Idanunshi gabaɗaya ya sakar yana me kallonta a lokaci ɗaya zuciyarshi na wani irin harɓawa, sanye take da peach tummy trouser me faɗi se blouse white shirt me dogon hannu wadda yake da tattara daga karshe hannayen, peach gyale ta yane kanta dashi se hill peach dake kafafunta da handbag white, a yadda take saurin se tayi mugu mugun tafiya da duk wani imaninshi, idanunta masu haske da suka haɗu da hasken rana se suka bada wani sparkle me kyau, lips ɗinta ya ɗan kurawa idanu banda shining babu abunda suke, ɗauke kai yayi yana jan iska tare da hurowa se ya lumshe idanunshi daidai sadda ta shiga motan kamshin ta ya dake shi, komai nata me sanyi da fusgan hankali ne.

Tafiyar ta, maganar ta, adonta, kai komai da ya dangance ta abu ne unique da be taɓa gani daga wurin kowa ba se ita, gaishe shi tayi hakan yasa ya ɗan buɗe idanu ya kalleta kan ya amsa cikin kulawa.

Har suka isa Airport yanayin shi be daidaita ba, ko a cikin jirgin ma lokaci lokaci su kan kama juna suna Satan kallon juna, ko da suka isa resorts me tsananin tsada aka musu masauki a harabar wurin kuwa suka haɗu da sauran en wasan na kwallon kafa wadda kowa ya ɗauka ita ɗin matarsa ce, wayancewa tayi wadda hakan ya burgeshi matuka suna gaisuwa cikin mutunci da colleges ɗin nashi da matansu, rashin hayaniyar ta ke bayyana kamewarta wadda komai sa idonka bazaka taɓa gane cewa ita bakuwar irin rayuwar ne.

Se yaji wani girma ya ƙaru mishi musamman da wasu ke tsokanarshi da dole ya dinga ɓoye matarshi yake hana kowa ganinta ashe ya san abunda ya ajiye, wasu kuwa yaran ke ɗauke hankalinsu barin ma junior da yake so energetic.

A gajiye suka kwanta, shi kam dayake ba wuri ɗaya suke ba Bama su san sadda ya kwanta ba.

Washegari da safe a tare dasu ya zo ya karya ya sake ficewa bayan ya tabbatar babu abunda zasu nema.

Da yamma suka fito a shirye tsab zuwa stadium ɗin da zasu yi wasan, ita ball ba abun kallonta bane sede ta wuce ana kallo amma yau se ta tsinci kanta da zumuɗin kallon wasan, tunda ta san yana ciki.

"King Boudouin Stadium" shine rubuce daga saman hadadden stadium ɗin, mutane ke ta shiga ta ko ina saboda zazzafar wasa ce barin ma an san PSG ne zasu buga, wadda ya kawo su ne yayi leading ɗinsu har kujerun da Raed yayi mishi umarni wadda suna daga gaba gaba.

Suna nan zaune ba'a yi mintuna ashirin ba se ga en wasan sun fara shigowa da joggings suna shaking hands da yaran da suke jere suna musu maraba, Seda suka daidai ta a filin kan aka fara gudanar da wasan da yayi mugun tafiya da ita.

A nan ta sake take mishi kallon da bata taɓa yiwa wani ɗa namiji ba, duk inda ze yi idanunta na manne dashi wani lokacin in an mishi mugunta ita se ta fishi jin zafin, yaran se surutu suke wadda Junior dake hannun su shi kuwa se son sulmuyewa yake ya sauka tsabar kiriniya, gaskiya ko! me kallon ball se me cikakken natsuwa in ba haka ba jininka a take se ya hau saboda suspense.

Wasan yayi bala'in zafin da duka clubs ɗin kowanne gwanaye ne, hakan ya sa aka ja lokaci sede attempts amma babu maganan ci, Ana gab da tafiya hutun rabin lokaci Allah ya ba Raed sa'a ya cilla kwallo a raga zo kaji ihun mutane, har Hidayat seda ta mike don murna tana tafa hannaye, shi kuwa sujada yayi yayinda sauran en team ɗinsu suka zo da gudu suka rungume shi.

Ba'a cigaba da wasan ba aka tafi hutun rabin lokaci inda suka koma gefe suka haɗe kai ana shawara, ko da suka dawo daga hutun chanza salo kowanni club suka yi, dayake in an dawo ana chanza raga hakan yasa yanzu nasu Raed ɗin ke kusa kusa da inda suke, Ko da suka fara wasan lokaci lokaci ya kan kalleta ita kuwa bata sanin tana sakar mishi murmushi, shima se ya mayar mata Dukda tazarar dake tsakaninsu.

Ana cikin wasa Raed ya ɗauki ball kenan yana cikin gudu seda ya shiga 18 kan ɗan ɗaya team ɗin ya zo da niyyar kwace ball ɗin inda da gangan ya sa kafafun Raed tsakankanin nashi ya murɗe, ƙara ya saki yana faɗuwa ringine a take referee ya hura wristle, don ba irin ciwon tashi lokaci guda bane daga yadda ya sa hannayenshi ya rufe fuskanshi hakwaranshi a haɗe zaka san yaji zafi sossai.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now