chapter 8

2.9K 128 35
                                    

🎻💕 EMRAAN ZAYD 💕🎻 page 8⃣
© Jeeddah ja'o🏵
www.jeeddahjao.WordPress.com

Garden ya wuce direct ya zauna kan wata resting chair gami da d'aga kansa sama ya kwanta jikin kujerar yana lilo da ita. Gaba d'aya yaji gidan ma ya fita kansa saboda wannan Amrah d'in, " Mtsew ! Yaja tsuka ya mik'e yana kallon wajen da tayi ta watsa masa ruwa d'azu ,kanshi ya kawar gefe kafin ya mik'e ya bar garden d'in bai zame ko ina ba se garage ya d'auki motar sa yaja ya fice daga gidan. Affan yana kallon tym d'in da ya fita yasan yau ran Emraan a b'ace yake don haka bai ma k'ira shi ba ,ya koma cikin gida...........

7:00 am...
Washegari....

Affan da Emraan ne zaune a falour suna kallon news, kamar daga sama Emraan yaji an kwara masa shayi mai uban zafi.
" OUCH!!!! " abunda ya iya cewa kenan kafin ya mik'e yana salati bai jira me zata ce ba ya d'aga hannu zai kai Mari ,da sauri Affan ya rik'e hannun sa yace " Haba yaya, tuntube fa tayi!"
Emraan ya dubeshi cike da bacin rai yace " And so what? Tuntube ma se a kaina zata yi? I believe baki da hankali amma Zan saita miki k'wak'walwa wlhy ,wannan dabi'ar taki ta dabbobi wlhy se na cire miki shi" ita de Amrah bata tanka ba illa shagwabe baki da tayi tana hawaye shi kuwa ya mik'e ya wuce d'aki fuuu rai a b'ace ,Ganin haka Affan ya bi bayan shi da sauri.

" Haba yaya! Mesa bazaka yi hak'uri da ita bane? I believe ka san irin society d'in da ta taso a ciki, hak'uri zaka yi,
Kuma kasan me kuwa yaya?" Emraan ya girgiza kai alamar " A'a"
Affan ya k'arasa bakin k'ofa yace " wlhy kun dace , she's beautiful and you are handsome! Nidai in zaka ji ta tawa kawai mu samu Dad kaga daga nan se musha biki"
Emraan tsabar haushi bai san lokacin da yabi Affan da gudu ba suna zagaye falon Emraan saida suka gaji duk suka zube a k'asa suna dariya Affan ya dubi Emraan yace " Yaya , ba lallai ne ta kasance yadda kake so ba , amma kuma masifan ka da fad'an ka bazai sa ta gyaru ba , irin wad'annan lallaba su ake yi saboda kasan fa hankalin mu da na mutanen Chan fa ba d'aya bane pls ka d'an rage zafi mana"

Suna cikin hirar su mai dad'i Dad yayi sallama fuskar sa d'auke da murmushi , tabbas yaji maganganun su,zama yayi kan kujera yana kallon su, A hankali Emraan ya zauna yana kallon Dad suka had'a baki wajen gaida shi,kana ya amsa cike da walwala da annashuwa kafin yace"

" Emraan aiki ne ya taso yanzun nan, saboda haka akwai meeting da zaka yi with the board saboda haka you'll take a flight to Canada duk wasu shirye shirye P. A ya kammala jirgin ka zai tashi by 8:30 am so pls ka shirya , nd pls do your best! Ka tabbatar mun fi kowanne company investing a business d'in, I believe kasan how important it is saboda haka ba se na tsaya surutai ba , mu kam gobe insha Allah zamu tattara mu wuce Chan kaduna Affan zai kula da belongings naka don haka just do your best , Allah ya taimaka"
Sosai Emraan yaji dad'i ,at least zai huta da ganin mahaukaciyar yarinyar nan ( Amrah) don haka ya mik'e yana murmushi ya nufi d'aki bai ma ce komai ba, Dad ya fahimci yana cikin walwala amma bai san dalili ba Affan ya dubi Dad yace " Am surprised Dad, yaya Emraan da baya k'aunar tafiya waje don meeting shine yau yake murmushi haka?" Dad yace " Hmm bar wannan yayan naka , tashi muje in baka wani aiki " Affan yace " pls Dad wlhy wannan aikin company d'in akwai wuya sosai , Dad Allah yasa ba shi bane" yana rufe baki yaji rankwashi " Toh da wanne kake tsammani? Come on zo muje !!" Affan ya bi bayan Dad yana Sosa kai ................

Finally Emraan zai yi nesa da Amrah na y'an wasu kwanaki , while a wajen Amrah da su Affan kuwa new life zasu tarar inda yanzu zasu koma Chan family house , ko yaya alamarin zai kasance???

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA 💃🏻

Jeeddah ja'o🏵

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 18, 2016 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

EMRAAN ZAYDWhere stories live. Discover now