“Ni ma bana fatan shiga alfarma, bana fatan kasancewa a karkashin inuwar alfarmarki, ina jin fiye da abun da kike ji game da auren nan”

Ta tintsire da dariya.

“Na nawa kuma? Ai na gama yi maka alfarma Kareem tun da har ka kasa rike kanka ka keta rigar mutuncina, kuma ka yi nasara har na haifa maka yaya biyu, ka gama cin alfarmata, sai kuma me?”

Ta daga masa gira tana jiran amsarsa. Baya jin zai biye mata su fara abun da suka dauki lokaci ba su yi ba, ta saba fada masa magana marar dadi amman a haka yake hadewa ya danne saboda yana jin shi namiji ne ya fita hankali da tunani, and wani lokacin yana jin kamar ta ci albarka cin yaransa. Yayi murmushi ya sake kallonta ya dauke kai ya juya ba tare da yace komai ba ya nufi stairs.

“Ga breakfast dinka nan”

“Ba a gida zan ci abincin safe ba”

Ta tabe baki ta ja kujera ta zauna tana magana a hankali da muryar da ba zai ji ba.

“Ni dai kawai ina ibada, kuma ina jiran ranar takaba”

Kareem ya shiga dakinsa ya cire tufafin jikinsa ya shiga bandaki ya fara murza jikinsa har yayi wankan ya gama maganar da Yusura ta jefeshi da ita cewar ta gama yi masa alfarma tun da har ya kasa rike kansa har sai da ya kai ga jikinta tana cin ransa. The part that ita bata san duk kokarin kai kansa da yake gurinta yana yi saboda ya bata hakkinta ba is more painful sama da aurenta. Yana fitowa ya shirya cikin farar shadda ya saka hula ya fesa turare ya dauki abubuwan bukatarsa ya saka talkaminsa ya fice daga gidan. Ko da ya sauko tana zaune a dinning din tana cin abinci. Be kulata ba ya fice daga falon motarsa ya shiga ya murza key mai gadin ya bude masa yana mika masa gaisuwar barka da safiya. Hannu kawai Kareem ya daga masa sannan ya kama hanyar da zata kai shi gidan abokinsa. Yana kan hanya kiran Safeena ya shigo wayarsa, duba wayar kawai yayi ya aje be sake daukarta ba sai da ya isa gidan Hafiz sannan ya kira ya sanar masa yana waje.

“Shigo ciki mana”

Kareem ya bude motar ya fito ya rike da wayarsa da Safeena ke kara kira. Iskar bakinsa ya busar sannan ya amsa wayar.

“Hello”

“Baka kira ka ce ya jikina ba? Baka yi tunanin ko bana jindadi ba? Miscarriage na yi ba jiya, yanzu baka ma damu da lafiyata ba Kareem?”

“Safeena ina son za mu yi magana da ke face to face amman bana son mu yi magana yanzu sai idan mijinki baya gari”

“Na ji muryarka wani iri, matarka ce ta bata maka rai?”

“Me zai saka matata ta bata min rai?”

“Ban sani ba, amman dai na san nice mai faranta maka a kodayaushe ba tare da gajiyawa ba”

“Ya jikinki.?”

Ya tambaya domin ko da yace be damu da Safeena ba ko lafiyatarta ko kuma yace baya sonta yayi karya.

“Da sauki, ina asibiti yanzu haka”

“Idan kin dawo zamu yi magana”

“Okay i love you”

Ba tare da ya amsa mata da i love you too ba ya kashe kiran ya saka wayar aljihu sannan ya doshi kofar shiga yayi knocking. Hafiz ya bude masa kofar.

“Shigo mana”

Ya shiga falon kamar marar lafiya.

“Bismillah ga breakfast na san baka karya ba”

Hafiz ya fada yana nuna masa dinning, Kareem ya karasa daman gidan ba bakonsa ba ne. Ya zauna a kujera Hafiz ma yaja kujera ya zauna.

“Yanzu nan ni ma na dawo gida, na sauke madan a gurin aiki”

Kareem ya sauke ajiyar zuciyar dakw bayyana damuwarsa sannan ya ce.

TA ƘI ZAMAN AURE...حيث تعيش القصص. اكتشف الآن