Page6

0 0 0
                                    

FARGAR JAJI
                  Na
  Aisha Abdullahi yabo

*October/Fitattu5 2023*

*PAID.*
BOOK

Pej6

Ummi ce zaune tsakar gida a kan tabarmar tana ta faɗa "matsalata da Aisha kenan ta matsa a barta zuwa biki idan an barta sam ba za tayi tunanin ta dawo cikin lokaci ba sai ta kai dare. Ƙasim kana ina ne ko har yanzu ba ka idar da sallar ba ne?"
"Gani nan yanzu na idar!"
"Yi ka fito ka zo ka dubu ta don Allah tun kan Abban ku ya dawo ya samu ba ta nan" Nasir ya shigo da sallama abakin shi zama yayi kusa da ita "ina wuni"
"Lafiya Lau Nasir, ya aikin na ku"
"AlhamdulilLah da godiya"
"Ummi ni fa ban san ina ta tafi ba" kai dubanta ta yi gare shi tana faɗin "gidan su Hanna za ka je ka ga ko suna tare"

"Waye ake nema?"
"Aisha mana, tun kan azahar ta bar gidan nan amma har anyi Isha shiru ba ta dawo ba" 
  "Haba tun kan azahar kuma? to ina ta tafi?"
"Humm bikin Yayar ƙawarta Hanna ta je da har na ce ba za ta je ba shi ne fa ita da ƙawayenta Fatima suka sani gaba da magiya akan na barta, duk gargaɗin da na mata yarinyar nan sai da ta kai dare" ransa a ɓaci ya tashi "yi zamanka Ƙasim bari na je da kaina"
"Yawwa don Allah idan kun haɗu tun daga can ka fara zane mini ita karka raga mata" komai bai ce da ita ba yasa kai ya fice.

Tsaye take bakin gyet da waya kanne a kunnenta sai murmushi take "Oh Abdul kafiyi rigima kamar ba yanzu muka rabu ba"
   "Kin san ba na gajiya da sauraren daddaɗar muryar nan taki, Allah na ƙagara ki zama mallakina"
  "Humm yanzu dai ka bari na shiga gida na san Ummi na can na jirana, idan nayi sallah zuwa anjima sai muyi magana" ajiyar zuciya ya saukar "shi kenan ki kular mini da kanki. I love you"
  "Love you t... hannunta ya fara kirma lokacin da idanunta suka sauka akan shi yana huce tamkar tsohun kumurci, wayar ta suɓuce mata jikinta sai kirma yake. Duƙawa yayi ƙasa ya ɗauki wayar  ya haɗa tare da miƙa mata wayar "ga wayar ta ki" kuka ta fashe da shi "don Allah ka yi haƙuri wallahi sai da na ce ba z... "Shiii!! Na tambayi ki ne, cewa na yi ki karɓi wayar ki ban tambaye ki wata magana ba"  sunkuyar da kanta ta yi ƙasa ta na ci gaba da kuka yau kam tabbas mutuwar ta ce ta zo dan ta tabbata idan ya fara dukan ta sai numfashin ta ya tsaya cak ko zai ƙyaleta. Ta yi maganar a zuciyarta na dukan uku uku. Hannunta ya janyo ya ɗora mata wayar a tafin hannunta ya bar wajan. Tafiya ya ke ya na haɗa hanya. Ganin ya tafi ba tare da ya ce da ita komai ba hakan sai ya ƙara jefa zuciyarta a cikin komar tsoro. Sai da ta share hawayen fuskarta tare da ƙoƙarin haɗiye kukan sannan ta wuce cikin gidan.

Ta na shi ga Ummi ta harareta "kin kyauta, kin kuma kashi hanyar gobe" gabanta ya ba da dum! Da ba a gabanta ya shiga sashinsa ba da sai ta ce ko ya zo ya faɗawa Ummi ne, 'to ko a waya ya kira ya faɗa mata?' Ta yi tambayar a ranta. "tsayen me ki ke a kaina za ki shi ge ko sai na wanka ma ki mari! Girma ki ke amma sam hankali ya ƙi zuwa maki tun kan azahar ki ka bar gidan nan shi ne dan rashin tunani za ki zauna har bayan isha saboda bikin na ƙanwar uban ki ne!" Ajiyar zuciya ta saukar 'tun da dai ba wacan maganar ba ce ai da sauƙi' ta yi maganar a zuciyarta.

   Ƙarasa wa ta yi gabanta ta na marairaici murya ta ce. "Ki yi haƙuri ba zan ƙara ba"
   "Ki ma ƙara ɗin idan na sake barin ki zuwa bikin gidan ƙawa" ta yi maganar ta na shigewa ɗaki. Jiki a sanyaye ta shi ge ɗakinta ta faɗa banɗaki. Ta na idar da sallah kiran Abdul ya shigo ƙin ɗaga wa ta yi dan a tsorace ta ke, ƙarshe ma kashe wayar ta yi gaba ɗaya ta koma ta lafe kan gado motsi kaɗan ta ji sai ta zabura a zaton ta Nasir ne ya zo dukan ta. Baccin ma ta kasa yinsa cikin daɗin rai.

Nasir tun da ya shiga ɗaki ya kwanta tare da lulluɓa cikin bargo dan wani irin sanyi ya ke ji can cikin ƙassan jikinsa, wani irin abu mai nauyi ya tsaya masa a zuciya. Faruk ne ya shigo ɗakin ko ina duhu kunna hasken fitilar wayarsa ya yi ya na faɗin "ko ba kowa ne?" Ya yi tambayar ya na kunna makunnin fitilar ɗakin ya haskaka. Ganin mutum kwance a kan gado ya na karkarwa ya ƙara sa bakin gadon ya na faɗin "SubhanalilLah! Nasir lafiya?" Shiru ba amsa zama ya yi gefen gadon ya yi bargon  hawayen da ya ga ni kwance a kan fuskar Nasir ya ɗaga masa hankali "na dai san ciwo ba ya sa ka kuka mutuwa a ka yi ne?"

Fargar Jaji Where stories live. Discover now