“Ga kununki in ji Mama...”

Na kalli kunun na dauke kai ina jin ba zan iya kai komai a cikina ba yanzu. Ni dai ba wani sanin damuwa na yi ba amman ina jin dakinta na daf da ni domin kokarin rabani da Zafeer da Baba yake ko ma yayi wani abu da ban taba mafarkin faruwarsa ba.

“Wa'alaikusalam”

Muka ji Mama ta amsa sallamar Zainab dake sanye da uniform din makaranta, Hana ta jiya ta fice daga dakin kamar dai babu wadda ya damu da halin da nake ciki, wata kila ba su yi zaton soyayya ta ta kai haka ba, ko kuma ganin suke wani abu ne da zan iya mantawa a take. Ko kuma dai saboda ni na janyowa kaina ne shiyasa lamarin ya zo min ta haka.

“Noor... Lafiya kike kuwa?”

Kamar an bude min kofar sassauci tana tambayar haka sai na fashe da kuka na kwanta jikinta amman na kasa fada mata damuwata har ta gaji da tambayata ta koma rarrashina.

“Allah dai yasa lafiya, Zafeer ya je gidanmu shi ma cikin damuwa yace na fada miki ya zo jiya amman be samu ganinki wai yana son ku hadu a gurin aikinsa ko kuma kwanar dan musa mai itace anjima da karfe goma”

A sirrance take fada min sakon na Zafeer, abun da hausawa ke cewa ga bikin zuwa babu zanen daurawa, domin ban isa na tsallake umarni da furucin mahaifina na je na ganshi ba, kuma a yau bana jin zan iya budewa kawata cikina balle na fada mata damuwata da babu mai min maganinta sai Allah.

“Noor akwai wata matsala ne? Fada min ko minene dan Allah”

Na girgiza mata kai na matsa baya na kwanta ina maida numfashi daker.

“Wai fada kuka yi da shi ne ko kuma me?”

Nan ma dai ban ce mata komai ba. Har ta gaji ta tashi ta fita ta barni rumgume da bakincikina. Ban iya fitowa na yi komai ba har Mama ta gama aikinta na gida, Yaya ya dauko ruwa sannan yayi wanka ya fita, a nan na samu mikewa tsaye ina jin kaina na masifar ciwo ga wani jiri jiri da nake ji yana dibata yana yawo da ni. Ruwa na zuba na shiga bandaki wai saboda na samu na yi wanka amman sai na saka yin wanka na zauna a bandakin ina ta kuka. Hankali be kara tashi ba sai da wani almajiri ya shigo ya ce Zafeer na sallama da Noor Mama tace masa yaje yace bana gidan. Rumgume kaina na yi ina ta kukana babu mai rarrashina har sai da na gaji na tashi na daura zanena na fito ba tare da na yi wanka ba na aje ruwan a waje sannan na nufi dakin Mama na zauna daga bakin kofar dakin ina kuka na ce.

“Mama Wallahi duk na daina abun da nake, ba zan sake kin jin maganar kowa ba, Mama ki yafe min kuskurena, kuma dan Allah ki roka min Baba yace ya yafe min yayi hakuri ya bar ni na auri Zafeer dan Allah Mama”

Kaya take ninka amman haka be hana ta kalleni ba ta ce.

“Kin fi kowa sanin halin Babanki ai, yanzu ya ga mai kudi ba zai yarda da soyayyarki da yaron nan ba, kuma ni ban ga laifin ubanki ba, daman tsuntsu da ya ja ruwa ai shi ruwa kan doka, tun abun nan be yi nisa ba ya kamata ki gane gadar zare kike yi ma kanki amman ina, hankali yayi yamma ke kin yi gabas, idan kika ga Babanki be hada aurenki da wannan mutumen ba to sai idan shi din ne yace baya sonki ko kuma wani ya gani wadda ya fishi”

“Ba so na yake ba Mama Wallahi wata kalmar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi ba”

Na fada da muryar kuka wani kukan na cin karfina.

“Wannan kuma ke kika jiyo, ga dubu biyu nan tashi ki kai gidan mai adashe, bashin da kika ci ne ban gama biya ba”

Ta jego min kudin ni kuma sai na kai hannu na dauka, na kalleta sannan na tashi na fice daga dakin ina hawaye. Dakinmu na koma na zauna gaba daya sai na rasa abun da ke mini dadi. Na kusan minti talatin a dakin ina kuka har sai da Mama ta yi magana sannan na yunkura na tashi idona a kumbure na saka rigata da hijab na riko kudin na fito na saka talkamina na fice daga gidan. Kamar wata marar lafiya haka nake tafiya har na isa gidan mai adashen na bata kudin na juyo na fito ta babu wani kuzari a tare da ni. Daf da zan isa gida na ji muryar Zafeer yana kiran sunana amman na kasa waigawa saboda bana son na yi arba da fuskarsa kar rauni ya saka ni karya doka da mahaifina ya saka min, amman hakan be hana shi shan gabana ba.

TA ƘI ZAMAN AURE...Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum