Page7

2 1 0
                                    

FARGAR JAJI.
               Na
Aisha Abdullahi Yabo

                     *October/Fitattu5 2023*
Pej7

Wata matashiya da take tsaye gefen hanya ta janyota da sauri har sai da suka kai ƙasa, ajiyar zuciya ya saukar yana mai dafi zuciyarsa da yake jin ƙiris ya rage ta faso ƙirjinsa ta fito. "Haba 'yar'uwa ya kike tafiya ba kya kallon hanya da ba dan Allah ya tsare ba tabbas da ko ba ki mutu ba za ki samu rauni"
   "Uhm! Na gode" abinda kawai ta iya faɗa ta miƙe tsaye tana kakkaɓar jikinta mai motar da ya samu ya ci burki wanda hakan ne ya taimaka wajan kaucewa hatsarin gefen hanya yayi Pakeng samunsu yayi a wajan tana gyara zaman jakarta ya kai hannu zai mareta Abdul ya riƙi hannunsa "akan me za ka mareta?"
"Har ma tambayata kake? Kai baka ga abinda tayi ba ne da ba dan Allah ya kiyaye ba da yanzu ban san a wani halin muke ba daga ni har ita"
"Na yarda tayi kuskure amma kuma ai baka san dalilin yin hakan ba, ka san duk wanda yake cikin hayacinsa ba zai taɓa tunkarar titi kansa tsaye ba tunda ba ɗakin kwanansa ba ne" tashin hankalin da take jinta a ciki bai iya sa ta tsaya sauraren su ba ɗan a-dai-daita-sahun da ya ajiye wasu ta faɗa tana faɗa masa unguwar da zai kaita.  Hangota da yayi za su wuce yasa ya biyo ta da sauri "Aisha!" Tun kan ya kai har sun wuce tsayawa yayi yana saukar da ajiyar zuciya.  "Ikon Allah wato shi ƙoƙarin kareta ma yake yi ba wai ganin laifin abinda ta aikata ba, lallai wannan mutumin ma"
    "Tunda ka ji yace bata a hayacinta ya kamata ka karɓi uzurinta, dan kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci hakan ɗin, sannan dukansu sun tafiyarsu kaga  gara ka tafi inda za ka tafi Allah ya kiyaye gaba kuma" matashiyar ta faɗa tana tarar mashin, ƙwafa kawai yayi ya tafi wajan motar shi yana faɗin "Allah na gode ma wannan yarinya da ta jaza mini masifa."

Tafe suke gaba ɗaya zuciyarta ta tafi cikin tunani ta kasa yarda da maganar Abdul 'taya ma Yaya Nasir zai ce haka ya ma za ayi hakan ba tare da sani na ba, kai ina ba ma zai  yu ba ba mamaki ya masa hakan ne saboda ya kore shi' riƙi kanta da yake matuƙar sara mata tayi 'innalillahi Wa Inna ilahi raji'un! Ya ilahi ka taimakeni kasa kar hakan ya zama gaskiya tabbas da na shiga tara ba ma uku ba wallahi!'
   "Hajiya mun ƙarasu unguwar ta ina zan ajiye ki?" Shiru ba amsa ɗan juyowa yayi "Hajiya ba kya jina ne?" Ajiyar zuciya ta saukar kafin daga bisani ta ce. "Ka yi haƙuri ban ji ba ne"
"Ba damuwa ina zan ajiye ki?" Nuna masa hanya tayi har suka ƙarasa gidan yana tsayawa ta fito har ta fara tafiya "kuɗina Hajiya" riƙi kanta tayi "oh Allah yi haƙuri don Allah" bayan ta bashi kuɗi ta shige gida ko sannu da mai-gadi yake yi mata bata amsa ba. Sashen Yaya Nasir ta nufa zuciyarta na dukan uku-uku a rufe ta samu ɗakin hakan ta juyo sai a lokacin ta kula da ba mashin ɗin shi cikin takaici ta shiga sashen su.

Ummi da take fitowa kichen ta kalleta da mamaki "lafiya kika dawo daga tafiyar ki?"
   "Banda lafiya"
"Ƙarya kike rashin son zuwan makarantar ne dai ya sa ki yin ƙarya ba wani ciwo da kike" turo baki tayi tana tafiya ɗakinta "shi kenan mutum bai da lafiya ba za a tausaya masa ba sai dai ma a ƙaryata shi"
"Ƙaryar kika saba yi shi yasa marar kunya kawai" komai bata ce da ita ba tayi shigewarta ɗaki. Sai safa da marwa take sam ta kasa zama "Yaya Nasir baya nan to waye zai bani amsoshin tambayoyina?" zama tayi gefen gado can kuma ta miƙe kamar wacce aka tsikara da allura ta fice ɗakin.

Ta samu Ummi na kallo zama tayi kusa da ita "ya aka yi ne ko har ciwon ya tafi?"
   "Uhm ni wata tambaya nake so nayi maki"
"Ina jinki" shiru tayi tana tunanin ta tambayeta ko dai ta bari har ya dawo, ji tayi ba za ta iya jiran dawowar shi ba, "Ummi wai gaskiya ne abinda Yaya Nasir ya faɗa?"
"Me ya faɗa? Shiru tayi kamar ba za tayi magana ba "wai mene ne kin sa ni gaba kina ta kallo"
"Um dama wai cewa yayi tun ina ƙarama kuka tsayar mini da shi a matsayin miji" zuba mata idanu tayi wanda ta kasa tantanci irin kallon da take yi mata hakan yasa ta ƙara tsurewa "shi ne ya faɗa maki hakan?"
"Ni ba ni ya faɗawa ba dama a kwai..." Sai kuma tayi shiru "kinyi shiru"
  "Ina jin tsoron kar na faɗa maki ki mini faɗa"
"Sai idan abin faɗan kika yi shi yasa kike jin tsoro, faɗa mini me ya faru kuma ban son ƙarya kin sani"
'wayyo Allana me yasa ban bari har ya dawo ba ga shi ina shirin yiwa kaina tonon silili' maganar Ummi ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi "tambayar ki nake fa!"

Fargar Jaji Where stories live. Discover now