Kiran wayanta ya hana shi magana ta ɗaga tana tambayar ta iso daidai wurin? Ummi ta amsa da eh, basu kara tafiyar mintuna uku ba suka hangeta suka tsaya suka ɗauke ta.

A mutunce suka gaisa da Raed, kan suka gaisa da Hidayat.. Aiko ummi tace
"Hidayat saura mu je ki zubar da hawaye a idanun waennan kaskantattun mutanen har su ga damarki ni da ke ne..!"

Murmushi kawai Raed yayi yana kallon hidayat da ta juya take harararta, Daga yanayin kalar unguwar da suka fara shigowa ummi da Hidayat suka buɗe baki suna kallon ikon Allah, wai anan umma da su Yusuf ke rayuwa?

Tunaninsu be gama kuncewa ba seda suka yi parking aka ce mota ba ze yi gaba ba sede a shiga a fiddo su.

Raed fuskanshi kawai ka gani se ka yi dariya, be taɓa shiga irin wurin a duniyan nan ba, kudaje da kwatami sune flowers da furannin unguwan.

Babu wadda ya fita a mota saboda Abba ma hana Maami fitowa yayi, se Soldiers guda biyu da polisawa guda uku cikin mota biyu da Mahaifin Rashida ya turo ne suka kutsa kai cikin unguwan a take mutane suka yi cirko cirko ana kallon su kaman ba'a kwaryar Kano suke ba, har da masu leke ta gini, ba'a yi minti talatin ba se ga umma, Surayya, Kausar, fahariyya da Yusuf an tuso keyarsu zuwa waje.

Da kallo tsuru tsuru kaman an tare ɓera a lungu suke bin zuƙa zuƙan Motocin da ko da suke da kuɗin ma basu ga irin ta ba bare yanzu, duk akan gwiwowinsu aka saka su zubewa, hidayat tana ta Kallonsu ɗaya bayan ɗaya a zuciyarta tana jinjina ikon ubangiji, a kan Yusuf ta tsaida idanunta zuwa hannunshi da gabaɗaya ya sauya halitta kaman ma ya ruɓa don wani baƙi da yayi, yana zubar da wani farin ruwa, shi karan kanshi ya rame ya tsirance yayi baƙi kirin, kana ganinsu kaga masu cutar tsananin yunwa.

Seda suka kwashe seconds a haka kan Raed y buɗe ya fito bayan ya saka facemask yana Kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kan ya sa hannu ya buɗewa hidayat kofa ya mika mata hannu ta sanya nata ya taimaka mata ta fito a hankali, duk idanu suka zuba musu kaman yadda sauran Jama'ar suke Kallonsu.

A lokacin Abba da Maami ma sun fito, daadida ma ta fito amma yaran kam Raed duk ya hana su fita, ita Aisha tunda ta kalle su ta gane su sede bata yi ko motsi ba don bata kaunarsu kaman yadda basa kaunar ta da mommyn ta.

"Hajiya don Allah kuyi hakuri wallahi bamu san laifin da muka aikata muku ba! Ku yafe mana wallahi bamu da abunda zamu iya baku bayan hakuri don ko abunda zamu sa a bakin salati ma gagararmu yake.. Ku tausaya mana bayin Allah!"
Umma ke rokon hankali tashe, don sanin waennan ɗin ba kananun mutane bane daga motocin zuwa kalar suturunsu da kalar fatar jikinsu.

Surayya da ta kurawa hidayat idanu ne tace
"laaaaaaa wallahi hidayat ce umma! Hidayat ce fa! Hidayat...."

Ta tashi da gudu zata yi kanta wani wawan kafa police ɗaya yayi mata se gata a ƙasa tana sakin ihu, Yusuf, umma, Kausar da Fahariyya a tare suka ce

"HIDAYAT???"

Tana aika musu da kallon da bata taɓa yi musu irin shi ba tace
"Kwarai Hidayat ce ba kuskure idanunku ke gani ba Amina!"

Duk zaro idanunsu suka yi, suna masu tsananin mamakin hidayat ɗin.

