“Rabi zan kawo miki”

Be jira abun da zan ce ba ya juya ya bar ni a gurin zaune. Babu jimawa ya dawo rike da plate wata yar shimkafa ce kamar na roka sai wani kofin lemu da gorar ruwa mai yawa.

“Yaya wannan ba zai ce min komai ba, iya halshe zai tsaya”

“Masu kudi kadan suke ci ki yi cin masu kudi, ko baki ga yadda Restaurant din yake ba?”

Ya zare min ido sannan ya tafi ya bar ni a gurin. Ba dan kar nutane su kalle ni da ba zan ci wannan abinci ba, wannan ai rowa Yaya yake min a gurin aikinsa. Na daure na kai zuciyata nesa na cinye abincin nan tass ko shimkafa daya ban bari a gurin ba, lemun ma duka na shanye sannan na dauki ruwan na sha. Kamin na mike tsaye sai ga Yaya ya zo yana kokarin dauke kayan har da ruwan aiko na saka hannu na dauke ruwana, gudun siyar da hali yasa be ce min komai ba ya shiga ciki da kayan, babu jimawa ya fito sanye da kayansa na gida ya rika hannuna muka kama hanyar fita.

“Mi zaki yi da gorar ruwa wane irin kauyanci ne wannan Noor dan Allah ki aje”

“Wallahi ba zan jefar ba, ai ba kyau wulakanta ruwa, kuma ai siya muka yi ba sata ba”

Ina jinsa yana jan tsaki amman ban jefar da ruwana ba, ko ba komai kowa ya gani zai san na ci abinci a gurin, masu kudi ma haka nake ganin suna yi ai, suna rike gorar ruwa a hannu idan suna yawa. Sai da muka fita gate din gurin gaba daya sannan yake tambaya me ya kawo ni ma.

“Yaya kudina zaka ba ni, bikin salwa zan je, dari bakwai daka ara zaka ba ni abuna”

Ya daka min tsawa.

“Ba salwa ba kwai, yanxu saboda bikin wata Salwa kika kwaso kafa kika zo har gurin da nake aiki har da aron na Napep, kuma sau nawa zan biyaki bashinki ne Noor shekarab jiya kin karbi dari biyu last week na baki dari uku dari biyu kawai kika biyo ni, kuma yanzu kin hau Napep da ita, gashi nan kin saka ni siyen plate daya 5k sakaryar yarinya kawai”

Ban san lokacin da na tsayar da tafiyar da nake na dube shi.

“Yaya wannan abincin da naman kahirar ne 5k? Kam bala'i Wallahi a ana zalimci duniya, kuma ni kudina 700 ne”

“Da yardar Allah ba zan sake rantar kudinki ba, ke idan an ari kudinki babu zaman lafiya, kuma sai ki rika kari saboda baki tsoron Allah”

Yana masifar yana tare mai adaidaita, yadda fuskarsa ta hade sai ka rantse da Allah ba shi ne yake tarairayata a cikin restaurant din ba.

“Kuma wannan abincin da kika ci bashi ne sai kin biya. Malam Wurno Road”

Ya karasa yana magana da mai adaidaita sahun.

“Yaya ba gida zamu je ba?”

“Ban sani ba, kuma Allah yasa mu je kin zubar min da mutunci mu koma gida ki ga yadda zan miki wulakanci”

“Toh wai ni nace ka kawo min abinci? Ba kai ka ba ni ba dan kanka to miye na masifa kuma”

“Saboda dari bakwai kika zo har gurin aikina, kuma idan ban kawo miki wani abu abokan aikina ai za su min gulma, kuma kin ba ni tausayi da farko”

Ban yarda na sake cewa komai ba, domin abu ne mai sauke ya sauke ni a hanyar ya tafi ya bar ni, na lura ba karamin hawa yayi wannan masifar da yake ta min kamar na ce ya ba ni abinci a dole. Tun da muka shigo unguwar mai adaidaita be tsaya ko'ina ba har sai da Yaya ya bukaci haka. Gaban wani katon gida ya faka Yaya ya fito ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ya bawa mai adaidainta.

“Zai wuce da ke gida”

Ina jin haka na yi saurin fita cikin Napep din na fara yi masa magiya ina kuka. Har ga Allah ba zan yarda ya shiga wannan katon gidan ba tare da ni ba, ko ba komai ai zan bawa idanuwana abinci.

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now