Page 46

254 11 0
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

FOLLOW ME ON Wattpad @Gureenjoh6763

AND ON AREWA BOOKS @gureenjo

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 46*

*FREE BOOK*

*Aunty Safeeya kin ɗaure ni da jijiyoyin jikina, babu yadda na iya na bazama wattpad🤧🤧🤧In shaa Allah final page ze sauƙa gobe*

Duk me ɗaukan duniya matabbata tabbas ya ɓata ɓat ba tare da sanin mecece duniyar karan kanta ba, Hausawa kan ce duniya budurwar wawa, kwarai duk wadda ya bi ruɗin duniya ya ɓata lahirarsa yana cikin tsaka mai wuya domin tabbas duniya ƙaryace, rayuwarta taƙaitacciya ce lahira kuwa ita ce daahir, a kusan lokaci ɗaya Baba Buba da Yusuf sun tafi gidan gaskiya.

Sun tafi ne ta hanya mabanbanta inda tsananin tausayin da jama'a suka nunawa Yusuf da labarin shi yasa dayawa suka mishi Adu'ar samun rabauta ciki har da Hidayat, ta roki Allah ya yafe mishi ita kam ta yafe, ta roki ubangiji ya sanyaya makwancinshi albarkacin tuba na gaskiya da yayi.

Yayinda Buba ya tafi cikin mawuyacin halin ƙishi da yunwa, ya tafi yana me kukan abubuwan da ya aikata ba tare da ya san makomanshi ba, dukkanin su an kaisu Gidajen su na gaskiya inda Zaka girbi abunda ka shuka. Allah ya sa mu fi karfin zuƙatanmu.

BAYAN WATA GUDA

Kwance yake hannunsa cikin nata, kanshi na a kan kirjinta hannunta ɗaya na cikin gashinsa da ya taru yayi baƙi siɗik yayi kyau, a tausashe tace

"Paapi!"

"Uhmm my love menene?"

"Yaushe ne zamu koma? Kaga an buɗe school ba nawa kaɗai ba har da yara ko mun dawo kenan?"

Dariya yayi ya ɗago yana shafa lips ɗinta yace
"Ina jin daaɗin zaman mu anan saboda ke kaɗai nake gani 24/7, bani da matsalar komai bani da Tunanin kowa da komai, ni yanzu maraya ne ina bukatar kulawarki amma in mun koma zaki manta dani ki ke shareni shiyasa bana so mu koma"

Murmushi sossai tayi tace
"Allah ya kula da maraicinka mijina, nayi maka alkawarin kulawa ta har abada, ko da yara, karatu da kuma aiki, dukda kasancewata me uwa da uba ka zamar mini mijin marainiya to me yasa zan kasa kulawa da kai?"

Peck yayi mata a lip yace
"in shaa Allah next week zamu koma I wanted to tell you tun jiya ma just carried away da maganan zuwa gembu ɗin nan"

Tace
"yeah hakane, but please muna kan magananmu ko?"

"Ba na ƙi shawararki bane, but bana son ɗibo yaran nan in kawo su su hana Daadida kwanciyar hankali, you know at her age tana bukatar natsuwa"

Shagwaɓe fuska tayi tace
"su huɗu ne fa kwata kwata suke gida, Maami ta ce a bata ɗaya, sannan su Baaba Laure zasu koma da ɗaya, biyun su zauna wurin Daadida I am very sure na wurin Baaba Laure da Maami baza'a samu matsala ba, su kuma na wurin Daadidan suna shakkarta don bata yi musu wasa, sannan ga ka nan akwai kuma security ba ta yadda zasu fita bare su yi wani abu marar kyau, su kuma na Gidajen mazajensu da suke fama se ka basu jari... Please kannenka ne Kaine matsayin uba yanzu a garesu karka duba halayen iyayensu mata, baka san ta inda Allah ze rama maka alkhairin ka garesu ba"

Ajiyar zuciya ya sauke kan ya miƙe zaune yana janyo ta itama ta zauna tana gyara towel ɗin jikinta
"since you insisted babu yadda za'a yi madame"

Rungume shi tayi tana murmushi, Daadida Tayi maganan ya ƙi shine ta Haɗata da shi, dira yayi daga kan gadon ya saɓeta suka yi toilet, ta sakale hannayenta a kafaɗansa suna hiransu.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now