Mikewa nayi a tsorace na rarumo jakana na rungume, fisgewa tayi tana cewa
"uwar menene ciki da kike mammaƙeta haka?"

Zazzagewa tayi zobuna na suka zubo waenda suke gwal ne masu kuɗi a lokacin guda biyu, ɗauka tayi tana Juyawa ta kalleni tace
"kam bala'i!! Wato Alhj ya iya saya miki gwal kina karuwarsa ni matar gida be sayawa ba?"

Girgiza kai nake ba tare da nace komai ba, mari ta sauke min tace in zo in fitar mata daga gida kan ta kulle idanu ta buɗe zobunan kuma wlh bazata bani ba tunda da kuɗin mijinta aka saya.

Kuka nake son yi ta fincikoni tare da toshe min baki ta ja ni har wajen gate ta cilla ni na faɗi har Seda goshina ya fashe da dutse, raina ne ya ɓaci ban sani ba ko aljannun da aka Haɗa ni dasu ne ko yaya kawai ina mikewa na dau hanya ba tare da ko waiwaye ba.

Seda nayi tafiyar da ban san na awa nawa ba gari dae yayi shiru kan na iso wani rumfa inda buzaye suke zube sun hura wuta, anan na shiga cikinsu na kwanta basu ganni ba seda safe, sun tsorata macen ta tashe ni, ina farkawa mijin yace kar kowa ya min magana, wasu Adu'a ya dinga yi min kan yace
"Baiwar Allah!"

Na kalleshi sede ban yi magana ba, yace
"hoo innalillahi wainna ilahi rajiun duniya ina zaki damu jama'a? Laure wannan mata na shikin masifa tana matukar bukatar taimako"

Matar tace
"to me gida ba se ayi wani abu ba?"

Yace
"yo ai ba ze yiwu anan ba duk abubuwan suna chan gida gashi kudu muka nufa"

Tana kallona cikin tausayawa tace
"kayi hakuri mu koma Nijar me gida! Wannan baiwar Allah duk inda danginta suke na tabbatar suna shikin tashin hankali"

Haka gamji da matarshi Laure suka fasa wannan tafiya suka tafi dani Nijar, na sha wahala sossai wurin adapting rayuwarsu, nayi jinya me yawa wadda har na kan yi wata ba tare da na san inda kaina yake ba, abun ya zo ya fi karfin Gamji Seda ya Haɗa da neman taimako a wasu nahiyar na Nijar.

Tsawon shekarun ashirin ina fama da jinya don se haukan yayi kaman yayi sauƙi se kuma ya taso, na samu lafiya shekaru uku baya inda komai ban manta ba, na basu labarina gabaɗaya saboda sun zama kaman yayyina sun riƙe ni da amana matuka, basu taɓa saka lomar wani abu a bakinsu ba tare da na saka ba, ko da suka ji labarina wadda ina zuwa wurin barin jinjirata da ba zan iya tuna fuskanta ba se kuka da firgici su rufe ni, ta ina zan fara neman ta? Kuma ta yaya? Wlh ko sunan Wannan bawan Allah da ya taimakeni ban sani ba bare unguwar da yake a birnin Kano.

Mun kara delay na shekara uku kan mu zo ne sbd tsananin rayuwa da gamji yake ciki ya sayar da duk dabobbin shi wasu yayi asarar su duk ta hanyar neman min lafiya don aljannun sun sha kashe mishi garke gabaɗaya sbd ni akan ana mishi gargadi ya Rabu da ni da rayuwata babu ruwanshi.

Da muka samu kuɗin suka taru kuma fita ƙasar Nijar ya gagareni seda muka yi ta biyan wasu kudade kan muka iya fitowa, mun kwana Kano kan muka nausa Gembu seda muka samu kab labarin abunda yake faruwa gidan Buba kan muka nemi layin mama, matarshi Badi'ah ta bamu shine muka kira, ko da muka iso Kano da neman taimako muka samu me adaidaitan da ya ɗauko mu zuwa wannan gida don ko biyar bamu tsira dashi ba kuma..."

Shiru tayi tana share hawayen fuskanta, tana me cigaba da shafa kan Hidayat da take ta kuka har da majina, Abbanta da ya hamza ma kuka suke yi duk dauriya irin ta maza, sossai jikkunansu yayi sanyi babu wadda ya iya magana se muryar Hajiya Balaraba suka ji ta fara cewa

"Hahahahahhaha ba kin dawo ba! Dama ya faɗa kina dawowa se na haukace ai kaikayi koma kan mashekiya ne! Aisha ke azzaluma ce, ina zaman zamana da mijina tun kan yayi kuɗi har yayi arziki shine ya tsallake ya auro ƴar gembu waenda ba inda labarin kyaunsu be je ba! Yana so ni balaraba in zama bora ya sa kyakkyawa gaban mota Hahahahahhaha"

Ta sosa kai ta sake gyara zama kan tace
"ni ce nan na je wurin neman taimako aka taimaka min ake sakar miki da ciwon ciki me tsanani da kuma zuban jini duk kwananki...! Hahahahahhaha kin ɗauka ban sani bane har da bani labari.... Ai wannan malamin ma ba malami bane ruwan asiri na yayi ta baki as magani ke kuma wawuyar kika yi ta amfani dasu har asirin warin jaɓa ya shige ki..."

