya faru dani ya dawoman sabo. Ni kuka Aflan kuka, bazan manta ba bayan mun kaishi airport har ya juya ya tafi, ya sake dawowa kallon su Uncle yayi yace "Daddy Mammy ga amanar Lady nan yanzu taimakon ku take nema dan Allah kudinga tsareta taci abinci" murmishi Uncle yayi ya dafa kanshi yace "karkaji komai My Boy in shaa Allah zamuyi iya bakin k'ok'arinmu" Kallon shi Yaya tayi tace "itama saika ja mata kunne dan kasanta da taurin kai"..
      Kallo na yayi yace "Lady dan Allah kidinga cin abinci, ya kamata ki cire damuwa a ranki ki d'auka sabuwar rayuwa zakiyi, ki manta da Saleem a rayuwarki sai kiga kinci nasara so kike kima kanki illa? Shifa ya manta dake saboda yayi aurenshi yakamata ki farka daga wannan mugun soyayyar" tabbas nasan gaskia Aflan ya fad'aman, murmushi nayi nace "in shaa Allah zan baka mamaki zan koma Ladyn da" sosai kowa yaji dad'in maganar danayi, rungumeni yayi yace "datz my yar k'anwa" duka na d'aka mashi nace "kafa raina ni" dariya yayi yaja trolley d'inshi yawuce yana d'aga mana hannu....

     Tun daga sannan na cire komai araina, kowa yaji dad'in yanda nakoma normal. Kullum muna mak'ale a waya nida Aflan yana k'ara kwantar man da hankali. Haka b'an garen karatuna ban samun wata matsala, saidai tun bayan tafiyarki ban sakeyin wata k'awa ba..
      Watarana na dawo daga makaranta, a gajiye na dawo da sallama na shigo cikin gida, karo naci da wani d'an matashin saurayi falo, zahirin gaskia bansanshi ba, cikin sakin fuska ya amsaman sallamata. Gaidashi nayi ya amsa tare da tambaya ta makaranta, saida nakai k'ofar d'akina kana na bashi amsa da lafiya..
     Da daddare muna falo muna fira, kallon Yaya nayi nace Yaya waye d'azu yazo? Sameer ne babanshi mutumin Uncle ne sosai, eyyah kawai nace, Uncle yace "kinganshi ne? Amsawa nayi da "Eh"...

      Tun daga ranan kullum sai Sameer yazo gida, gaisuwa kawai ke had'ani dashi wani lokacin ma ban gaidashi daya shigo zan nufi d'akina na barshi dasu Yaya..
      Wata ranan asabar ina zaune nikad'ai bakowa gidan, sallamarshi naji tsoki nayi cikin raina nace shidai wannan ya cika naci toh yau bakowa gidan, ban ankara ba naji yace "Lady baki amsa sallamata yau?" Yak'e nayi nace "kayi hak'uri banji baneba" murmushi yayi yace "bakomai" inasu Anty? Basunan abinda nace kenan..
       Deeyerh na kira ta kawo mashi ruwa da lemu, tana ajewa na kwashi wayoyina natashi, nakai baki k'ofa kenan na tsinkayi muryanshi yana ceman ina zaki? Shiru nayi kamar ban jishi ba, cikin marairaicewar fuska yace "dan Allah Lady kiyi hak'uri kizauna magana zanyi dake".

      Ba yanda na iya na dawo na zauna, cup d'in hannunshi ya aje ya kalleni, murmushi yayi yace "Lady miyasa baki san yin fira dani?" Babu komai abinda nace mashi kenan, kiyi hak'uri Allah tun randa na fara ganinki naji ina sha'awar yin abota dake, ke kuma da alamu haushi nake baki..
       Bansan sanda na zaro ido ba nace "haushi kuma?" Eh mana in ba haushi ba miyasa baki tsayawa muyi fira. Yanzu duk ba wannan ba kinga tunda na dawo 9ja bansan kowa ba bani da aboki bani da k'awa, pls ki daure ki zama aboki na..

      Bansan sanda na saki dariya ba nace "Sameer da abun dariya kake" ashe kinsan sunana? Shine baki tab'a fad'a ba? Yau na fad'a amsar da nabashi kenan
      Bakice komai ba? Bazanyi ba, zaro ido yayi yace "miyasa?" haka kawai..
      Mik'ewa tsaye yayi ya kalleni yace "shikenan na gode".....

©FEEDOH DEEDOH

JARABAWA TACE Where stories live. Discover now