"Die hard! Why are you shedding tears? Kin san bana son kukanki ko?"

Hawayen ta share cikin wani murya dake nuna farin ciki, mamaki da kuma sallamawa tace
"Hawayen farin ciki ne, lallai na zama mace mafi sa'a a duniya! ni ce annabi ze shaida aurena...."

Kuka ne ya ci karfinta, tace
"ko a haka ka barni kayi min komai a rayuwata paapi, na gode kwarai Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa ya kaimu gobe lafiya! Ina kaunarka sossai da sossai"

Murmushi ya sakar mata, yace
"ana Aidan uhibbuki hubban khasira(I love you more)"

Murmushi suke sakarwa juna na kauna yana ji ina ma akwai aurenshi a kanta da yayi mata rarrashi yadda ya kamata, zata yi magana taga sun iso Airport kuma mutane suna ɗan fitowa hakan yasa ya fiddo face mask ɗinshi ya saka ya fita hannunshi ɗaya cikin aljihu ya zagaye ya buɗe mata ta sauko suka nufi ciki a tare, in ka gansu bazaka taɓa cewa suna da yara a gida ba, sun yi mugun dacewa barin ma da yake fuskan hidayat kaman gonar auduga sbd farin cikin da take ciki a yau...

Ko da suka isa arrivals tsayawa suka yi yana ɗan mata magana, idanunta ne suka sauka kan wata dattijuwa bazaka kirata tsohuwa kai tsaye ba sbd daga shiganta zuwa yadda take tafiya zaka tabbatar da akwai cikakken hutu da natsuwa a tattare da ita, sanye da Atampha riga da zani da hijab ɗinta hannunta rike da sandarta tana tahowa, bayanta masu ɗaukan kaya ne ture da akwatinta, tsantsar kama da taga suna yi da Raed ne yasa ta kalleshi se taga yana yiwa matar murmushi kan ya kalli hidayat yace

"finally! meet Daadida!"

Fuskanta ne ya kara washewa da fara'a da sauri ta taka ta nufi Daadida, tana zuwa kawai ta rungumeta se ta fara hawaye, Daadida na murmushi ta ɗago ta tace
"Hidayat! Yau dae Allah yayi na ga jikata, masha Allah tabarakallah!"

"Sannu da hanya Daadida kin zo lafiya?"
Cewar hidayat ɗin.

Tace
"Alhamdulillah hidayat, sannu kinji tabbas kin cika mun alkawari na, kuma mafarki na ya tabbata, kin zama fitila a gidan Raed Allah ya miki albarka"

Da Ameen ta amsa tana murmushi, yace cikin yanayin shagwaba
"ni kuma fa?"

Dariya suka yi Daadida tace
"kaima Allah yayi maka albarka"
Ya saki murmushi yace
"yanzu na ji zance"

Wucewa suka yi zuwa motar da ta kawo su, aka sanya mata kayan ta a baya, hidayat ce ta buɗe mata kofa ta shiga shi ya shiga gaba hakan yasa hidayat ta koma ɗaya gefen inda ya zauna ɗazu ta zauna, suka bar Airport ɗin.

Kwarai Daadida dattijuwar arziki ce, daga zuwan su gidan zuwa tayi wanka taci abinci ta huta duk kusan suna tare da Hidayat ko wani motsi tayi zata tambaye ta abunda take so, suna yi kuma suna hira cikin hikima Daadida ke wayar mata da kai take kuma nusar da ita menene aure, abunda ba'a mata ba a zaman ta da Yusuf, dukda wasu ta sani sbd islamiyya, wasu kuma ta sani sbd experience ɗinta na aure sede ba duka ba, wannan na nagartacciyar tsohuwa ne me cike da hikima da sanin makamar aure da na rike miji a gargajiyance.

Yaran basu shaku da Daadida sossai ba, dukda haka sun yi mata maraba sun kuma gaida ta tana ta masifar da wanchan pastorn ne baban mamansu da tuni sun cike wurin da hayaniyar ganinshi amma Raed ji yaranshi a gabanta, Norah kam ma tun lokacin rasuwar mahaifiyarsu bata sake ganinta ba se yau don bata zuwa Nigeria.

"Ai ya kamata daga nan Nijeria Zaku yi bari uban naku ya dawo ma"

Dariya kawai Rashida da Hidayat suka yi ashe da gaske take bayan ya dawo ta tabbatar mishi daga nan duka tare zasu tafi da Hidayat akwai abubuwan da take son ayi mata, be Musa ba yace Allah ya kaimu.

Washegari karfe ɗaya na rana a cikin garin madina ya musu, kusan irin hotel da suka zauna a jeddah anan ma haka suka zauna, garin madina gari ne me cike da tarin ni'ima da albarka, jinta take wasai gata ga manzon Allah, har hawaye Seda ta zubar zuciyarta a cike da farin ciki, rashida na taya ta da su Norah.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now