Page1

19 3 0
                                    

FARGAR JAJI
Na
Aisha Abdullahi yabo

*October/Fitattu5 2023*

*PAID.*
BOOK.

*Da sunan Allah mai Rahama Mai jinƙai. Tsira da amincin Allah su ƙara tabbata ga Fiyayyen Halittu Annabi Muhammadu RasululLah (S.A.W) da matayensa 'ya'yansa da kuma Sahabbansa da jikokinsa baki ɗaya.*

*Allah ka ƙara haskaka ƙabari da kuma ruhin Mahaifiyata Hajiya Zhara'u M. Abdullahi Yabo. Tare da Malamina Yayana M. Abubakar Abi Allah ka jajjada Rahamarka a garesu tare da dukan Musulmi baki ɗaya Saboda Alfarmar Annabi (S.A.W) Ina baran addu'a a gare su ga duk wanda ya ga littafin nan.*

*Haƙƙin mallaka (m) Aisha Abbdullahi Yabo.*

*Banyi wannan littafin don wani ko wata ba, na yi shi ne don faɗakarwa da nishaɗantar da al'umma. Don haka duk wanda ya ga wani abun ya zo daidai da rayuwar shi ba da shi nake yi ba arashi ne.*

*Gargaɗi*
*A guji juya min littafi ta ko wacce siga ba tare da izini na ba, yin hakan kuskure ne, zan ɗauki mataki ga ko waye a kiyaye sai a zauna lafiya.*

*Pej 1*

Wani irin sanyi ƙafafunta suka yi da har ta kasa ci gaba da tafiya ta faɗi tim! Kamar wacce a ka sarewa gwuawoyin ƙafa, tafiya suke yayin da take ji tamkar ba tafiya suke ba zuciyarta ciki da tsoro da tararraɗin abinda za su tarar. Suwaiba da take janye da ita ta juyo da sauri "ya haka Aisha ki tashi mu tafi tun kan ya kai ga illata maki 'ya!" Wani irin tsinkewa ta ji zuciyarta ta yi, idanunta suna zubar da hawaye ta ce. "Ji nake ƙafafuna tamkar ba nawa ba" riƙo ta tayi tare da tayar da ita tsaye tana faɗin "ki ƙarfafa wa kanki babu abinda zai faru da ita, ki yi sauri dan ba mu da lokaci."

Suna zuwa Suwaiba tayi ƙarfin halin buɗe ƙofar ɗakin tayi sa'a ƙofar a buɗe take, ta ja hannun Aisha da ta zama tamkar mutum mutumi. Suna shiga wayam babu kowa sai shirgin tufafinsa da kuma yangalallar katifarsa, kallon Suwaiba take a tsorace wacce take bin ɗakin da kallo fuskarta ɗauki da mamaki "Wallahi da idona na ga ya shiga da ita cikin ɗakin nan" durƙushe wa tayi a wajan tana kuka "na shiga uku ina to ya kai mini 'yata!"

Kamar wacce a ka tsikara da allura ta miƙe tsaye ta fita ɗakin da gudu tana ihun kiran Hussaina. "Hussaina! Hussaina ina kika shiga ne!? Innalillahi wa inna Ilaihi raji'un na shiga uku!!" Suwaiba da ta biyu bayanta ta rufe mata baki tana faɗin "kin ga daina wannan kururuwar kar ki tara wa kanki jama'a, ki kwantar da hankalinki ba mamaki abin da nake zato ba hakan ɗin ba ne ko ya aike ta ne"

"Ya aike ta kamar ya ya aike ta? To tana ina shi ɗin ina ya je!?" Hayaniyarsu ce tasa jama'ar unguwar fitowa suna tambayar lafiya, Suwaiba tayi shiru tana rarraba idanu tsoranta ɗaya kar a zo abinda take zato ba hakan ɗin ba ne ta shiga bakin 'yan unguwa uwa uba mahaifiyarsa ta tabbata masifar Inno har wajan hukuma sai ta kai ta da sunan tayi wa ɗanta sharri. "Wai me ya faru ne ku ka tsaya cirko-cirko da ku. Aisha lafiyarki kuwa ki ke wannan kukan ko mutuwa a ka yi ma ki?" Wata dattijuwa take tambayarta hankali tashe.

Durƙushe wa tayi a wajan tana kuka ta ce. "Hussaina ce Suwaiba ta gani tare da Idiris a ɗakinsa yanzu kuma mun zo babu ko ɗayan su" nan fa jama'ar wajan suka hau salati "to ke ya a ka yi ki ka ƙyale su?" a ka yi mata tambayar kusan a tare
"Uhm! Na je na kira uwar ne dan ta tabbatar kar a ce sharri nai masu" ta basu amsa jiki a sanyaye "ai kin yi wauta da sanda ki ka gansu sai ki masa magana ba wai ki ƙyale su ki je kiran uwar ba. Yanzu to ga shi nan ba a san a ina ya kaita ba"
"Wallahi Inna Mairo ban yi zaton zuwa na kira Aisha mu dawo zai tafi da ita wani wurin ba, nayi hakan ne saboda yankan hujja" tayi maganar a ruɗe.

"To ai ga yankan hujja nan kin ga ni tunda garin kiran na ta yanzu kuma sun yi sama ko ƙasa, anya kuwa kin tabbatar su ɗin ne?" Baba Isa yayi mata tambayar tare da kafeta da idanu. "Wallahi Baba yadda na gansu Ubangiji sarkin sarauta ya nuna mini Annabi hakan!"
Aminiyar Inno ta zame jiki ta je ta faɗa mata abinda yake faruwa ta fito babu ko mayafi "ina munafukar take ne kai ku gafara ku bani hanya don Allah!" Ta kutsa cikin jama'ar ta cakumi wuyan Suwaiba tana faɗin "munafuka algunguma munafuncin na ki ya tashi daga kan kowa ya dawo kaina, to ta Allah ba ta ki ba wallahi na fi ƙarfinki!"

Fargar Jaji Where stories live. Discover now