Ummi da ta fito ne tayi dariya tace
"Surayya ashe Zaku gane hidayat ɗin haka da sauri? Kun ɗauka da kuka koreta cikin wulakanci da kaskanci rayuwarta ya tagayyara ne? To Allah ba azzalumin bawansa ba! Hidayat ta samu rayuwa me kyau da nagarta gata nan ta dawo muku da mahaifiyarta da mahaifinta, kakarta da kuma mijinta wadda yake wa a gareta sakike!"

Hidayat ta sake cewa
"Amina kin ga uwata da ubana! Hidayat ba shegiya ba ce kaman yadda kuka raine ta da Kalmar shegantaka!"

Maami Umma ta kurawa idanu muryanta na tsananin rawa tace
"Aisha???"

Maami tayi murmushi tace
"kwarai baki yi kuskure ba ni ce dae Aisha da kika rabata da ƴarta a tsummar goyo saboda rashin imani da tausayi"

Umma ta rarrafa ta riƙe kafafun Maami tace
"Na tuba Aisha Don Allah ki gafarceni! Bani da hujjar kare kaina daga laifukana na sani na cancanci a kirani da kowanni suna... Na tuba ki yafe ni"

Maami tace
"zan iya yafe miki laifukan da kika min amma wadda kika aikatawa ƴata ba me yafuwa bane Amina! Me hidayat ta miki kika zalunce ta irin wannan mugun zaluncin?"

Tana kuka sossai tace
"Wallahi wallahi nayi nadama, son zuciya ne kawai da rashin sanin Allah! Don Allah ku gafarcemu yanzu ma abunda muka shuka muke girba, alhakkinku ne yake bibiyar rayuwarmu don Allah ku yafe mana!"

Yusuf yana kuka ya fara magana
"Hidayat ni kam bani da wani bakin da zan iya neman yafiyar ki don na san ban miki adalci a rayuwa ba, na zalunce ki ba tare da na san kaina na zalunta ba, hidayat ina Aisha da abunda kika haifa? Ina yarana....!"

Wani mummunan kallo da bata taɓa sanin ta iya ba ta aika mishi, bazata iya Haɗa jikinta da nashi ba a yanzu haka bazata iya bari mijinta ya taɓa shi ba, da sauri ta kalli Sojan dake tsaye gefenta cikin harshen turanci ta bashi umarnin tana so ta ga jini a bakin Yusuf....

Wasu irin zafafan maruka da ya saka shi tumurmushewa cikin ƙasa ya sauke masa, a tare bakinshi ya fitar da jini a gigice a kuma ruɗe ya samu ya ɗago idanunshi da suka cika da ƙasa yake kallon ta, idanunta da suke rine take Kallonshi dasu tana kaɗa yatsa tace
"Wannan shine ze yi ta zama hukuncinka a duk sadda ka sake alaƙanta min yara da kanka! Ko ka manta na maka gargadi kan tafiyata? Ka manta na yanke duk wani alaka dake tsakanin ku?"

Kausar tace
"amma ai kin san ko me kika yi jininshi ne ke yawo jikinsu so babu yadda kika iya don ba'a chanzawa tuw...."

Kallon da tayiwa wannan Sojan ne ya saka shi sauke mata nata rabon da seda haƙorinta ɗaya ya fita.

Raed hankalinshi duka yana kan hidayat da take neman birkicewa, Kallonsu kaɗai sosa mata abubuwa dayawa yake yi, tana Kallonsu ne kaman tana buɗe shafuka shafukan rayuwarta a idanunta da zuciyarta, aka ce me hakuri be iya fushi ba....

****Menene ra'ayoyinku game da Yusuf da iyalan shi da kuma hidayat??? Shin kuna gani rayuwa kaɗai ya isa koyar dasu darasin abubuwan da suka aikata ko kuwa anan ma hidayat tayi anfani da zuciyar haƙurin ta wurin yafe musu ko barin su da halinsu??? Shin idan Kaine a kafafun hidayat wani irin abu zaka iya aiwatarwa a irin zuciyar ɗan Adam??? Sun chanchanci ƴanci kuwa? Karku manta Allah yace duk wadda be yi anfani da hukuncin da na saukar ba lallai shi ɗin kafiri ne.., fasiki ne.****

#Vote
#share
#comment


                  🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now