“Me ke faruwa a nan?”

Yarinyar ta juyo ta kalleshi da sauri sai ta kara rushewa da kuka.

“Wai daga na shigo ina nemanka sai ta buga min cup din ruwa akai kalla har yayi jini”

Ta nuna masa jinin hannunsa. Sai ya juya ya kalli Yusura.

“Why?”

“Rashin kunya ta yi min”

Ta ba shi amsa babu alamar wasa a fuskarka. Yarinyar ta girgiza kai da sauri.

“Wallahi karya take komai ban ce mata ba, kawai na shigo nace dan Allah ina mai gidan nan, mijinta shi ne kawai ta buga min cup a kai”

Kareem ya juya ya kalli Yusura dake tsaye rike da cup din.

“Kishi kike?”

“Kishi?”

Ta maimaita tana ja baya tare da yin dariyar rainin wayo.

“Kishi dai kishi? Na rasa waye zan yi kishi sai kai? Allah ya tsare gatarina da saran shuka mtscheeeeeeee”

Taja dogon tsaki ta juya ya bar musu gurin. Kareem ya kalli yarinyar da jini ke fita a goshinta yace

“Me yasa kika dawo?”

“Yaya ya tafi abun shi, wai ba zai koma restaurant din ba, kuma zai buga waya ya fada musu karya nake kar a bani, yana ta min fada a hanya, kuma yace ba zan bishi gida ba sai dai kowa yayi tafiyarsa, shi ne ya saka a Napep yace ya kai ni gida, ni kuma sai da muka yi nisa sai na cewa mai napep din ya dawo da ni nan gidan amman ya biyo wata hanya da Yaya ba zai gani ba, kuma yana waje ban bashi kudi ba”

“All this long story ban gane me kike nufi ba”

“Ina nufin Yaya so yake na tafi gida ba tare da na karba kyautar da ka ba ni ba, kuma yace ba zai tafi da ni can din ba”

Ya rike kunkurunsa yana murmushin da ya kusa zame masa dariya.

“Ammm ya ma sunanki?”

“Noor sau uku kenan ina fada maka”

“Yanzu ba zan sake mantawa ba, I'm sorry yanzu muje a duba kanki...”

Ta juya tana rike da goshin ta fita daga falon, sai ya bi bayanta har sun saka entrance din sun isa gurin motarsa ya tuna keys dinsa basa aljihunsa.

“Noor jira ni a nan zan dauko keys dina”

“Toh amman ka yi sauri kar ta fito”

Yayi murmushi.

“Ba zata sake fitowa ba”

Ya juya ya koma cikin falon, kai tsaye sama ya nufa ya shiga dakinsa ya dauko keys din, ya nufo curtains dinsa dake dage zai sauke kasa sai ya hango Noor tsaye a inda ya barta sai daga hannu take bakinta na motsi da alama masifa take, hakan ya saka shi saurin saukowa domin yayi tunanin ko Yusura ce tsaye jikin kofar falon, saboda ya hango kofar take kallo. Ga mamakin sai ga ita kadai ce take fadan tana kallon kofar falon. Sai da yaja kofar sannan ya nufi Motar ya bude sai da ya fara shiga sannan Noor ta shiga, yayi reverse ya fice gidan, tuki yake a hankali yana kallon yadda Noor ta natsu sam ba zaka ce tana da yawan magana ko kiriniya ba, babu wannan alamar a fuskarta da jikinta natsassiya ce sosai idan bata bude baki ba.

NOOR POV.

Shiga motar alfarma irin wadda ban taba shiga ba, ga wani sanyi ac mai dadi da laushi yana ratsa fatata ya saka natsu sosai ina jin yadda duniyar masu arziki take da dadi, sam na manta da ciwon da mahaukaciyar matar ogan su Yaya ta ji min a goshi har sai da muka isa wata babbar Asibiti, ni da nake zaton chemist zai kai ni domin ciwon ba wani babba ne ba. Fakawa yayi a gaban kofar emergency baya tsoron ma su masa fada.

TA ƘI ZAMAN AURE...Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz