Yace yana harzukowa
"eh ai gwara ni da degree na ke fa? A sadda ake neman kiyi karatun ƙi kiyayi kika ce aure gashi yanzu uwar miji ta sakoki ba Chas ba ass se tallar doya"

"ahayyeee ai gwara ni ban zama malohuwa sokuwa ba, mace nake kuma ina amsa sunana wasu mazan da suka koma mata fa? Kai da kayi degreen da me ya anfana maka? Gaka nan marabinka da mahaukaci bin bola...!"
Ta kare tana buga kafa kasa cike da masifa, tsabar rama da talauci kana iya ganin ƙura na tashi in tayi wani jijjigan

"ni fa kun ishe ni Haba!"
Surayya dake fitowa daga fallen ɗakin dake gidan bayan wani me ciki da parlor ta faɗa tana saɓan mayafinta a kan igiya.. Tayi gaba

"yawon shashancin da aka saba, tsabar lalacewa ma wai a wurin masu shayi da layin ga ruwa ake ƙarewa"
Cewar Kausar again.

Surayya da har ta fita ta dawo tace
"ai gwara ni ina da abunda zan bayar ɗin in wata ta isa tayi mana..."

Harzukowa Kausar tayi sede tuni Surayya ta fice, Zasu cigaba daga inda suka tsaya da Yusuf umma ta fito sanye da wasu riga da zani da suka ji jiki ta kare kaman ba umma ba, zata yi magana wata sangamemiyar mata ta fito daga daki me ciki da parlorn tace

"kai ya isheka hakanan! Ina cefenen da na ce karka dawo gidan nan babu shi?"

Sosa kai yayi cikin wani irin ladabi yace
"Wallahi wallahi ba aiki yau dako nayi kuma shima ɗari ɗaya kawai na samo"

"kawo ka wuce ka koma...marar zuciya sususu"
Zuwa yayi ya miƙa mata ya juya ya fice.

Kallon tsakar gidan tayi tana kallon umma tace
"ya aka yi kwata kwata wurin ba'a kimtse ba?"

Umma tayi saurin cewa
"eh..eh dama yanzu ne za'a kimtsa..."

Fara tattare gidan tayi tana kallo Kausar ta gama Haɗa doyarta ta fita ko yanka ɗaya bata bar mata ba gashi tun safe babu abunda ya shiga cikinta.

Tunanin rayuwa ta faɗa..
Ashe haka hidayat ke ji a sadda suke azabtar da rayuwarta? Wani irin sakayyah ce wannan me muni? Tun bayan da ƙasa ya rufe idanun Abba ibtila'i yake sauko musu abu na karshe da tayi nadama shine korar kare da tayiwa hidayat da ɗanyen jariri.

Yadda hidayat ta sa kafa ta tsallake kaman ta tafi ne da duk wani sauran rayuwar da suke lallaɓawan, garin wawancin yusuf ya zube dukiyar su duka hannun rikakkun ƴan 419
Sun sayar da Motoci har biyu wurin bin polisawa ko za'a samu clue dukiyar su ta dawo sede a banza.

Bayan tafiyan hidayat Yusuf ya haɗu da wata mata, tunda ta ganshi taji shi take so kuskuren shi daya shine zina da ya fara da ita wadda shine makasudin rayuwar da suke ciki yanzu, saboda ana rade raden cewa muddin  ka kusanceta to zata mallake ka ne da abunda ke kewaye da kai har se in ita ta tafi da kanta amma baka isa guje mata ba.

A yadda yake a hauka hauka saboda kasa sukuni da mafarke mafarken Usman cikin mugun yanayi ta saka shi aurenta, ita ke tura shi ya sato abubuwa masu muhimmanci da su umma suna sayarwa kan umma ta farka wayam, kayan sawa ma be bari ba, karatun Surayya ya tsaya Chak hafiz ya ɓata ɓat kaman walkiya.

Har ta kai ta kawo gidan Abban ya fi karfinsu saboda suna zaune ne kaman a kango tunda gashi a cikin babban gida sede ba abinci, dalilin sayarwan kenan suka dawo suka saya wannan me saukin kuɗi a cikin irin wannan anguwa da da ko wucewa babu ɗayansu da ze iya yi.

Kausar ta gamu da sharrin uwar miji sanadiyar kaninshi da tayiwa ƙage akan ya neme ta wadda kashe ɗan uwanshi ne kawai mijintan be yi ba, daga nan uwar mijin ta sa mata karan zuƙa wata biyar tana gana mata kalolin matsaloli har asirin ta ya tonu kawai tana jin haushin cin arzikin ɗan uwanshi da yake yi ne, nan suka mata jina jina tayi tilis kan suka korota daga ita se kayan jikinta.

Daga karshe taje ta kwashe kayan ta sede a hankali suma aka sayar da komai chanjin ne har yanzu take Juyawa shima da tsiya tsiya.

Fahariyya kuwa mijinta aure yayi ya auro wacce ta maida ta bola, tana zaune ne kawai saboda tsoron irin rayuwar da ake a gidansu amma kwarai tana azabtuwa yadda ya kamata!

Matar Yusuf ba ginin da za'a taka a hau bace hakan yasa komai na gidan su suke yi, sau daya Kausar ta gwada Haɗa  ƙashi da ita Seda aka mata ɗauri, har yusuf ɗin in ta ganshi yana kallon wata haka zata saka shi a gaba ta zane tsab! Har Seda ya fara dana sanin zina a rayuwar shi.

