Shiru yayi, tace
"kaji? Please"
Yace
"Toh naji na amince, yanzu dae bar maganan zainab ya namu maganan?"

"Yadda kace in Shaa Allah"

"Toh na ce daga Abba ya samu sauki saboda 100% goyon bayanshi na tare damu, yana karasa warkewa in Sha Allah zaki zama matata"

Murmushi ta saki tace
"yanzu am engaged kenan?"

Yace"
Morethan that ma, ni a wurina kin riga kin zama tawa"

Dariya ta ɗan yi tana kallon Farrah da ta tashi da gudu ta fice kaman wacce aka kore ta tace
"Ohk ka gaida Abba"

Yace
"in shaa Allah! Thanks take care"
Ta sauke wayan tana me kishingiɗa da pillow, hannunta ɗaure bisa kan shafaffen cikinta da bazaka taɓa cewa ƴaƴa har uku sun zauna ciki ba, hamza is something else ta rasa menene ke hana shi kwantar da hankalinshi in har dae abu da ya shafe ta ne, ba wai tana da niyyar yaudaranshi ko wani abu ba sede tana jiye mishi idan Allah be qaddareta a matsayin matarshi ba!

Kwarai zata iya aurenshi ta zauna dashi da iyalan shi lafiya ta auri Yusuf ta zauna da Yusuf ma na kusan shekara goma da daaɗi ba daaɗi bare hamza da yake matukar son ta?.

Da gudu ta shigo ɗakin bata damu da zaune yake yana aiki a system hannunshi ɗaya rike da waya yana call jingine da pillows ba ta haye gadon tare da jan hannunshi dake rike da system ɗin tace
"Daddy! Daddy! Miss hidayat wants to leave us"

Da sauri ya kalleta yace
"what??"

Yarinya kam se hawaye sharrrr, katse wayan yayi tare da sauke system ɗin ya kamo hannunta
"Farrah explain why did you said she wants to leave us?"

"Dad this guy we called Daddy hamza he want to take her away from us! She's promising to marry him ahhh I can't believe this"
Ta karashe da zabga tagumi tana cigaba da hawayenta.

Kallonta kawai yake ganin kaman be ɗauki maganan serious ba Dukda a nashi ɓangaren he's in Morethan shock yasa tace
"Daddy this is a big problem, he wants to take her away from us!"

Cikin wani yanayi yace
"Ohk baby! U know what am gonna do? I will talk to her not to leave us ok?"

System ɗin ta rufe tare da matsarwa ta fara jan hannunshi
"dadd come with me and talk to her..."

Da kyar ya samu ya lallaɓa ta ta kwanta anan bacci ya ɗauke ta, se ya mike ya fara safa da marwa a cikin ɗakin, be taɓa jin fargaba da tsoro irin wannan ba har rawa rawa zuciyarshi yake yi, a hankali ya kai hannunshi aljihun wandon jikinshi ya fiddo wani gidan zobe me tsananin kyau black, da babban yatsanshi yayi anfani ya buɗe wani diamond ring hadadde ya bayyana se kyalli yake, shafa kai yayi ya sake rufewa.

Wannan dare haka ya kwana be iya runtsawa ba cikin Tunanin mafita, daga karshe kuma ya tsayar da mafita guda ɗaya.. Idan har be yi working out ba yana da Plan B baya Tunanin kuma ze faɗi.. gab asuba kuma aka kira su akwai wani training haka ya fice da wuri.

Ko da ta shirya su suka tafi school ita yau ma bata je ba, kasancewar revision suke yi suna gab da fara exams, bayan ta gama ayyukan ta karatu ta zauna tayi ta dubawa daga karshe ta sake gwada layin Ummi kaman yadda kullum take yi sede bata same ta ba.

Abincin rana ta ɗaura musu bayan ta sauke tana fitowa parlor taji Paul na magana, da sauri ta juya wurin kofa yake ce mata oga ya ce ta shirya ta zo ze kaita wani wuri.

Tambayar yaran tayi yace lafiyansu ƙalau suna school, ɗaki ta shiga bata tsorata ba sbd ta san dae baze taɓa cutar da ita ba, don haka a natse ta shirya cikin wani riga da skirt na material me taushi da tsada wadda a dinke yazo, hannun dogo ne sede yana da tsagu zuwa gwiwan hannu, kayan ya zauna mata sossai, ta ɗaura dankwalin sossai ya haske fuskanta kasancewar kayan ruwan powder ne.

Milk veil ta yafa da milk shoe se handbag shima milk bayan ta saka fashion dan kunne milk, se ta saka sarkar da ya saya mata jiya, fuskanta ba komai banda kwalli da pink lip balm me haske.

A natse ta sauko tana duba agogon da ta ɗaura na Apple watch me gold hand, yaran suna da ɗan sauran lokaci kan su tashi don haka bata damu ba ta fito, Paul da kanshi ya buɗe mata bayan katuwar farar GLK ɗin ta shiga ya rufe tare da zagawa ya tayar suka bar kofan gidan...

****

"Wai Alhj me nayi maka ne? Bayan Duka shekarun nan da ka kwashe a kwance ina fama da wahalar ka in ci kashinka in ci fitsarin ka da abunda zaka saka min kenan bayan farkawarka? Ai ko me nayi maka ban cancanci haka daga gareka ba Alhj bare ma babu abunda nayi maka"
Ta karashe cikin masifa, idanu ya zuba mata yana kallo, chan yace..

"Kika ce babu abunda fa kika min? Toh ba dole kiyi ba tunda ke kika zaɓarwa kanki? Ko kin manta kece sanadiyar wannan ciwon nawa?"

Wara idanu tayi tace
"Wallahi ba de ni ba, kaima ka san sanadiyar ciwonka ba ni ba kam karka ɗaura min... Ah to"
Tana kai nan ta juya fuuu ta fice, da kallo ya bita, Hajiya bazata taɓa chanzawa ba a duniyan nan, Allah ya bashi lafiya shine rokon shi don yana da babban Burin da yake son cimma a duk ranar da cikakken lafiya ta same shi, lumshe idanunshi yayi yana ambaton Allah..

#Vote
#share
#comment


                   🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now