Page10

4 0 0
                                    

FARGAR JAJI
                  Na
  Aisha Abdullahi yabo

         *October/Fitattu5 2023*

*PAID.*
BOOK

Pej10

Ummi da take linki kayan da Abba ya cire ta kai dubanta gare shi tana faɗin "ba ka ce komai ba"
  "Na rasa me zan ce ne ma, ban taɓa tunanin Aisha za ta yi wa Nasir da mu kanmu irin wannan tijarar ba ko kaɗan, amma ba komai je ki kira mini ita" kai kayan tayi tasa a wadrp "bari na duba ta Allah yasa ba tayi bacci ba"
"Ko tayi bacci ki tashe ta!"
"To shi kenan."  Zaune ta same ta a tsakiyar gado tana kuka tsayawa tayi daga bakin ƙofa "ashe kuwa aiki ya sameki in har kika ce za ki sa wa kanki damuwa da kuka, dan ba abinda zai sauya in har ki ka ga ba ayi auren nan ba ki tabbatar da ba ranmu ko kuma na ki ran. Ki  mu je Abban ku na kiran ki" barin ɗakin tayi ba tare da ta jira jin me za ta faɗa ba. Bayan hannunta tasa tana goge hawayen da ke kwaranyowa a kan fuskarta kallabi ta ɗauka ɗorawa tayi akanta, ƙafa ba ko takalmi ta shiga ɗakin Abba ta samu suna falo, ɗan nesa da shi ta zauna "ga ni Abba"   harararta yayi yana faɗin "na ji duk irin tijarar da kika yi wa Nasir na gode sosai domin ni kika yi wa ba shi ba"
   "Kayi haƙuri" tayi maganar kanta a ƙasa tana zubar da hawaye. "Haƙurin uwa ki! Na ce haƙurin uwa ki! Wato so kike ki nuna ban isa da ke ba?"
"Ba hakan ba ne, ni wallahi ba na ƙi jin maganar ku ba ne, ni maganar soyayya bata taɓa haɗani da shi ba. Sannan sa ni ne ba ku yi ba wallahi Yaya Nasir ba sona yake ba idan har kuka aura mini shi kashe ni zai yi da muguntar sa"
  "Aisha ai na ɗauka ko cikin wuta na ce ki faɗa za ki faɗa bare Nasir da nake da tabbacin ko bayan raina zai riƙe ku da amana. Dama ban ce dole sai kina son shi ba ko sai ki so shi" nunata ya yi "ki sani aure dai babu fashi, kuma wata mai fita za ayi aure kya ƙarasa karatun a gidan ki!" Firgice ta kalleshi "aure kuma wata mai fita? Don Allah Abba kayi haƙuri wallahi zan iya mutuwa idan har ka aura mini shi, ni Abdul nake so ba zan iya rayuwa idan babu shi ba"

"Ba mu san ba za ki iya rayuwa babu shi ba har sai an kai ki gidan Nasir kin zama mushe, sakaryar banza marar tunani!"
   "Wayyo Allah na mutu na lalace don Allah ku mini rai kar ku aura mini shi wallahi na tsane shi! Da gaske nake mutuwa zanyi idan ku ka rabani da Abdul!!" Nasir da har ya hankaɗa labule zai shiga kalaman suka faɗa kunnensa da sauri ya saki labulen ya bar wajan. Takaici ya rufe Ummi ta kai mata duka Abba ya ɗaga mata hannu "daina dukanta. Ba ihu ba ko mutuwa za ki yi kina dawowa ba zan taɓa sauyawa daga hukuncin da na yi ba, maza ɓace mini da gani!" Barin ɗakin tayi da gudu tana ihu kuka. Riƙi baki tayi "ikon Allah yau ni Maryama naga abinda ya fi zare tsaye, anya Alhaji ba aljanu ne a kan Aisha ba dubi yadda take yi mana ihu muna faɗa tana faɗa"
   "Ba wani aljanu shegantakar banza ce, tayi haukarta ta gama ba abinda za a fasa"
"Uhm! Allah ya kyauta" gyara zamansa yayi yana faɗin "Amin."

Da ƙyar ya iya kaiwa falon shi saboda jirin da yake ji, zaman dirshin yayi idanunsa a rufe yana mayar da numfashi kifi kanshi yayi jikin kujera 'innalillahi Wa Inna ilahi raji'un, allahumma ajibni fi musibati wa ajibni khairan minha' addu'ar da yayi ta maimaita wa a zuciyarsa har natsuwa ta zo masa. Wanka yayi  haɗi da ɗauro alwala hakan ya raya daren cikin ibada da ambaton Allah dan neman mafita. Ki ɗauki abincin Yayan ki ki kai masa kafin ki tafi islamiyar"
   "Ai ba ya nan" ta faɗa tana sanya takalmi "wallahi Ummi yana nan bai jima ma da dawowa ba"
"Ni take so ta mayar shasha, maza wuce ki kai masa!" Cikin turo baki ta je kichin ta ɗauki abinci "kowa ma ba ya sona a gidan nan Allah yasa ma na mutu kowa ya huta"
  "Shi kenan idan kin mutu ai mun huta ba kuma za mu fasa rayuwar farin ciki ba marar kunyar kawai!" Fau ta ɗauki abinci ta fice tana kuka "Aunty Aisha jakarki fa, ko na zo maki da ita ne?" Tsayawa tayi ta waigo a fusace "wallahi Ƙasim idan ba ka fita sabgata ba sai na ɓaɓɓalaka na yayyaga ka banza kawai!!"
   "Tab mu dai ɓaɓɓalla juna, duk shekara nawa ma kika ba ni da kullum kike cika bakin za ki dakeni, ba dan Ummi da Abba suna hanani ba ai da tuni mun cire raini tsakanin ni da ke"
   "Ban son rashin kunya Nasir maza kamar hanya kayi tafiyar ka, kuma idan na ji labarin kunyi faɗa a hanya ko makaranta daga kai har ita ba za ku ji da daɗi ba" fankan-fankan ta bar wajan tana magana ciki-ciki. "Ummi ki mata magana ni ba zan kulata ba ita ce dai na san za ta iya cewa ta dakeni a gaban abokaina"
   "Kaima ai jan faɗa ne ya ma yawa ina ruwan ka da ita, ka san halinta ba sai ka ci maganin zama da ita ba. Ba na son haka" ɗaukar jakarsa yayi "kiyi haƙuri"
   "Ka dai kiyaye ba na so"
"Na daina Ummina. Na tafi "
"Allah ya tsare ya ba da ilimi mai albarka. Kar kuma ku tafi ku jira ta fito ku tafi tare"
"To."

Fargar Jaji Where stories live. Discover now