Chapter 7

1.3K 59 1
                                    

🎻💕 EMRAAN ZAYD 💕🎻 page 7⃣
© Jeeddah ja'o🏵
www.jeeddahjao.WordPress.com

Ganin k'ofar tayi half opened ,don haka ta tura a hankali ta shiga tare da furta " Wow! This place is totally amazing! " tana magana tana juyi , saida ta gama kalle kallen ta sannan ta nufi wata k'ofa , jin motsi a d'akin yasa ta nufi k'ofar ba tare da sallama ba ta fad'a d'akin direct bakin mirror ta nufa tana ta gwada perfumes d'in gaban madubin duk na maza ne amma tsabar rigima da rashin aiki saida ta fesa ,daidai lokacin Emraan ya fito daga wanka yana k'ok'arin kunce towel ita kuma ta juyo, 😳

CHAI!!! Wani irin daskare wa yayi a wajen itama hakan tayi bayan ta sake kwalbar turaren shi a 'kasa , tsabar ta rikice ta kan kwalbar tabi ta taka da gudu ta fice a d'akin , Emraan bai san lokacin da ya bi bayan ta ba ,bayan ya maida towel d'in ,bata ankara ba ta ji an chafke hannun ta ,yayi baya da ita har ta kusa fad'uwa da 'kyar ta iya tsayawa ,tana d'agowa bata ji komai ba se sauk'ar Mari har biyu on both sides of her face. Tsabar gigice wa bata san lokacin da ta kurma ihu ba.
Hankad'a ta yayi ta zube kan kujera yana nuna ta da yatsa " wai ke wacce irin yarinya ce? Ko dabba bazai yi abunda kika aikata ba? Kada ki kuskura ki bar yahudancin ki yayi tasiri a wannan gidan? Banda rashin tarbiyya yaya za'a yi ki shigo waje babu sallama ? Kuma uban me ma ya kawoki d'aki na?ko kinga nayi Kama da sa'an ki ne? Barin yi warning d'in ki !!! Kada ki kuskura na 'kara ganin ki a nan wajen ,cuz bana had'a hanya da mara daa and mind you idan kika sake kika 'kara irin wannan shashanci saina karairaya ki !!" Tashi ki fita min a falo tun kafin in tattaka ki!!!" Duk da jinin dake zuba sanadiyyar glass d'in da ta taka bata san lokacin da ta d'eba da gudu ba tayi waje...

Daidai lokacin da ta fita Affan yake k'ok'arin bud'e d'akin sa, tabbas su Tasleem sun sanar da shi zuwan ta , amma kuma yanayin da ya ganta a ciki ya tsorata shi sosai don haka ya tare ta yace " Me kuma ya same ki? " ba tare da ta amsa shi ba ta Fara k'ok'arin wucewa , Affan ya damu sosai don haka ya Fisgo hannun ta cikin falon shi ya zaunar da ita kan kujera , a hankali ya d'aga k'afan nata saman center table sannan ya je d'aki ya d'auko first aid kit ya yi treating Mata ciwon taci sa'a babu glass da ya shiga ciki , bayan ya kammala ya bata pain reliever sannan ya zauna yana tambayar ta me ya faru?" Hawayen ta tafara gogewa tace " Yaya baya sona , ba da sani na bane bafa na shiga d'akin shi kawai Zan kai mishi agogo shine kuma ya fito daga wanka . kuma......kuma ni ban ga komai ba se ......" Dariya ce taso kufcewa Affan gudun kar ranta ya sake b'aci yayi sauri ya gimtse sannan yace " Kinga Amrah ! Nan fa ba turai bane , kinga a nan in zaki cigaba da fad'awa d'aki babu sallama toh lallai zakiga abun da yafi haka , yanzu kar ki damu am here! We will be friends komai zai dawo daidai , kuma kar ki sake cewa yaya baya son ki don babu wanda yaya baya so , I'll give you some leaked out akan halayen shi" murmushi tayi tace toh indai haka ne we really are friends Kaje ka d'auko min waya na a d'akin shi don ya Hana ni shiga wlhy wai karairaya ni zai yi " Affan ya d'ago idanuwan shi ya kalle ta yace " Alright Zan d'auko miki but promise me idan aka tambaye ki inda kika ji rauni bazaki ce yaya ne yayi sanadin shi ba ko?" Kai kawai ta girgiza tana goge hawayen ta sai a lokacin ya Lura da yanda tafin hannun Emraan ya kwanta a fuskar ta, sosai ya tausaya Mata , ajiyar numfashi yayi kafin yace " Tashi muje lunch is ready " a tak'aice tace " A'a ni Kaje barin ci abinci ba bana jin yunwa"
Mik'ewa Affan yayi ya kama kunkumi yace " gud! In har bakici abinci ba toh say gud bye to your phone " a take ta mik'e tace " toh muje!" Dariya Affan yayi yace " yawwa! Kanwata ! Kin san wani abu kuwa gaskiya kun dace da yaya Emraan fa! " ya fad'a yana kanne Mata ido d'aya ita kuwa ta wurga masa throw pillow rai a b'ace tace " wa zai auri wancan masifaffen?" Hannun ta Affan ya Kama suka fita se masifa take wai me zai sa ta auri masifaffe"

A tsanake ya iso dining room yaja kujera ya zauna fuska babu yabo ba fallasa ya yi serving kanshi ba tare da yace komai ba ,har ya debi abinci zai kai baki ya d'ago ido kawai se a cikin na Amrah da suka yi ja daga gani tayi kuka sosai , a take yaji abincin ya fita ransa ya mik'e ya bar dining room d'in ya kalli y'ar Aikin su Talatuwa yace " Ki je ki gyara min d'aki na , kuma in kin kammala ki kawo min green tea ina garden " a rusune ta amsa da " toh" ya juya ya fice Affan da su Dad suka bi shi da kallo har ya fice Hanan ta ce

" wai me ya samu yaya ne yau? He seems disturbed" murmushi Dad yayi ya kawar da tambayar da cewa " Hanan je ki d'auko min waya na a d'aki " murmushi tayi sannan ta mik'e ta wuce ciki................

Dedicated to FEEDOH Y'AR FICIKA 💃🏻

Jeeddah ja'o🏵

EMRAAN ZAYDWhere stories live. Discover now