“Wai Zafeer yana sallama da Noor”

“Ka ce gata nan zuwa”

Yaron ya juya ya fita, shiru ban ji Mama tace na tashi na tafi ba, na san kuma Zafeer ba tafiya zai yi ba sai ya gan ni, ko kuma idan an fada masa ba zan samu fitowa ba. Dan haka na mike tsaye na fice daga dakin na isa bakin kofar dakin Mama na tsaya daga bakin kofa na fara da bata hakuri.

“Mama ki yi hakuri, ba zan sake ba”

Ta yi kamar bata ji ba.

“Na tafi gurin kiran da Zafeer yake min?”

Na tambaya a kokarin na zama yarinyar kirki.

“Idan kika tashin fitsararki umarnina kike nema? Yar iskar yarinya marar mutunci”

Daga jin wannan kalama na san Mama bata gama sauka daga fushin nan ba. Sululu na fice daga gidan kamar macijiya, ina fita waje na samu Zafeer tsaye yana danna wayarsa, kamin na karasa gurin da yake tsaye na fashe masa da kuka a take ya dago kai da sauri ya kalleni hankalinsa a tashe.

“Me ya faru Baby Noor waya taba ki?”

Ya kunna fitilar wayarsa ya haska fuskata.

“Subhanallahi me ya same ki waya fasa miki kai? Me kika yi Noor who did this to you? Who touch my Babeee”

Tambayata yake hankalinsa a tashe zuciyarsa na cika, ban yi mamaki ba domin ya saba fusata a duk lokacin da aka taba ni.

“Waya miki wannan duka Noor fada min mana...”

Cikin kuka na fada masa abun da ya faru tun daga irin karyar da Kareem yayi ma su Mama cewar mota ce ta buge ni, har zuwa dukan da Mama ta yi min.

“Kuma sun cinye duka naman ba su ba ni komai ba, ko yar tsutsar nan da na so na ci ba su ba ni sun zubar”

Juya baya yayi yanayin fuskarsa ya sauya kamar zai fashe da kuka, ya jingina da ginin gidanmu ya kife kansa. Kamin ya dago ya kalleni.

“Iyeyenki kadai suka kai su yi miki haka Noor, su kadai ne suka da ikon dukanki su fitar miki da jini haka kuma na kyale su, Allah ya daran talauci Noor, ba dan shi ba da yanzu na aureki da yanzu karkashina kike rayuwa, wani abu duk ba zai faru ba”

“Sun cinye komai har tsutsar nan irin wadda masu kudi suke ci, na so na ci na ji me ake ji”

“Ana zancen rauninki kina zancen tsutsa, idan kin ci me zaki ji?”

“Na ji abun da suke ci mana, har kai na dauko maka naka fa, ai kasan komai na samu sai na kawo maka”

Na fada cikin kuka.

“Ni dai dan Allah ki daina daukar komai kike gani ki saka a bakin nan Noor, wani abun da kike ganin masu kudi suna ci, masu kudin nan ba dukansu ne suka da hankali ba, komai kika samu ki ta kaiwa bakin nan na ki kuma idan mun yi aure....”

Na share hawayena na kalleshi.

“Me? Kawai ba ina son na ji yadda ake ji ba ne, yanzu ai ba zan sake samu ba”

“Yanzu dai shiga cikin gida ki fadawa Mama zan kaiki a duba raunin nan”

Na juya sai ya kira ni na dawo. Ya haska fuskata ya saka rigarsa ya goge min hawayen da kyau.

“Kar ki shiga kuma tace kin min kuka ta miki fada”

Na dauke kai na koma cikin gidan na tsaya daga jikin kofar dakinta na sanar mata.

“A dawo lafiya”

Ita ce amsar da ta ba ni, sai na juyo ya dawo na fada masa muka kama hanyar titi ni da shi. Muna tafiya yana kallona har muka isa na zauna a kujera mai shagon ya bude ciwon ya sake wanke min ya sake rufewa ina kuka saboda zafi, Zafeer kuma yana rarrashina kamar wata jaririya.

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now