Murmushi me sauti Daadida tayi tace
"Alhamdulillah! Se ka ji tsoron Allah ka kula da ita saboda Allah, hidayat wata haske ce a rayuwarku wadda idan ka bari ta dusashe rayuwarku ma zata dusashe"

Kai ya gyaɗa yace
"Daadida I want you to cook for 200 people ayi sadaka wa almajirai Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

Murmushi me kyau ta saki lallai rayuwar Raed akwai chanji me matukar girma, kalaman da da baya yin su wadda a musulunce suke kaman dole sbd sunna ne yanzu duk yana yi, da da ne sede ayi celebrating a kashewa abokai ayi kida amma yanzu almajirai yake so ya baiwa, da da ne ba ze ɗauki Kalmar tabbatuwar alkhairi da muhimmanci da har ze furta ba don be san menene Adu'ar ya kunsa ba se gashi yanzu ya sani.

Har ze kashe tace
"wani hanzari ba gudu ba! Raed hankalina baze taɓa kwanciya kasancewar ku yanzu a inuwa guda da soyayya babu aure ba, a duk lokacin da Zaku keɓe sheɗan ne ze zama na ukun ku, kaman yadda Allah ya faɗa a cikin Alqur'ani me girma, shi kuma bashi da wani buri illa na ya haddasa fitina a ban ƙasa, don haka zan shawarceka da ka natsu ka yanke hukuncin da zata ficceku tun kafin sheɗan yayi nasarar ratsa tunaninku don daga sannan kuma wannan soyayya zata samu cikas, rayuwar aurenku baze taɓa yin albarka ba don an kashe albarkar daga waje"

"zan yi tunanin hanya mafi bullewa kan in koma Daadida bana son abunda ze kawo mana rashin albarkar aure kaman yadda kika faɗa, in shaa Allah I will call back in faɗa miki hukuncin da na zartar"

Murmushi ta saki tace
"Allah ya maka albarka"

Ya amsa da Ameen kan ya kashe wayan, kuɗi masu yawa ya tura mata na sadakar da yake so ayi, kan yayi call akan a tura mishi numbern Farik Naik ze mishi tambaya..

Cikin mintuna talatin ya samu personal line ɗinshi sbd connections ya kira shi, bayan sun gaisa ya sanar dashi waye shi suka sake Gaisawa kan yayi mishi tambayar da yake so yayi mishi, gamsashiyar Amsa ya bashi wadda Alqur'ani da hadisi suka zo dashi, yayi mishi godiya suka yi sallama..

Hidayat ya sake kira, Aisha ce ta ɗaga suka fara mishi hayaniya, Seda duk ya gama jinsu wai next week zasu yi hutu, they want a holiday outside Paris.

"Where is ur mom?"
Ya tambayi Farrah, se ta fara kwala kiran hidayat

"mom! Mom dad want to talk to you"

Fitowa hidayat tayi tana sakin murmushi ta karɓi wayan tare da sallama... Seda ya lumshe idanu kan ya amsa yace
"Die hard when are you finishing ur exams?"

Tace
"Amm ina Tunanin in 8dys time"

Yace
"ok, I will be bit busy to then don zamu yi final muma in 10dys....!"

Tace
"kaiii...! U mean zaka fi week kan ka dawo?"
Ita kanta bata san sadda tayi maganan murya a karye ba.

Murmushi yayi me sauti yace
"someone is already missing me ko?"

Murmushi kawai tayi, yace
"I want us to go for a trip after ur examination"

Cikin zumuɗi tace
"where?"

Yace
"it will be surprise, ke de kiyi mana Adu'ar sa'a a wasanninmu masu zuwa don sun ɗauko zafi"

Tace cikin murmushi
"I trust you in shaa Allah ku Zaku yi nasara! Allah ya bada sa'a ku ɗauko mana UcL cup"

Sossai yaji daaɗin Adu'ar ya amsa suka yi sallama.

Daadida ya sake kira ya gaya mata hukuncin da ya tsayar taji daaɗi sossai tayi mishi Adu'ar nasara itama, ta so ta kawo mishi zancen Mahaifinshi sede bata so ta ɓata mishi mood na farin ciki da yake ciki, kudin da ya turo rabi ta kira Badi'ah ta tura musu akan a koma asibiti sbd ita yanzu bazata iya tafiya daga Kano zuwa gembu da mota ba, ko daga cikin jalingo zuwa gembu tafiya ne me nisa sossai dole se da jirgi kuma babu jirgin da ze iya kaita gembu in ba helicopter ko private jet ba.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now