Hannu ya sa ya matsar da ita yace
"wuce baiwar Allah"

Na wuce ya biyo ni zuwa karamin sashen dake daga gaban wannan ɗin, da sauri ta kuma shan gabanmu tace
"ɗakin ka zaka kai ta?"

Yace
"eh tunda nan kam ba naki bane baki da hurumin hanani ko yi mini iko"

Bori sossai tayi tayi wadda wasu ba zan iya tunawa ba akan kilan cikin ma nashi ne dangina suka koro ni na dawo mishi da abunshi in ba haka ba ina ze sameni da sassafen nan, babban damuwarta kankantar shekaru da kyau na Dukda sossai ya ɓuya sbd wahala.

Daga karshe ganin da gaske sashen shi ze ajiyeni tace ta hakura in zauna sashen ta, haka muka koma ta bani extra room, be barni ba seda ya tabbatar na ci abinci nayi sallah, ina gabamawa nayi pillow da jakana as usual na hau bacci.

Dukda kasancewar Amina mace ƴar uwata sede ko sau ɗaya bata taɓa jin tausayina ba a zamana da ita Dukda taga banda cikakken lafiya da hankali, bayin ta babu pampo se wurin wanke wanke, da safe zata saka ni diban ruwa in cika mata randunan bayi, in yi wanke wanke kan ta bani abin karyawa, abincin rana wani lokacin se yamma idan Alhj ya dawo mutum me tsananin mutumci da karamci ze ɗauki nashi ya bani Dukda barazana da matarshi ke mishi a kaina iri iri.

Na zauna na tsawon sati uku a gidan bana yiwa Kowa magana tun ruwa da nace ina so ban sake cewa kowa tak ba, da dare Alhj ya kan zauna ya tambayi suna na, mijina, garin da na fito ko wasu en uwana amma babu abunda nake iya ce mishi ko nake tunawa.

Wata rana na tashi da nakuda bayan na ɗibi ruwa ina a na karshe cikina da bayana suka riƙe sossai, ban iya karasawa ba bokitin ya faɗi nan tsakiyar parlor ya jike Mata ɗaki, wani irin bangaza tayi mini ta hau zagi na babu irin sunan cin mutuncin da bata kirani ba har marina Seda tayi akan se na gayamata gaskiya mijinta ne uban ciki na?

Ina fama da wahalar nakuda hakan yasa duk abunda take yi ɗin ban ma san tana yi ba, ta saka ni na share mata ruwan da na zubar ina cije baki da komai a tsugune na yi aikin ban iya komawa ɗaki ba nan tsakar ranan na faɗi ina shan azaba, matar nan bata fito ba bare ta kulani na fi awa uku a wurin har jini da ruwa suka fara bin kafafuna ga rana ana yi na jike sharkaf da zufa, da taimakon Allah Allah ya turo Alhj Dukda yaranta na nan suna kai kawo sede kallo babu wacce tayi min.

Hankali tashe ya kirata ta zo ta taimaka min mu tafi asibiti tace ba da ita ba, lokacin da aka yi abunda aka yi ba'a gayyace ta ba se yanzu, haka ya taimaka min sbd babu yadda ze yi muka je mota ya kaini asibiti, da kyar suka karɓe ni seda suka yi faɗa sossai akan rashin kulawa da sakaci da aka yi gashi ba wurinsu nake zuwa awo ba.

Bayan baƙar wuyan da nasha na haifo yarinya mace, ina haifanta kuma na fara wani kalar bacci kaman wacce ta bugu, su suka mata komai har nono suka bata ba tare da na sani ba.

Se washegari da yamma bayan sun gama bincikensu suka bani sallama, tunda na farka kuma se hauka na muraran ya bayyana, ba zan ce na riƙe yarinyar ba sbd Alhj tsoron bani ita yake kar na yarda ta.

Muna dawowa Amina ta sake tada sabon bore, Seda suka kai ruwa rana kan na shiga ɗakin da suka saukeni, da farkon dare ya kawo min yarinyar yace
"Baiwar Allah ya kamata kiyi magana ko sunanki ne mu sani! Babu daaɗi yadda Amina take adressing naki da sunaye marar kyau"

Kallonshi nayi kaman zan ce wani abu se nace
"Aisha! Aisha!!"
Ina ta maimaitawa Seda ya gaji yace
"sunanki Aisha?"

Kai na gyaɗa yace
"daga ina?"

Ban yi magana ba se jaka na buɗe na fiddo box na miƙa mai nayi murmushi, karɓa yayi yana Juyawa kan ya ɗago nayi bacci fita da yarinyar da ko kukanta ni ba zan ce ga yadda yake ba yayi, madara ya sa aka sayo mai ya bata a tare suka kwana.

Karfe Taran dare naji ana tashina, ɗago kai nayi na kalli Amina ta zaro min idanu tace
"tashi tsohuwar munafuka ki fitar min daga gida.. Ai nayi kokari tunda kika yi sama da sati uku"

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now