Red dress ta ciro mata, doguwar riga ce kaman me zuwa promp night haka dress ɗin ya amshe ta Dukda ba ta inda jikinta ya bayyana banda tsagu dake bariyin kafan ta na dama shima se idan ta buɗe kafar sossai ne ake iya kallon skin ɗinta daga cikin net ɗin rigar shima be kai rabin sharaɓarta ba.

coler neck ne kaɗan ne kawai a buɗe se ta saka mata sarkar ta da ta zo dashi da wasu designers ɗan kunne da kyaun su kaɗai ya ishi bayyana tsadarsu suna dauke da back stones daga tsakiya, kanta se ta saka mata cikin wani silk black ɗan kwali da ya zauna sossai a kan nata se black shoes masu Tsai, harda wani black purse, duk wadda ze kalli hidayat a lokacin ze ɗauka irin international celebrity ɗin nan ce saboda kyaun da tayi.

Ita kanta se kallon kanta take a lokacin da aka gama shirin, matar ta feshe ta da turaruka masu sanyin kamshi.

Ta lura matar se duba time take, bata dae ce mata komai ba ta samu wuri ta zauna, se dab karfe biyar da rabi kan tace mata zasu iya fita.

Mikewa tayi da bismillah sbd takalman kafan ta, ji take kaman zasu yarda ita sbd tsinin su hakan ya sauya mata salon tafiya kaman me tafiyar tarwaɗa, sake idanunta tayi tana kwasar kallo sbd yadda saman ya juya mata daga yadda ta shiga ta bari, wow masha Allah, abunda ta furta kenan tana kallon jajayen furrani masu fitanannun kamshi da aka kawata jirgin dashi an yi organizing table da ɗazu ta zauna babu komai kai da wasu varieties na abinci harda cupcakes masu candle iska na ɗan kadawa kaman ze mutu kaman kuma baze mutu ba.

Abunda yafi ɗauke mata hankali kuma shine rana da yake ta kokarin faɗuwa yayi wani haske me kyaun gani bata taɓa sanin haka sunset yake ba, ta shagala da kallon sunset ɗin taji wani ƙara kaman na flying boat yana zuwa daga nesa, a hankali ta sauke idanunta saitin inda take jin ƙaran zuciyarta ne yayi wani kalar tsalle.

The view of him a tsaye ba riga se wata three quarter black yana riding flying boat ɗin cike da tsantsar kwarewa gashi ya fito ta ɓangaren da hasken ranar ke shirin faɗuwa se ya bada wani kalar kyau da ɗaukar hankali, lumshe idanu tayi ta sake buɗewa tabbas shine builded body ɗinshi se wani haske yake, bata san ta ɗan yi gasping ba ta kuma kasa ɗauke idanunta a kanshi har ya iso jikin jirgin da take yayi tsalle ya haye tare da Juyawa ya ja flying boat ɗin ya sa a mazauninshi na cikin babban jirgin.

Se ya juyo suka Haɗa idanu daga inda take tsaye, lumshe nashi yayi ya sake buɗewa she looks so breathtaking to him, kaman kawatacciyar flower dake samun ban ruwa ta fitar da Fure me tsananin kyau da ɗaukar hankali haka ta zama, ji yake kaman ya hadiye ta ko ze huta da bugawar da jijiyoyinshi suke da sunanta.

Cikin tafiyarshi ta xaratan maza yake tunakaro ta hakan yasa tayi kokarin fusgan idanunta daga cikin kwayar nashi se kuma ta saukar a inda ya kusa sumar da ita, don sun sauka ne bisa shafaffen cikinshi wandon shi ya ɗan sauka har kana iya hango v line ɗinshi cikin azama ta sake daukewa se ta rasa takamammen mazaunin da idanunta suke sha'awar kallo bayan shi ɗin.

Wani ash cotton shirt da ya sa aka ajiye mishi a linke a wurin ya ɗauka ya sa kan ya karaso gabanta ya tsaya ya sakar mata shanyayyun idanunshin nan yana yaba kyaun halittar Allah a wurin, ganin ta kasa Kallonshi se kafafunshi da suke kyalli sanadiyar ruwan da ya taɓa su gasu bearfooted take ta kallo yasa yayi anfani da wata kalar murya yace

"diehard!"
Wani irin amsawa kirjinta yayi, tsikar jikinta suka bada wani yaammmmm she started to get confuse bata ɗago ba seda taji ya sake maimaita

"die hard!"
Did he mean da ita yake?

Cikin tsoro ta ɗaga manyan Fararen idanunta da suka ji liner ta zube bisa kanshi seda ya so yayi loosing balance ɗinshi, ya lumshe idanu ya sake budesu a kanta ze yi magana se wani cool music ya fara tashi a cikin jirgin inda ya haɗu da yadda suke ɗin ya tafi da bugun zuciyarsu ya bada wani romantic scene.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now