Page9

5 1 0
                                    

FARGAR JAJI
                  Na
  Aisha Abdullahi yabo

         *October/Fitattu5 2023*

*PAID.*
BOOK

Pej9

Kishingiɗi ta same shi akan kafet yana sauraren labarai "salamu alaikum" kai dubansa yayi gareta yana mai amsa mata sallamar "me ya faru kuma kika tsaya?"
   "Ba komai" ta ba shi amsa tana mai zama kusa da shi, gyara zamansa yayi idanunsa a kan ta "ba ki da lafiya ne?" Gyaɗa masa kai tayi "a'a"
"Me ya faru naga duk kin sauya ko ke da Umminku ne?"
"A'a Abba ba komai fa. Ina kwana"
"Shi kenan tunda kin ce ba komai. Lafiya lau" idanunsa akanta ya ce. "Waye wanda aka ce an ganku tare da shi?" Ƙyabci-kyabcin idanu ta shiga yi tana mai ɗan ja da baya "tambayarki nake waye shi kuma tun yaushe kuke tare?"
  "Kayi haƙuri Abba mun jima tare kuma tsoro yasa ban bari ya zo gida ba dama na bari ne sai mun kammala karatu sai na kawo shi gida" jinjina kai yayi "ban taɓa kawowa a raina Aisha za ki iya fara soyayya da wani har kuna haɗuwa a waje ba tare da mu iyayenki mun sani ba, na yi mamaki  sosai da na ji wannan labarin, kuma tsoro ya shigeni da tunanin lallai tunda har kika iya ɓoye mana al'amari irin wannan tabbas komai za ki iya aikatawa a bayan idanmu"
  "Wallahi ba hakan ba ne wannan ma tsautsayi ne Abba kayi haƙuri na tuba ba zan sake ba wallahi ba zan sake ba"
   "Daina rantsuwar ko kuka duk ba zai sa na sake yarda da ke ba, koma miye ai ya riga da ya wuce"  bayan hannu tasa tana share hawayen da suke ta kwaranyowa daga kurmin idaninta ta ce. "Da gaske nake ba zan sake ba, kuma zan ma faɗa masa ya zo kuyi magana da shi ba zan sake haɗuwa da shi a waje ba" murmushi yayi "ni ba sai kin turo mini shi ba, yadda kuka haɗu ba mu sani ba ba na buƙatar na ma san shi ki dai yi ƙoƙarin dakatar da shi daga zuwa wajanki a ko ina ma ne dan na riga da nayi maki miji" kallonsa tayi firgici "miji kuma Abba?"
"Miji fa, Yayanki Nasir shi ne na zaɓa maki a matsayin abokin rayuwar ki" ihun kuka tasa da yasa Ummi tayi saurin ƙarasa shigowa "ke lafiya wannan ihun fa na miye?"
"To tayani dai tambayarta daga magana tasa mini ihu kamar wacce aka aikuwa da saƙon mutuwata"

"Ni wallahi ba na son shi, shi ma da ya faɗa maku yana sona ƙarya yake yi so kawai yake ya rabani da farin cikina ya kashe mini rayuwata, mutumin da koyaushe duka da zagi ya ke yi mini kuma har za ku yarda da shi  wallahi ni ba zan yarda ba."
   "Aisha rashin kunyar ta ki har ta kai ana faɗa kina faɗa, mahaifanki ya yanki hukunci ki ce bai isa ba!" Ɗaga mata hannu Abba yayi "kinga Maryam ba na son faɗa abinda duk lumana ba tayi ba faɗa ba zai yi shi ba. Ke Aisha faɗa mini me ɗan'uwanki yake yi maki da ba kya so?"
  "Dukana fa yake yi ya zageni, ya sa ni aiki mai wahala. Kuma shi ne za a ce na aure shi salon na je ya ƙarasa ni. Shi fa mugu ne na bugawa a jarida"
"Ko me ya yi maki wannan ai halinki ne ya janyo maki, me yasa sai ke kaɗai yake yi wa, ba ga ƙanenki ba da ya kama kansa ya masa ne?"
"Kinga ki yi shiru" ya kai duban sa ga Aisha da take ta murzar idanu da sharɓar majina "idan ya daina za ki yarda ki aure shi" da sauri ta girgiza kai "a'a ni ba na son shi ko ma ya gyara ina da wanda nake so, kuma ma ai ba gyarawa zai yi ba ma bare kuma ba zan taɓa son shi ba"

"Na gama fahimtar ba lallashi za ki ji ba, dan haka ki sani na riga da na gama magana ko bayan ba raina ba ki da miji sai Nasir. Idan har kuma kika kuskura na sake jin labari ko na ganki tare da wancan saurayin tabbas ba za ki ji daɗina ba. Maza bar nan!" Da gudu ta fice ɗakin tana ihun kuka. "Humm dama na sani sai an hau sama da ita an faɗo kafin adaidaita da ita"
  "Barni da ita, in banda shirme waye take tunanin za ta samu nagartacci tsayayyen namiji sama da shi Nasir ɗin, kawai ruɗun sheɗan da na 'yan bana bakwai ke son ruɗarta"
"Humm Allah ya kyauta yasa dai komai ya zo mana yadda muke so dan ina tsoron kafiyar Aisha"
  "Duk kafiyarta ta kaini ne, daidai nake da ita ta gama borinta ta bi yadda muke so. Haɗa mini ruwan wanka"
"To" ta faɗa tana mai tashi tsaye.

Tana fitowa bakin gyat ta samu yana tsaye sanyi yake da kayan motsa jiki yana waya, ganin ta fito yasa ya yanki kiran yana mai ƙyafituta da hannu yi tayi kamar bata gan shi ba za ta wuce "Aisha!" Cak ta tsaya ba tare da ta jiyo ba. "Ba magana nake yi maki ba!" Tana goge hawayen fuskarta ta zo  gaban shi ta tsaya kanta na kallon ƙasa "ina za ki tafi ne?" Haushi ya ƙumeta 'kayan makaranta ne fa ajikina amma dan iya yi har wani tambayata yake'
  "Magana fa nake maki"
"Makaranta zan tafi"
"Ina Ƙasim shi bai shirya ba ne, sannan me yasa za ki tafi a ƙafa ina direban?"
"Ina sauri ne shi yasa, dreba zai tafi tare da Ƙasim" zuba mata idanu yayi "Humm na san wannan sammakon tabbas da abinda kika ƙulla a ranki za ki yi. Wajan wannan saurayin za ki je ko?" Kallonsa tayi da sauri "na faɗama ni ban taɓa zuwa wajansa ba idan ka zargeni da hakan Allah zai mini sakayya"  ta masa maganar cikin gatsalewa mamaki ne ya bayyana a kan fuskarsa har ma ya rasa me zai ce da ita ganin bai da niyar ce mata komai hakan yasa ta bi ta gefensa za ta wuce sai a lokacin ya samu zarafin yi mata magana "ki bari na zo na kai ki" ya faɗa murya a sanyaye"
"Ba na so" tayi maganar tana barin wajan da sauri. Bin bayanta da kallo yayi har ta bi wata kwanar ta ɓacewa ganinsa ahankali ya juya zuwa cikin gidan.

Fargar Jaji Where stories live. Discover now