Wani irin shakuwa ke shiga tsakaninsu da Rabecca don da ita kaɗai yake hira har yayi dariya, itace ƙawarshi a komai..

Wasa wasa be sake maganan Gidansu ba seda ya zama shahararren ɗan kwallo ba wadda be san 'R MAI NAGGE' ba se lokacin ya samu Pastor Philip yace yana so ya je gida.

Be hana shi ba ya shirya ya tafi Gembu, gidan Daadida ya fara zuwa ya kuwa ci sa'a tana wurin har lokacin rungume shi tayi tayi ta kuka a jikinshi tana mamakin yadda ya wani girma ya zama namiji sede kana ganinshi ba addini ba komai rayuwar Turai kawai..

Da kyar yake iya Haɗa hausa ya tambayi Babanshi fa.

Shiru ta ɗan yi kan tace
"Babanka babu inda be shiga ba a garin nan don nemanka saboda ya ɗauki mataki a kanka don cutar da ta shigi shanayen nan sune sukayi sanadiyar karyewar arzikinshi duk dabbobbinshi sun mutu, abinci ma gagararsu yake a gidan shiyasa ya ɗauki laifin komai ya ɗaura maka ban san ko yanzu ya huce ba amma duk sadda ze shigo nan se yayi magana marar daaɗi game da kai"

Shiru Raed yayi yana kallonta yace
"kin yafe mai kenan"

Tace
"Raed ai ko me bukar yayi min ɗa na ne Dukda ya bakanta min sossai har yanzu kuma zuciyata kuna take in na tuna sede Bukar ko ban yi fushi dashi ba ko ban mishi baki ba Allah ba ze barshi ba ina ga in na mishi baki? Ina mishi tsoron fushin ubangiji Raed"

Rumgumeta yayi yace
"ban taɓa ganin mutum irin ki ba lallai uwa uwa ce Allah ya ji kan mama"

Ta amsa da "Ameen zaka je wurin mahaifin naka ko?"

Kai ya gyaɗa ya mike ya je ɗakin da ta sauke shi yayi wanka ya sake kaya, three quarter ne as usual da shirt lokacin Daada ce ma a kanshi a murɗe ya saka ɗan kunne ga sarka a wuyan shi kana ganin shi dae zaka danganta shi da arne.

Haka ya fito duk Yadda Daadida ta so ya sauya ki yayi yace mata ma sune kayan shi gabaɗaya, ko da ya fita jama'a suka gane shi da kyar ya tsira ya samu ya je kofan gidansu.

Da sallama ya shiga, da Badi'ah ya fara cin karo se kwakwalwanshi ta fara tuna mishi karshen maganganunta gareshi tayi wani kala kaman tsohuwar da ta shekara saba'in, Zarah na tsaye tana zaginta ko sallamar shi basu ji ba seda ya sake suka juyo suna hadiye masifar da suke yi da junansu, ihu suka kurma kowacce ta ruga ɗakinta Badi'ah na cewa

"Malam! Malam!! Fito ka ga wani gardi kasurgumin kirista da ya shigo mana kai tsaye gida"

Da sauri Bukar ya fito riƙe da sandarshi yace
"kai me haka? Me ya shigo da kai cikin gidana?"

Raed yace cikin hausar shi da ta bace
"Baaba Raed ne baka gane ni ba?"

Wani ashariya ya lailayo ya maka tare da sake kiran sunanshi da karfi, Raed ya amsa se ga su Badi'ah sun fito su ma suna maimaita Raed!

Seda bukar ya tabbatar shine kan ya ɗaga sandar hannunshi ya lailaya ya muka shi, kara ya saki yana tarewa tare da cewa
"Holy christ! What the Fuck"

Aiko se bukar ya sake haukacewa
"Ni kake zagi da yaren yahudanci? Yahudu ka koma Raed? Dama Alkawari nayi duk randa na ganka se na maka dukan karya ni da kayi Muhammadu Allah ya isa tsakanina da kai, wuta bal bal wallahi kuma ka fitar min daga gida"

Badi'ah tace
"Raed ashe ridda kayi? La'ilaha illallahu wannan yanzu malam se ya ambaci sunanshi ya Haɗa da naka? Ƴaƴayenmu da suke fama da Gidajen miji ai se auren nasu ya karasa lalacewa aka ji jininmu ya zama Kaɗo"

Zarah da Naja ma suka tofa nasu albarkacin suna cewa
"kaci amanar Mairamu wallahi da tana nan na san mutuwa ce kawai sakamakon wannan bakin cikin da zaka kunso mata"

Bukar ya fashe da kuka yace
"Allah sarki Mairamu, wallahi Muhammadu ka sake jingina sunanka da ni ban yafe ba, na tsaneka! Bana so na sake ganinka cikin gidana ko kuma wallahi in yi ajalinka..."

KOWA YA GA ZABUWA...Where stories live. Discover now