PART (6)

1.2K 62 1
                                    

🎻💕 EMRAAN ZAYD 💕🎻 page 6⃣
© Jeeddah ja'o🏵
www.jeeddahjao.WordPress.com

      Sun yi nisa sosai kafin ta d'ago tana kallon Emraan baki a tab'e, tabbas yaji a jikin shi kallon shi take ya kule sosai yaja tsuka " Mtsew! Pls babu abunda na tsana irin kallo a rayuwa ta don haka mind your business!"
Maimakon ta kauda kai se tayi dariya ta gyara zama tacigaba da kallon shi harda tagumi kafin tace " Sorry bro! Amma fa ba dan kallon da nake maka na baka hak'uri ba ! Kawai de na laifin d'azu da na buga maka mota nake baka hak'uri! Amma don na kalleka ba laifi na bane ,laifin ka ne da ka zamto kyakkyawa! Dan ma baka yi murmushi ba!da abin zai fi haka armashi."
   Wani mahaukacin birki ya za tsabar bak'in ciki ko motar bai rufe ba ya fice ya shige cikin gida. Tab'e baki Amrah tayi ta juya baya tana kallon Dad kafin tace " wai meye a ciki don ance mutum yana da kyau? Nidai a yadda na sani mutum murmushi zai yi yace Thank you! Amma sam shi na daban ne ," Dad yayi murmushi yace " Kar ki damu my daughter, he's just stressed out." Tab'e baki tayi tace " Wow! Amma uncle wannan gidan ya had'u! " murmushi kawai uncle yayi yana k'ok'arin shiga gida ita kuwa ta wuce hanyar garden ,kasantuwar ma'abociyar son furanni ce ita.

      Dad tafiya yake yana ta surutai har ya shiga falo , a tunanin sa tana biye da shi saida yaji shirun yayi yawa ya juya yaga wayam ! Babu ita balle kyallin ta , kai kawai ya girgiza ya k'ira Emraan dake k'ok'arin hurawa sama yace " je ka dubo ena Amrah ta shiga "
  Rai a dakile ya juyo yana murza zoben azurfan hannun sa , tabbas Dad yaga bacin rai a fuskar Emraan tun zuwan Amrah don haka ya Kira sunan shi kafin ya fita yace " Emraan ! Hannun ka baya rubewa ka yanke ka yar , idan akwai abunda take buk'ata bai wuce gyara ba , you are her brother kada ka tsane ta ,try and show her the right way!" Murmushi kawai Emraan yayi ya fice domin dubo ta shi kuwa Dad ya haura upstairs to freshen up..........

      Cikin garden ya jiyo dariyar ta don haka ya nufi wajen ,ko da ya shiga kuwa a wajen ya dank'are sanadiyyar ruwan da ta watso masa daga hose ( Tiyo) kuma ta tsaida shi a kansa kawai ruwan ke zuba gashi Ana suburbud'a sanyi ,se lokacin idanuwan ta suka sauk'a kanshi , don tayi zaton flowers take zubawa ruwan , kasa sauk'e tiyon tayi baki a sak'e tana kallon shi , yayinda yake matsowa kusa da ita a hankali , tsayin shi, kwarjinin shi, kyau,duk suka kafe ta waje d'aya bata ma san ya karb'e hose d'in ya kashe ruwan ba. Yana tafe yana matse jikin rigar shi har ya dawo inda take ba tare da ya kalle ta ba yace " Dad yana k'iran ki " a hankali tace tace " Oh! Ohk ! Tana dariya tana bin shi a baya tana irin tafiyar shi ,duk abun da take yana kallon ta jikin mirror glass na k'ofa don haka ya tsaya chak yace " Ke ni sa'an ki ne? " saida ta had'iye miyau ta girgiza kai Tace " Aww! Yi hak'uri kawai wlhy tsayin ka mamaki yake bani! " tana maganar tana k'ok'arin jerawa da shi tana d'angale k'afa tana dariya ,duk ta Hana shi wucewa ga iska yana busawa mai sanyi duk jikin shi kamar an sa kankara ,suna cikin haka driver ya iso da su Tasleem daga school ganin haka yasa ya zame hannun shi daga cikin nata tare da agogon shi da take faman cirewa ya shige ciki ita kuwa ta tsaya bakin k'ofar tana k'are musu kallo ,su Hanan ma suna isowa kallon ta suka hau yi ,ganin yadda take murmushi tana motsa bakin ta kamar mai son magana yasa Tasleem tace " Hy am Tasleem " murmushi tayi ta mik'a Mata hannu tace " Amrah is mah name ! Daga England " hanan ta zaro ido " Laaah !! Kece y'ar gidan uncle Yusuf? Dad bai fad'a mana zaki zo ba ! Wlhy kin zo at the right time ! Gobe Friday birthday na Sis Tasleem it will be great celebrating with you " sosai suka yi ta surutu Tasleem suka rik'e ta suka shiga ciki sai zuba take musu tana basu labarin London, duk hirar da suke yi agogon Emraan yana damk'e a hannun ta saida suka gama shiri har sun fito zasu sauk'a downstairs tace " Wait ! Agogon yaya a  hannu na , ena Zan kai mishi yanzu? Tasleem tayi murmushi tace " Kije ki kai mishi inyaso ki same mu downstairs kibi wancan corridor d'in zakiga flat nashi  white door komai na ciki fari ne" kai ta girgiza ta nufi inda sukayi Mata kwatance su kuma suka wuce downstairs.................

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA 💃🏻

Jeeddah ja'o🏵

EMRAAN ZAYDWhere stories live. Discover now