Abba yace a kyale su da sun damu ai da sun zo, shi dae Raed ya fita wani taro da aka gayyace shi, planning tafiya Saudia da baba Buba kawai yake, ko ba komai in ya ɗan samu karfi su shiga yayi aikin hajj don ya ragewa kanshi zunubi.

Tunda hamza ya bar gidan ɗauke da hajiyarshi kai tsaye gidan mahaifinta ya nufa, a hanya ya kikkira yayyunta da en uwa na kusa akan su haɗu a gida akwai matsala, bayan an zazzauna a ɗakin taro aka buɗe da Adu'a hamza be ɓoye musu komai ba cikin duk abubuwan da suka faru sbd labarinta izina ne ga en baya masu irin halin ta, ina mijin? Ina dukiyar? Ina lafiyan? Duk ta salwantar da hannunta ba na wani ba.

Daga karshe ya rufe da
"ba na baku labarin bane saboda in tona mata asiri, na faɗa muku ne saboda ya zama dole ku sani kar ku ga kaman Abbana butulci yayi nata a sadda shi ya samu lafiya, zan gyara mata ɗakin inna (mahaifiyarta) zan samu me kula da ita su zauna tare, ku yi mata fatan samun lafiya da fatan shiriya saboda babu wadda ya fi karfin wannan jarrabawar"

Kwarai sun jinjinawa karfin zuciyar hamza, yayi kokari sossai wurin ganin ya hana kanshi tsanar mahaifiyar shi, dukda ya san ta riga ta ɓata mai rayuwa da na zuri'a, kaman yadda ya roka Dukda yadda hajiya balaraba take da nuna isa da son a san ita fa wata ce, haka dae a gaban hamza suka yi mata Adu'ar shiriya da samun lafiya sede babu wadda ya kara da ko Naira biyar bayan nan.

Ɗakin mahaifiyarta da single room ne sbd gidan ba masu karfi bane sede rufin asiri ya shigar da ita, be san a yau ɗin wa ze kwana da ita ba haka ya zauna ya zabga tagumi yana kallonta, daga karshe kuka sossai yayi a haka suka kwana ɗakin ko ta fara bacci zata tashi a firgice tayi ta ihu cikin dare.

Haka ze tashi shima ko yayi mata karatun Qur'ani ko yayi mata Adu'a, da asuba kaninta dake gidan ko gaisuwar hamzan be amsa ba sbd kaman yadda basu yi bacci ba haka shima da iyalan shi dake gidan.

Se rufe ta a ɗaki yayi da safe ya fita, a sannan suka yi waya da Maami da wayan Abba take tambayarshi ko ze shigo ya karya?

Yace ba ze samu shigowa ba ze yi a wurin zainab.

Hakan kuwa aka yi gidansu yaje ba laifi zainab ta tausaya mishi tunda taji labarin wurin mahaifinta, ita ta bashi breakfast kuma ganinsu ya sa ya ɗan samu karfin gwiwa, ta mishi alkawarin neman me aikin da zata iya kula da hajiyar.

Daga nan wanka yaje yayi ya ɗan runtsa, kan azahar ya tashi ya sayi abinci a restaurant ya koma gidan se ya samu ma zainab taje da girki ta taimakawa hajiyan tayi wanka ta bata abincin tana ci, sossai yaji daaɗi a ranshi wani damuwan ya sake raguwa, a nan suka zauna har me aikin da ta kira ta zo, taimakon Allah hajiyan bata duka sede ihu da firgici se surutai marasa kan gado.

**

"Isa ka gane kwatancen kuwa?"

Yace
"ai Alhj sede idan ba cikin birnin Kano yake ba, na gane tsab yanzu zamu isa"

Kai kawai Abba ya gyaɗa kan ya maida hankalinshi kan maganan da suke da Maami a bayan motan, Farrah ce zaune daga gaba.

Daga motan isa se na Daadida ita da Norah ne da Aisha se driver ɗinta, daga karshe kuma Raed ne da kanshi yake driving zaune daga gefenshi hidayat ce, daga baya junior.

Kallonta yayi yadda tayi shiru ta kurawa hanya idanu, hannunta dake kan cinyarta ya sa hannu ya riƙe tare da matsewa, ta kalleshi ta ɗan yi murmushi yace
"please die hard ki daina sawa kanki damuwa akan waennan mutane da basu cancanci damuwarki ba, promise me bazaki yi kuka don tuna wani abu da suka miki a baya ba, yanzu rayuwarki is a better life abunda ko a mafarkinsu basu taɓa hange ba"

Idanunta da suka sauya ta mayar ƙasa tace
"paapi sun yi min illa a rayuwa, sun yi min sanadin mutane biyu masu muhimmanci a rayuwata! Komai aka yi musu ko menene hukuncin su bana ji zan ji sassauci a raina idan har na tuna, sede Alhamdulillah idan na kalli irin rayuwar da Allah ya sauya min se in jinjinawa karfin hukuncin ubangiji dake fitar da rayayye cikin matacce ya kuma fitar da matacce cikin rayayye.."

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now