“Baki ji ciwo ba dai ko?”

Na dubeshi ina mamakin haka ko wane uba yake ko kuma dai nawa ne a haka? Na daga mishi kai sannan na mike tsaye shi ya rika ni ya saka ni a dakinmu sannan ya kalli Hama dake zaune ido a kumbure ya ce.

“Ke yau baki zuwa makaranta ne?”

“Ina zuwa”

Ta amsa sannan ya fice ita kuma ta tashi ta fara shirin tafiya makaranta a lokacin da na san kamin ta isa ta yi latti sosai. A tare suka fice da Yaya aka bar ni kadai a gidan sai damuwata da kunci.
Baba ne ya sake dawowa dakin ya same ni a kwance.

“Noor Allah yasa ba wata maganar kika fadawa Alhajin nan ba, na ga yayi saurin tafiya kuma kin dawo cikin gida”

Na daga kai na kalleshi.

“Ba mu yi magana ba Baba, yace zai dawo anjima ne”

“Tom tom tom shikenan”

Ya juya ya fita daga dakin be fita gidan ba sai bayan sallah azahar, a haukace na dauki Koko da Hana ta siyo na sha saboda wani yunkuri na amai da nake saboda yunwa har ina jin numfashina kamar zai dauke. Daker na iya tattalawa na fita na yi alwala na dawo na yi sallar a zaune saboda ciwon da cikina yake yi. A gurin na zube ban sake motsawa ba sai da aka yi sallah la'asar, ita ma dai haka na yi ta cikin karfin hali, ina jin kadaici da kewa domin ni kadai ce gidan, ba mamaki Hana ta wuce gurin Mama domin ya isa ace ta dawo daga makaranta tun karfe 2pm, Yaya ma be dawo ba balle kuma Baba da be fita ba sai azahar.

Yammancin La'asar na ji an buga kofar gidan har sau biyu, ban fita ba ban kuma tambaye waye ba domin babu kuzari ko muryar aikata hakan a gareni yanzu. Har sai da yaron makota ya shigo ya ce wai ana sallama da Noor inji Kareem da abokinsa, shi ma dai ban amsa masa ba amman na tashi sanye da Hijabin dake jikina ina dukuduku na fita dakin na saka talkamina na isa zaune gidan, sai na tsaya daga cikin zauren har sai da na dan huta sannan na rike gambun karfen na leka waje. Kareem da ya bawa kofar gidanmu baya ya juyo ya kalleni. Abokinsa kuma dake zaune a motar da gambunta yake bude ya fito daga motar,  sai na ja baya na koma cikin zaune na duka kana kallona ka san a wahale na ke.

“Noor...”

Cewar Kareem da ya fara shigowa zaure yana kallona, shi ma sai na duka daidai tsayina damuwar da tabbatar ta munafurci ce tana shimfide a fuskarsa.

“Noor...”

Ya sake kirana, muna hada ido sai na ji wani kuka mai karfi ya zo min a take na fasa kuka har ina sarkewa.

“Subhanallahi me ya faru Noor? Kin rame kuma kuka kike yi akwai wata matsala ne?”

Ni dai ban san ya aka yi mutumen da nake fushi da shi ya samu sa'ata ba har na bude baki ina fada masa damuwata.

“Baba ya saki Mama jiya, Hana tun da ta tafi makaranta bata dawo ba, Yaya be dawo ba, ni kadai aka bari a gidan, bana ina cin abinci jikina babu karfi kuma ina ganin jiri, Baba kuma yace ba zai aura min Zafeer ba, kuma Zafeer na san ba zai yafe min ba...”

Haka na jera masa komai tsab ina kuka sai ya matso kamar zai taba ni kuma ba taba din ba, sai ajiyar zuciya da ya sauke ya daga kai ya kalli abokinsa dake tsaye kamin ya sake dubana. 

“Saboda ke ne Baba ya samu matsala da Mama? Yanzu ina Mama take?”

Na watsa masa wani mugun kallo ina jin kamar na shake wuyansa.

“Ban san a ina Mama ta tafi ba, kila gidansu gurin Yayarta saboda saki uku Baba yayi mata, amman duk saboda kai ne komai ya faru, kai ka lalata komai Kareem, kai ne kasa Baba ya juya ma Zafeer baya, kuma saboda kai aka saki Mama jiya, kuma ka saka aka kama Zafeer...”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now