“Abbah ina wuni”

Na gaishe shi, sai yayi saurin dauke kai kamar be gan ni ya hade rai.

“Abbah gidan dawo (Fura) za a siyo maka kawo na karbo maka”

Na fada cikin ladabi sai dai hikimar ba dan na siyo masa ba ne kawai sai dan na dalilinsa na zuwa gurin.

“Me kike yi a nan?”

Ya daka min tsawa dai da na zabura zuciyata ta buga kamar zata fado.

“Mama ce ta aike ni na siyo mata fura”

Na fada ina kokarin kare kaina, rufe bakina ke da wuya sai ga Bilki ta fito daya daga cikin yan matan da suke gidan ta chaba ado kamar wanda zata je gurin biki. Ganina tsaye ina kallonta ya saka ta juya da sauri ta koma cikin gidan ba tare da ta fito ba.

“Zaki wuce ko sai na ci ubanki?”

Kalamin da Abbah yayi ya dawo da dubana gurinsa sai na matsa baya da sauri na kama hanyar gida ina tafe ina waigensa shi kuma be fasa cika yana min dakuwa ba (Zagin hannu kun san hausar mu da ta ku ba daya ba😁) har sai da na karya kwana a nan na boya cikin wani kwararo ina lekonsa, wayarsa na ga ya ciro yana dannawa sai dai kamin ya kai wayar a kunne wani kamin yaro ya fito yayi magana da shi, sai na ga Abbah ya mika masa ledar hannunsa sannan ya juya ta hanyar da na biyo ya wuce.

‘Wato Balki da Abbah na take soyayya kenan hmmm’

Na fada a raina a zahiri kuma sai na juya na nufi hanyar gida, kamin na isa zuciyata ta cika har ta kusa fashewa tsabar takaici da baki ciki. Ban tsaya sallama ba haka na shiga gidan na zauna kusa da Mama dake tuka tuwon masara na jera mata abun da ya faru sai hakki nake saboda bacin rai.

“Wata kila dai fura zai siya”

Yaya Nabil ya fada kamar wanda be yarda da maganar ta ba.

“Wallahi ba wata fura, ai ba leda aka kawo masa ba shi ya bada ledar aka shiga da ita gidan, kuma har ce masa na yi ya kawo kudi na karbo masa sai ma zagina da yayi”

Ina maganar ina yamutsa fuska.

“Wallahi sai na mata mugun duka”

Mama ta nuna ni da muciyar da take tuka tuwo da alamar dake nuna babu wasa maganarta.

“Wallahi ko yatsa na ji ance kin nunawa Balki sai na ci ubanki sai na miki dukan da zai daukeki lokaci kina jinya, kuma kin san halin Abbanku ko? Bara saboda Amaryarss ya karya miki hannu, idan baki cire idonki akan Balki ba sai zai iya kashe ki ma”

“Amman abun da yake be dace ba, irin wannan ke janyo raini s unguwa, kuma ko aure zai yi me zai yi da Balki Fisabilillahi”

Cewar Yaya Nabil cikin da bakinciki. Mama tace

“To ya zaku yi Mahaifinku ne sai Hakuri, idan ya tashi aikata abu kun san babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa, saboda haka bana son na ji bakin kowa a cikinku, musamman ma ke Noor ke ce marar jin magana, duk dukan da za'a miki ba ki ji”

Na turo baki gaba, domin Allah kadai ya san irin rashin mutum da zan yi ma Balki idan ta yarda da auri ubanmu.

“Har da leda baka ya bata”

Na sake fada ina tuna dukan da yayi ma Mama dazun saboda tace ya bada garin masara babu kudin cefane.

“Daman ke kin iya karawa miya gishi ai, idan baki fadi komai ba to ba ke ba ce”

Na juya ba kalli Hana na watsa mata harara. Yaya Nabil ya shafa kansa damuws na bayyana a fuskarsa.

“Wani lokacin sai na ji kamar na tafi na bar garin nan Wallahi, abubuwan da Abbah yake sun yi yawa, muna neman abun da za mu ci amman shi ta aure yake, yaushe ya auro Baaba Maryam yanzu kuma ace har ya fara tunanin auro wata, watan ma karamar yarinya sa'ar yarsa”

TA ƘI ZAMAN AURE...Where stories live. Discover now