Alama he started getting Interest akan abunda suke yi, tace
"to a Tarihin wa muka tsaya ma?"

Suka ɗaga hannu ta nuna Aisha.
"Annabi Nuhu(As) inda yayi katoton jirgi saboda tseratar da kanshi da mutanenshi tare da dabbobi daga ruwan ɗufana"

Itama takbir tasa aka mata, daga nan ta cigaba musu da tarihin cikin muryarta me sanyin daaɗi, gabaɗaya hankalinshi ya Mika musu yana jin tarihin kuma yana mamaki don be taɓa ji ba, tana yi har ta zo inda ɗan Annabi Nuhu (As) ya ƙi shiga jirgin yace ze hau saman tsauni ruwa baze same shi ba amma daga karshe shima ya mutu don yana daga cikin taɓaɓɓu.

"Wani darasi kuka koya cikin wannan Tarihi?"

Nora ta ɗaga hannu tace
"Ba zaka ɓoyewa Allah ko ka guje mishi ba in de har ya tashi kama ka da laifukanka"

Takbir ta sa aka mata tare da Satan Kallonshi se suka Haɗa idanu, fuskewa yayi ya maida kanshi kan system ya cigaba da aikinshi da ya ma manta me yake yi.

Wa'azin Bin othman ta kunna musu a iPad ɗin ta inda yake magana akan sallah.

Inda ya ɗauko ta da zafinta yake cewa
"Allah madaukakin sarki cikin Suratul Maryam aya ta 59 yana cewa 'se waensu en baya suka zo a bayansu suka tozarta sallah kuma suka bi sha'awowinsu. To da sannu a hankali za'a jefa su cikin gayyah"
Allah SWT ya kuma cewa 'sede wanda ya tuba, kuma yayi imani ya kuma aikata aiki na kwarai' shima cikin Suratul Maryam aya 60."

Babban Sahabin nan ibn Abbas Allah ya qara masa yarda yace "ba wai sun wulakanta sallah bane ta hanyar barin ta ba a'a kawai sun kasance sun jinkirta yinta ne akan lokacin ta"
Kunga kenan da wannan fassarar ta ibn Abbas zamu fahimci cewa lallai waenda suke jinkirta sallah akan lokacinta wato basu yinta se lokacin da suka ga dama wannan aya akan su take, waenda suke wulakanta sallah da sannu a hankali zasu afka cikin wutar gayyah bayan mutuwar su, lallai kuma zamu fahimci cewa wanchan ayan ba tana magana ne akan kafirai bane a'a tana magana ne akan waenda suke ikirarin su musulmai ne!
Saed ibnul musayyib imamat-tabi'ina Allah yayi masa rahama yana cewa dangane da wanchan Ayar sai yace
"sune waenda basu yin sallar azahar har se lokacin la'asar, basa yin la'asar har se lokacin magrib basa yin magrib har se lokacin isha kuma ku sani duk wadda ya mutu yana a cikin wanna hali be tuba ba lallai alkawarin Allah a tattare dashi ita ce wutar gayyah!
Wato wani Kwari ne a cikin wutar Jahannama wadda yake da zurfi mai nisa  kuma zasu dinga cin wani mummunan abinci me wari da ɗaci da uquba"

Lokacin magrib da yayi ne ya sakata tsayar da Wa'azin tana me satar kallon shi, tsikar jikinshi tayi wani irin tashi idanunshi sun sauya, saboda yadda bin Othman ɗin ke Wa'azin dole In kana cikin masu aikata irin laifin hankalinka ya tashi.

Jin tana cewa yaran suje su yi Sallah ya saka shi ajiye system ɗin shima ya miƙe ya nufi ɗakin shi don yin sallar.

Da kallo ta bishi har ya shige, he's so soft and gentle sannan zama da yayi da su Philip ya hana shi tabuka komai a addininshi wadda ba laifin kowa bane laifin Mahaifinshi ne, kuskuren shi shine da ya girma ya mallaki hankali me yasa be nema sani da kanshi ba? Allah ba ze karɓi hujja akan Babanshi ba sede a karan kanshi.

Tana fata ya sauya a hankali.

Yana shiga yayi alwala ya zo ya gabatar da sallar bayan ya idar ya zauna se ya rasa Adu'ar da ze yi, be san ta yadda ake tuban ba cikin wani irin ciwo da zafin zuciya ya ɗaura fuskanshi bisa tafukan hannunshi hawaye masu zafi suka gangaro mishi.

Wasa wasa kullum tare dashi ake jin tarihin annabawa da kuma wa'azuzzuka, wani Wa'azin mufti menk da yayi akan girman uwa da kuma muhimmancin yi mata Adu'a idan ta rasu yasa ya kasa rike hawayen shi wadda a idanun Hidayat suka ganganro da sauri ta kauda kanta itama idanunta na cika da hawaye.

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now