PART (4)

1.3K 63 1
                                    

🎻💕 EMRAAN ZAYD 💕🎻 page 4⃣
© Jeeddah ja'o🏵
www.jeeddahjao.WordPress.com

       Bayan magariba Emraan ya kwashi su Hanan suka fita Dad ma bai sani ba , Affan kad'ai aka Bari a gida.
   Shoprite 🍾 suka shiga a nan sukayi exhausting time nasu ,ganin basu da niyyar fita da wuri Emraan ya fita don yayi sallah ,kasantuwar ya bar musu credit card nashi ko da ya dawo ma a mota ya zauna don ya gaji tun kafin ma Aje ko ina, haka kowa ya fito da kaya nik'i nik'i a hannu ,kawai booth ya bud'e musu suka zuba kayan sannan suka shiga motar ya ja , gidan abokin sa ya sauk'e su sukayi sallar isha sannan ya wuce da su Silverbird movie theater suka kalli american fairytale (Maleficent ) they really enjoyed their brothers company fuskar su d'auke da farin ciki Tasleem ta matso kusa da shi yana k'ok'arin bud'e mota ta Kama hannun sa tace " yaya kaga yanda Hanan ta fasa min screen na waya!" Murmushi yayi yace " yi hak'uri princess bata sani bane " hannu yasa cikin aljihun sa ya ciro wayarsa k'irar IPhone 7 ya mik'a Mata yace " gashi se ki cire min Sim d'ina ki sa min a naki ke kuma Hanan bana son rigima !" Sosai Tasleem tayi hugging nashi tace " wow yaya thanks ! You are the best! " hanan ta juya idanuwan ta ta furzar da iska daga bakin ta tace " barin sake d'auka miki waya ba  kuma " Tasleem tayi dariya tace " oho de ai da yafi miki ! " shidai Emraan yayi dariya yace " come on hop in the car ! Ku shiga mu tafi its getting late!" Ba musu suka shige mota suka d'au hanyar gida........

     Falon shiru babu kowa se Affan kwance k'afa daya a 'kasa d'aya a sama ya rungume remote se bacci yake yi hankalin sa kwance , Tasleem tayi dariya ta yi sand'a a hankali ta isa inda yake ta fiddo wayar ta tana ta capturing pics nashi , Hanan tana ta dariya. Emraan ya girgiza kai yana murmushi ya kashe switch na wutan falon se ya rage beam light sannan ya haura upstairs zuwa d'akin sa , su Hanan kuwa saida suka huta kafin suka haura zuwa bedroom nasu cike da gajiya ko kaya basu cire ba balle wanka tsabar sun gaji ,haka suka zube Hanan ko takalman ta bata cire ba......

       Dad ne ya fito falo yana zagayawa kamar yadda ya Saba , ya ga Affan kwance yana bacci ,  ganin an rufe k'ofa ya tabbatar su Emraan sun dawo don haka ya tada Affan ya tafi d'aki, ya bi su kitchen ya kashe wuta sannan ya haura zuwa d'akin su Tasleem ya gansu duk babu shiri , murmushi yayi ya nufi inda Aysha take ya gyara kafafun ta sannan ya rufa Mata blanket  ya zare wa Hanan takalman ta sannan yayi musu addua ya juya ya fice bayan ya kashe wutan d'akin , yana fitowa daga flat nasu ya hango k'ofar d'akin Emraan rabi a bud'e don haka ya nufi wajen zai rufe daidai lokacin Emraan yazo shima zai rufe ,suna had'a ido duk sukayi dariya Emraan yace " thanks Dad ,yanzu fa sha d'aya ne kamata yayi ace kana bacci " Dad yayi murmushi irin na manya yace " Wannan abun da na Saba da shi ne each and every night! Its for your safety , kar ka damu my son! Am by the way ! Akwai maganar da zamuyi mai muhimmanci gobe in Allah ya kai mu saboda haka Kaje ka kwanta don zaka sauk'e ni a office da k'arfe takwas "

    Emraan yayi murmushi yace " Alright Dad Allah ya kaimu goben gud night" nan sukayi sallama Dad ya wuce side nasu shima Emraan ya koma d'aki shima yayi shirin kwanciya...........

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA💃🏻

Jeeddah ja'o🏵(30/10/2016) 💞🎸EMRAAN ZAYD 🎸💞

      Karfe bakwai da rabi daidai.
Tsaye yake gaban madubi yana d'aura ash silky tie dinshi ,Aysha ta shigo sanye da uniform ,amsa Sallamar ta yayi sannan ta k'araso inda yake tace " Bro, pls ka kaini school yau" Yana fesa turaren shi bai san lokacin da ya ajiye ba ya juyo yana kallon ta ya durk'usa a gaban ta yace " Me yasa princess? Akwai matsala ne ? " kai ta girgiza tace " eh , kasan wannan Yaron farouq? Shine yake bullying d'ina wai y'ar tulik'a kawai don na yi magana suka yayyaga min takarda kuma suka watsa min ruwa da aka tashi , ni gaskiya yaya Kazo kayi musu magana su fita a harka ta" shiru Emraan yayi yana kallon ta cike da tausayi yace ok muje kiyi breakfast se in yi dropping naki inyaso se inyi magana da school authority d'in"
   Tsalle tayi tana dariya sannan ta d'auka masa briefcase nashi ta Kama hannun shi suka fita yana faman saka cufflinks nashi  yana murmushi " toh sake ni mana princess! Ban gama shiryawa ba " A'a yaya muje mana kowa yana jiran mu breakfast is ready !" Sosai yayi dariya yace " toh naji yanzu de koma ki d'auko min car keys d'ina a d'aki " da saurin ta tajuya zuwa d'akin Emraan don d'auko masa keys d'in shi kuma ya wuce downstairs.................

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA 💃🏻

Jeeddah ja'o🏵

EMRAAN ZAYDWhere stories live. Discover now