"Eh kwarai na gane, wacce ka ce tana zaune ne wurin marikinta kuma bata jin daaɗin rayuwar gidan, daga karshe kuma aka aura mata ɗan gidan ko?"
Ta faɗa tana mishi wani kallo.

Yace
"eh hajiya!"

Cikin tsananin masifa ta fara magana
"ban gane eh ba? Kana nufin ita zaka sake tura mahaifanka a tozarta su kaman yadda aka yi a baya? Marar tushe da asalin? Wacce dama tun a wanchan lokacin karfin ikon me mazari ne(kakanshi na wurin uba) yasa na zuba muku ido, Ko kana so ka ce zainab bata wadace ka as mace ba da har bata shekara ba kake maganan yayibo wani aure?"

"Hajiya uban goyon ta ya rasu, bata da kowa se Allah don Allah karki hanani aurenta"
Ya faɗa cikin roƙo.

"Dakata ma tukuna! Yanzu a Paris ɗin wurin wa take zaune?"

"Hajiya tana aiki ne na kula da yara waenda suka rasa mahaifiyarsu shine baban ya ɗauke ta aiki kuma tana karatu" ya faɗa da iyakar gaskiyar shi.

Wata doguwar salati hajiya ta ja ta sallame nan fa ta fara balbale shi da masifa akan wallahi ba'a zuri'ar ta ba, ƴar bariki dake zaman kanta Inaaa..
Duk yadda ya so ya fahimtar da ita ta kasa fahimta, Hajiya irin manyan matan nan ne en duniya waenda duniya kuma tayiwa daaɗi, bata da mutunci ko na sule biyar bata san wani abu wai shi kawaici ko kunya ba, bata da kirki in ka taɓa ta kaman yadda girman kai da izzarta ba ze bari ta rabi kowa ba barin ma idan talaka ne, shi kuwa yana jin ba ze iya rayuwa babu hidayat ba.

Daga karshe korarshi tayi, ɗakin Abban shi ya nufa ya same shi kwance jiya e yau, rufe yake da blanket fari, hancinshi abun oxygen ne ba uhm ba um um kuma yayi shekaru da dama a haka, idan jikin yayi tsanani se an saka mishi oxygen da abun abinci ta baki amma idan da sauƙi ya kan yi numfashi.

Hannunshi hamza ya riƙe ya ɗaura fuskanshi a kai se hawaye, yana son hidayat son da be sani ba seda hajiya ta fara nuna mishi turjiya akan aurenta, kaman fa baze iya rayuwa ba tare da Hidayat ba, kwarai in hajiya ta raba shi da ita kwananshi kirgaggu ne a duniya.

****

Tafiya yake kaman sabon kamun hauka wurjanjan, riga daban wando daban na yaɗi kodadde wadda ake kira wanke kuɗin ka, kayan da da in ya gani jikin Usman yake kyarar shi saboda kyamkyami se gashi yau na Usman ma yafi nashi kyaun tsabta da sabunta.

Daga kafaɗun a yayyage yayi baƙi gabaɗaya ya koɗe kaman ba Yusuf ɗan kwalisa ba, buhun karshe na dako da yake yanzu ya kai ya karɓi Naira ɗari ɗaya da aka bashi yana juyata..

Me ɗari zata mishi? Ba Wa shi kaɗai ba harda familyn shi da suke gida suke jiran ya kawo? Ba ga matarshi da yake ji kaman ya mata sujada ba, ba ga mahaifiyar shi da ƙannenshi ba.

Hanyar gidan ya kamo a rikicenshi in ya ga yaro tsaran Usman se ya ruga da gudu ya kama shi
"Usman! Usman!! Baka mutu ba ko? Yauwa zo muje gida ba zan kara dukan mamanka ba don Allah ka barni in sarara"

Wani lokacin idan abun ya Motso se an yi da gaske ake kwace yaro a hannunshi se yace Sam Usman ne ze kaiwa Hidayat shi saboda ya dena zuwar mishi a mafarki da zahiri.

Gida ne na laka cikin wata kwaraɓaɓɓiyar unguwa da kwata shine abu mafi rinjaye da yayiwa anguwan ƙawanya, kudaje kuma suka zama ma'abotan huldarsu, kutsa kai yayi ba tare da ya damu da yayi sallama ba.

Zaune yaga Kausar wacce itama ta zama wata jagwal, tana Haɗa abubuwan da take anfani dashi wurin toya doyanta na yamma..

Harara ya zabga mata ba wata wata itama ta rama.
"Ni kike Harara?"

"An harare ka ɗin, in ban harare ka ba wa kake so na harara? Wallahi in na ganka wani baƙin ciki da takaici nake ji kaman in kashe kaina, in banda wawanci irin naka da daƙiƙanci taya da degreen ka za'a damfare ka kudadenmu? Gashi ka mana sanadiyar baƙin talaucin da babu ranar fita daga cikinta.."

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now