Gabaɗaya rayuwarsu ta taɓarɓare wadda a shekarun baya ko a mafarki basu taɓa Tunanin kasancewa cikin irin wannan rayuwa ba.

(Ni ko nace ai wadda ya ƙi Sharan masallaci dole ze yi na kasuwa!)

PARIS

Zaune take riƙe da waya a kunne
"Daadida! Don Allah ki kwantar da hankalinki a bi komai a sannu, a gaskiya taɓon da Baba bukar yayiwa rayuwar yallaɓai me matukar girma ne wadda bana Tunanin ze gogu sede watakila idan addininshi yayi zurfi zuciyar musulunci tasa ya iya gyara alakarshi da Mahaifinshi, karki manta ba iyaye bane kaɗai ke da hakki a kan yara, ƴaƴa ma suna da hakki a kan iyaye.. Mu yi ta Adu'a Allah ya dubi lamarin se kiga komai ya zo ya wuce"

Daadida ta share hawayen fuskanta tace
"bana so in mutu in bar su haka Hidayat, kullum ƙara tsufa nake rayuwar bukar ta riga ta gama taɓarɓarewa saboda abunda ni na san hakki ne...! Ciki harda laifi mafi girma shine na saɓawa iyaye, A hakan ma kullum ina rokar mishi gafara sede Allah babu ruwanshi abunda kayi shi za'a maka... Jiya ya bar nan cikin tashin hankali saboda wani mummunar faɗa da Badi'ah da Zara suka yi wadda yayi sanadiyar jefa ƴaƴan su rijiya, ya ce kullum gidanshi kaman gidan kaji ko na ƴan dambe, ko allura ya ajiye za'a nema a rasa saboda sata gashi har yau bayan Raed be da wani ɗa namiji... Yara mata ne cikinsu babu abunda babu, har da ƴar daba wacce yace tayi ikirarin yanka wuyanshi ya sake ɗaga mata murya gidanshi kuma dole ta shiga... Hidayat abunda ya ɗaure min kai har yanzu be yarda hakki ne ke binshi ba ya kasa neman yafiyata ya nemi albarka... Ya kasa neman ɗan shi ya nemi ɗauki wani irin azabtar da kai ne wannan?"

Hawaye hidayat ta share tace
"Ki cigaba da Adu'a da sadaka Daadida in shaa Allah komai ze yi sauƙi... Watakila Allah ne ya ɓatar dashi ya kuma mantar dashi Tunanin da ya kamata yayi wurin gyaran kuskuren shi saboda ya girbi abunda ya shuka, muyi fata Allah ya tsayar dashi iya haka"

Dukda hidayat bata taɓa ganin Daadida ba sede akwai wani shakuwa da ya shiga tsakaninsu ta waya, saboda matsaloli Raed Dukda har yanzu ba shiga harkar ta yake kaman da farko ba, iyakar su karatu wadda yana gamawa ze fice,  ya fi maida hankalinshi kan sana'arshi yana kuma azabtar da kanshi da motsa jiki a ko wani lokaci.

Sallama suka yi da Daadida tana sauke wayan hamza na kira.
Ɗagawa tayi yace
"Hidayat da wa kike waya tun ɗazu layinki busy?"

"Da grandmother ɗin boss ɗina muna tattauna wani batu ne da ya shafe shi..!"
Ta faɗa kanta tsaye da iyakar gaskiyar ta.

A zafafe yace
"kina so ki kashe ni ne hidayat? Wallahi hangen kwanana nake kusa...! Rayuwata na shirin taɓarɓarewa na kiraki ko zan samu sanyi ta wurinki shine kike gayamin maganan wani boss?"

Dafe goshinta tayi tace
"ya ilahi! Ya Hamza wani furuci nayi da ze harzukaka haka? Tambaya ta kayi na kuma baka amsa.. Me ke faruwa ne?"

Runtse idanunshi yayi yace
"Hidayat hajiya ta ƙi tsayawa ta saurareni zainab ta rigani a wurinta, a sanina yadda hajiya ke so na a matsayin tilon ɗan ta komai nake so yi min take amma yanzu tana shirin juyamin baya"

"ya hamza ka san me ya fara burgeni da kai?" Ba tare da ta jira amsar shi ba ta cigaba.
"Kaifin basirarka da natsuwarka amma yanzu duk kana nema ka rasa, ni ba gudu zan yi ba ina nan ka bi komai a sannu har mu samu albarkarta kaji don Allah?"

"Hidayat companies ɗin Abba na na rawa wadda sanadiyar abubuwan dake faruwa dasu na bar aikin soja na dawo don in kula dasu amma na kasa focusing don Allah in zo a ɗaura mana aure daga baya se mu nemi yafiyar hajiyar ko zan samu in mai da hankalina kan abu guda.."

Kasake hidayat tayi, Wai me ke faruwa ne?.ta tambayi kanta.. Wani irin possession ne wannan?

(Nima nace ku tayani gani)

**Don Allah wa ya san wani magani na ciwon kunne? Wallahi nayi yawon Asibiti na gaji**

#like
#share
#comment

                  🖤Gureenjo🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now