PART (3)

1.4K 71 2
                                    

🎻💕 EMRAAN ZAYD 💕🎻 page 3⃣
© Jeeddah ja'o🏵
www.jeeddahjao.WordPress.com

     Tafiya suke cikin nishad'i iska mai sanyi na yammaci yana kad'awa yayinda glasses d'in motar duk a sauk'e suke , Tasleem dake zaune setin Emraan ta bayan shi ,ta tashi daga seat nata tana mai lankayo hannuwan ta biyu ta wuyan shi sannan ta lek'o fuskar shi ta gefe tace " Yaya, pls ina son kud'i" a marairaice tayi maganar kuma a tsanake.

    Ba tare da ya juyo ba tace " Princess ! ( sunan dayake k'iran su duk dashi ) me kuma zakiyi da kud'i ? Yaushe na baki twenty thousand?" Tabe baki tayi tace " yaya fa wancan nayi dinki da shi wannan kuma Zan yi siyayya ne na birthday na kuma wlhy yaya ina facing wardrobe malfunction duk kayan are outdated"
  Murmushi Emraan yayi yace " naga alama so kike ki zama like a spoilt brat ! Don't worry I'll take you all for shopping kafin nan de yanzu mu d'auko Dad ,idan mun kaishi gida mukayi sallah I promise ko dinner bazamu ci a gida ba! We'll go shopping, have some snacks and ice cream se kuma mu tafi muga movie! Hakan yayi??"

     Duk suka sa ihu cikin motar " yeeehh!!! " dariya sosai Affan yayi yace " Yaya toh ni kuma me Zan samu? Kasan ni dai bazan bika shopping ba muddin wannan k'atuwar tana tare da ku! Kar muje ta bamu kunya ,haka ma wancan lokacin tun daga shopping mall ta Fara cin chocolate kamar wata y'ar k'auye ,wlhy yaya ban ga amfanin karatun ka na health ba tunda bazaka dakatar da ita wannan shegen ciye ciyen Nata ba ! Mutum sekace an hura balloon! Koda yake Tasleem bakya buk'atar balloons next week a decorations na birthday naki don ga wata nan ,kinga se mu yi hanging nata a sama  kuma zata yi kyau.

     Duk da dariya ta taho wa Tasleem bata san lokacin da ta gimtse shi ba kasantuwar ta hango yanda Emraan ya turnuk'e fuska . Basu ankara ba sai ji sukayi yayi parking motar ya zagaya side d'in Affan ya Fisgo shi daga cikin motar " Ka fita min daga mota ! And believe me you! Idan har ka sake maimaita irin haka abun da Zan maka se ya fi yanda kake zato!* yana kai wannan ya koma mota ya ja Affan kuwa ya daskare wajen yana fad'in

   Lallai ma yaya! Kawai daga magana! Se. Ya yi waje Dani? Gaskiya am embarrassed !! Ji yanda ake kallo na big guy da ni Mtsew!!" Ya fad'i hakan ne yana zaro wayar sa daga aljihun sa hannun sa guda kuma yana tsayar da taxi.

INTERNATIONAL AIRPORT....

        Da gudu y'an matan suka nufi inda yake gami da manne masa a tare suka fad'i" welcome home Dad!!" Dariya yayi sosai yana Jan su a jiki " My lovely daughters! Yaya kuke?" Lpya lau daddy just that we missed you so much"
   " ha ha ha ! I know! Nima nayi kewar ku ,amma ba gashi Allah ya dawo Dani ba?" Kai suka girgiza yayinda shi kuwa Dad ya maida duban sa ga Emraan dake tsaye yana murmushi yace

    " Emraan, yaya aiki?hope all is well ? You look stressed out" murmushi Emraan yayi yana daidaita zaman trolley d'in Dad yace " Alhamdulillah Dad! Kawai de d'azu nai headache ne " Dad yace Subhanallah toh Allah ya sawwak'e " duk suka amsa da "Ameen" sannan suka cigaba da tafiya cike da k'auna abun gwanin burgewa kowa kallon su yake yadda Dad ke Jan y'ay'an sa a jiki  har suka isa parking lot domin d'aukar motar su, duk suka shige Emraan ma ya sa kaya a booth sannan ya shiga ya Fara Jan mota , Farin cikin dake d'auke a fuskokin ba ya misaltuwa ,suna k'aunar Junan su ,hakan yana burge Dad sosai yana sa hankalin shi ya kasance cikin ruwan sanyi ,cike da k'auna yake kallon su yana murmushi....

     Basu ankara ba sukaji Emraan ya ja birki " keeeeeeeee!!!" Duk cikin su ya dura ruwa sun 'kank'ame rigar Emraan saida suka ji shiru motar ta tsaya sannan suka bud'e idanuwan su . A fusace Ya fita daga motar ya Kama kunnen sa " Affan! Kai wanne irin mutum ne ehen? Wannan abunda kayi is very risky! Tsabar rashin hankali yaya zaka shige min gaban mota?"
Affan ya ce " Amma de yaya ka taimaka ka sake min kunne na , pls barin sake ba I promise " kai Emraan ya girgiza ya juya ya shiga mota ya zauna yana kallon Affan wanda ke faman Sosa kunnen sa. " Kai! In bazaka je ba mu tafiyar mu!  " washe hak'ora Affan yayi ya zagaya ya bud'e k'ofa ya shiga..

  " Dad Sannu da zuwa! " Dad yayi murmushi yace " Affan my son yaya karatu?" Affan ya Sosa 'keya yace Dad, Alhamdulillah" Emraan ya daka masa harara ta madubi yace " Dad wanne karatun ? Mutumin da ina fita aiki baya komai se waya da chicks dinshi kaide abar kaza cikin gashinta "
   Bata rai Affan yayi yace " Hmm toh kuma na yaushe ? Tunda ka riga ka tona kazar daga gashin ta ! Nifa yaya ka saka min eyes ! Ba gwara ni ba?.... Sosai Dad yayi dariya shi kuwa Emraan bai tanka masa ba ya cigaba da da tuk'in sa yana murmushi.................

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA 💃🏻

Jeeddah ja'o🏵

EMRAAN ZAYDWhere stories live. Discover now