Kallon maman Rashida tayi tana kwalalo idanu tace
"ke Adama ke munafuka ce! Har abada a matsayin hoto na so Aisha ta zauna gaban Usman se kika min zamba cikin aminci kika karya mun magani ba tare da na ankare ba.... Boka na yace min tunda har wannan ya karye babu yadda na iya sede in fara Haɗawa da kissa irin ta mata su zasu na aiki har gunki ya basu nasara..."

Hararan Aisha tayi kan ta kwashe da dariya se ta fara kuka tace
"Munafuka! Algunguma kwai na guda ɗaya jal na gani gidan Usman amma ke! ke seda na zubar miki da ciki har bakwai na karshe da ya fara girma na baiwa Boka suka shanye mai jini suka musanya shi da kadangare sbd duk maza ne"

Hahahahahhaha tayi dariya kan ta cigaba
"kuka maida ni shahasha kuka koma inda ban isa in taɓa ku ba baku dawo min ba seda ciki, na harzuka naje wurin Boka me taimako na, maji roko na! Yace tabbas cikin nan haifaffe ne be kuma san mace bane ko namiji don basa iya gani...! Na ji haushi raina yayi baƙi nace ya kashe ki Aisha ko ya ɓatar min dake in dena ganinki a rayuwata"

Sosa jikinta da ya fiddo wasu manyan kuraje tayi tace
"kin san me yace min? Munafukar bazata mutu ba sede a ɓatar da ita, amma duk shekara za'a dinga zubdawa aljannu jini sbd su kasance cikin gaskiya a aikinta, million biyu"

Ta Nuna da hannunta tace
"ko wani farkon shekara se na kaiwa Boka million biyu ya zubarwa aljannu jini... Ni ban ma san ko na mutum bane ko na dabba Hahahahahhaha..... Sharadin shine duk ranar da kika dawo ko jininki ya dawo har yayi ido biyu da Alhaji kaikayi ze koma kan mashekiya, ya ce min baze bari ku haɗu ba sbd barbushe ya bashi sa'a...! Yace har ku mutu bazaku sake arba da Usman ba! Munafukar ɗiyarki ta fara dawowa... A fujajan na tafi Kwara wurin Boka sede na samu dajin da yake ya ƙone kurmus babu abunda ya saura shi karan kanshi ko ƙashinshi ba'a samu ba! Shikenan na haukace Aisha ta haukatani... Kaikayi fa ya koma kan mashekiya, wallahi ya koma hahahahaaaaaa"

Cikin tsananin kuka hamza yace
"Hajiya why????? Meyasa hajiya? Hajiya kin cuceni kin cutatar min da rayuwa innalillahi wainna ilahi rajiun.... Menene ribarki? Me yasa kika zama uwata a duniya????"

Kuka yake sosai wadda seda zuciyar kowa ya tabu Dukda kowa na cikin shock da jimamin jin wannan mummunar labarin daga hajiya... Alhj Usman yana zub da hawaye yace

"Allah a gode maka! Allah na gode maka da ka jarabceni da samun irin wannan mace a matsayin mata! Balaraba kin cucemu, kin cuci mata ta da ɗiyata da ni karan kaina sede na gode Allah da ya nuna miki iyakar ki ya maidani Hoto a gabanki ni da kike son mallakewar, me ribar ki??? Kin raba Aisha da ni don in zama naki ni kaɗai, a ranar da Aisha ta tafi a ranar na bi hanyar gembu cikin tashin hankali da talatainin dare na faɗi cikin tsaunuka wadda na shekara ashirin ban anfane ki da komai ba! Ban farka ba kuma Seda ana gab da dawowar Aisha da Hidayat gareni, kin ga ikon Allah ko? Wallahi wallahi ba zan taɓa yafe miki wannan zalunci ba Balaraba, Allah ya isa wahalar Aisha..."

Kuka ne ya kubce mai kaman ba babban mutum ba, Daadida na zub da hawayen tausayi tace
"Hidayat!"

Idanunta da suka kumbura suntum ta ɗago ta kalli Daadida, Daadida tace
"Aisha ta barki hannun Amina, A labarin Aisha Amina bata da mutunci bata san shi ba, shin ya rayuwa ya zame miki hannun ta da iyalinta?"

Raed da idanunshi suka sauya ne sbd damuwa yace
"A'a Daadida don Allah! Ku ji tausayinta mana, kukan nan ya isa haka zuciyata na gab da samun matsala in ta cigaba... I cannot take it anymore!"

Da gaske zuciyarshi na beating fiye da yadda ya kamata ya buga, har daci yake ji a makogoronshi.... Kallonshi hidayat tayi tace
"I'm fine..! It's OK"

Yayi saurin cewa
"no you are not fine, it's not ok please die hard not now, not today"

Abban Rashida yace
"Raed kayi Hakuri ka barta ta bayar ɗin sbd iyayenta na so su ji irin rayuwar da tayi! Ina Alhjn da ya taimaka ma mahaifiyarta yake a yanzu da take a matsayin matar ka bayan ta aureka ne as me aikin gidanka! Ba tare da dangi ko zuri'a ba..."

Runtse jajayen idanunshi yayi ba tare da yace komai ba.

A hankali hidayat ta fara bada labarinta....

#Vote
#share
#comment



                🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Donde viven las historias. Descúbrelo ahora