Page 10

254 22 1
                                    

KOWA YA GA ZABUWA...
(DA ZANEN TA YA GANTA)

بسم لله الرحمن الرحيم

FATIMA MUHAMMAD GURIN.
(Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Marubuciyar:
*Zuhraa*
*Hamrah*
*Igiyar Rayuwa*
*Noor Iman*
*Ruwan Sama..*
*Lelewal*
*GAMON JINI paid*
And Now
*Kowa Ya ga zabuwa..*

*PAGE 10*

*FREE BOOK*

Dama Sila ummi ke nema kuma ta samu, Seda ta tabbatar tayiwa Surayya mugun duka kan ta kira police waenda basu da nisa dasu aka zo aka kwashe kowa aka yi police station, banda kuka babu abunda hidayat take cikin tashin hankali don umma ma Seda aka fitar mata da jini.

A police station ɗin ma ba'a natsu ba kace nace gabaɗaya ya cika wurin, Seda Dpo ya fito da kanshi don jin ba'asin abunda ke faruwa, umma ce tayi Charab tace

"Yallaɓai mijina, marikinta kuma surikinta ta kama da maita, shekaran shi bakwai ana neman na takwas yanzu yana jinya kan daga zuwan yarinyar nan sati biyu da suka wuce ya ce ga garinku, ni kuma alkawari nayi jininshi ba ze tafi a banza ba"

Dpo hidayat kawai ya kurawa ido kaman yana so ya ga ta inda maita ya bayyana a suffanta, ummi tace
"Wallahi karya take! matarnan azzaluma ce, marar tsoron Allah ranka ya daɗe tun hidayat na tsummar goyo take hannunta, banda azabatarwa da bauta babu abunda ta sani na farin ciki a rayuwarta, tare muka yi karatu har zuwa matakin secondary kan kaddarar auren ɗan wannan azzalumar ya hau kanta, shima a gidan bata yi sukuni ko farin ciki na ko da second guda ba, daga mijin har dangin shi sun hanata sakat a rayuwa ai ko me tayi musu abun yayi yawa..! Bare babu abunda ta musu, laifinta ne don bata fito cikin gata ba? Laifinta ne don bata da dangi? Laifinta ne zaɓan wannan rayuwa da take ciki? Ai babu ɗan Adam da ze so zaɓarwa kanshi rayuwa cikin kakani kayi irin na Hidayat..."

Kuka ne ya ci karfinta tayi shiru tana shesheka, kowa a wurin jikinshi yayi sanyi, Asabe tace

"kwarai kuwa yallaɓai tun da muka san hidayat a matsayin makociya bata da wani banzan hali ko mugunta, yarinya ce me cike da kalubalen rayuwa bata jin daaɗi wurin ko ɗaya daga cikin zuri'ar dake kewaye da ita, daga miji har danginshi har ma wasu daga cikin maƙota, wannan matar"

Ta Nuna umma
"ita da yaranta basa sati guda chur basu zo sun musgunawa rayuwar baiwar Allahn nan ba, yanzu ba don Allah yasa akwai jama'a a gidan suka zo da wannan babban maganan ba da kila sede wan labarin ba wannan ba, wallahi duk abunda suke hidayat ko iya ɗaga kai ta kallesu bata yi abun takaicin ma dube ta nan faɗa har police station kuma wai da takaba a kanta"

Dpo da ya tausayawa hidayat sossai sede bashi da wani hurumi a kan aurenta sede ze sama mata sauki ta wani ɓangaren, su Umma ya sa aka saka a cell yace Gobe da yamma hidayat ta dawo a karasa shari'ar don yana so kan gobe suma su ɗandana kaɗan daga cikin halin da suka jefa hidayat.

Kowa tafiya yayi, ummi kaman ta daki hidayat don kuka take tana rokon DPO ɗin akan kar a saka su umma a cell be saurare ta ba har Seda aka cika umarnin shi.

Jiki a sanyaye hidayat ta dawo ita kaɗai take hango masifar da ummi da su Asabe suka sakata, da sun bar umman ta buge ta ta huce ba se abun ya kai ga hukuma ba tunda dae duka baya kisa, ko da ta kawowa ummi maganan ummi cewa tayi

"se kiyi, ina nan a gidan nan har se na ji hukuncin da DPO ze yanke gobe wallahi babu me taɓaki, karki manta ɗinki ne a jikinki ɗanye sharaf sannan taya zasu yi accusing ɗinki da kashe Abba alhali su da wannan banzar hallayar nasu su suKayi sanadin shi, wallahi su kiyayi sakayya da kuma hakki don baƙin cikinsu shine ya kashe Abba"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now