Tace
"wa ya gaya miki saka kunne a zancen wani abu me kyau ne? It's not a good habit kin ji? Don't do that again.. Oya let's go ki ci abinci"

Hannun da ya ɗaura kan handle ɗin ya janye jin ta fuske magana na biyu da yarinyar tayi, Juyawa kawai yayi ya wuce room nashi yana ji Farrah na sake tambayar ta zata iya kiranta mom sbd mama is not for her yayi local, maganan ya so bashi dariya sede baya cikin mood ɗin yi ɗin har ya shige be kula su Norah da suke shiga zancen nasu ba don already sun fito parlor.

Kasan shower ya shiga tare da dafe glass ɗin da ya zagaye standing shower ɗin ya lumshe idanunshi ruwan na zuba daga kanshi zuwa jikinshi, hidayat na so ta hura mishi wuta, he never expected what she did.. Ya jima sossai a haka kan yayi wanka ya fito, a gaban madubin toilet ɗin ya tsaya ya riƙe kwankwaso yana kallon kirar jikinshi da kyaun surarshi.

Lallai Hidayat daban ce a cikin mata, baya tunanin a kab kasashen da suke duniya akwai inda ze shiga be samu masu sonshi ba, ba ɗaya ba ba biyu ba, ko da macen bata kallon ball ta kan yi social media kuma baza'a rasa shi a kullum a yanar gizo ba Dukda shi ba ma'abocin yin bane sede ayi ta buɗe accounts da handle ɗinshi, wadda yake dashi ma sakuna suna mishi yawa don se ya samu thousands of dms a kowanni flat form da yake, but to his biggest surprise hidayat turns him down.

A kasalance ya shirya yayi sallahn magrib da isha tare da kwanciya don ko fita be sake sha'awar yi ba, ko da junior ma ya tashi daga baccin nashi a nan ɗakin ya bashi madara ya sha sossai yayi mishi wanka ya sa mishi pjmas don duk yaran basa rasa kaya a ɗakin shi, anan suka sake komawa kwanciya.

Yadda yaga rana haka yaga dare yana ta juye juye cikin damuwar da Hidayat ta haddasa mishi, kaman yadda be yi bacci ba haka itama bata runtsa ba, sossai take jin ba daaɗi sede bata so tayi gaggawa wa rayuwarta Sam, chance ɗin yanzu ne kaman yadda ya faɗa kuma a duk iya Tunaninta da hangenta auren hamza shine babban kalubale da zata so fuskanta a yanzu sbd matsalolin family ɗinshi yayinda auren Raed kaman wani kofa ne na dawamammiyar natsuwa da kwanciyar hankali don ko ba komai shi kamilalle ne, yaranshi suna sonta haka ma kakarshi na son ta, sede ko ta ina in ta duba Sanannen mutum irin Raed yafi karfinta a ko wani ɓangare ita ba tsaranshi bace, da taga Tunanin babu inda ze kaita se ta mike ta gabatar da alwala ta zo ta hau nafilfili daga karshe tayi istikhara tana me neman zaɓin Allah..

****

Yau aka sallami Abba daga asibiti sbd komai ya dawo normal tafiya ce dae kam har yanzu se a hankali, a parlor suka yada zango gabaɗaya sbd mutanenshi da suke zuwa akai akai ana taya shi murnar samun cikakken lafiya.

Kowa ya shigo zaka san ba karamin mutum bane don harda minista me ci a yanzu da su comissiononi, en majalisu duk dae wadda yake a tare da Abba a da sbd Abban mutum ne me jama'an gaske, hidima ya hana hamza natsuwar duba waya Seda bayan isha suna zaune a babban parlorn da hajiya da Zainab su biyu suke hiran su don Abba ya bace a duniyar tunani yayinda hamza ya fiddo Wayanshi ya fara dubawa.

A Twitter ya fara cin karo da abunda ya kusa zauta shi, clear picture me tsananin kyau da ɗaukar hankali har ze wuce sbd be sheda macen ba se kuma sunan Footballer Raed ya ja hankalinshi ya sake komawa don dubawa.

"Breaking: the girl with the greatest footballer MOH RAED in the last pictures that go viral wasn't actually his wife she's his girlfriend as he is proposing in a best romantic way ever #Sunset at Seine River❤️"

Be taɓa zagin kanshi ba se yau, yayi Adu'a wani ya fito ya shedawa duniya cewa ba matarshi bace sede gashi a lokacin da Adu'ar shin ta karɓu se ta zama wani kifiya da ya zo ya cake shi a zuciya ya hana gudanar numfashin shi, a take wani mummunan tari ya sarƙe shi kuma ya kasa dena kallon background ɗin don ko a hoto zaka san ba karamin ƙawatuwa wurin yayi ba gata ta fito kaman international celebrity gashi yayi wani tsuguno a gabanta dukkanninsu kuma idanunsu na bisa camera.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now