Yana fita ya kira Father ya sanar dashi, a rikice yace ze bi available flight yau ya zo Paris ɗin.

Norah da Farrah jikinsu duk yayi sanyi kaman sune ba lafiyan har Aisha da kyar ta lallaɓa su suka tafi school, ita ta girka mishi abu marar nauyi da kanta ta kai mishi..

Cikin karfin hali ya mike yayi brush da ta ɗauko mishi har nan ta ajiye mishi abincin, kaɗan yaci yace ya koshi, maganin shi ta ballo ta bashi ya sha da coffee ɗin da ta hada mishi.

Tattare wurin tayi ta fice, da kallo ya bi ta har ta rufo kofan ya koma ya kwanta.

Da rana ma haka ta sake kawo mishi cikin muryarshi yace
"baki je school ba?"

Kanta kasa tace
"eh, idan na tafi babu me kulawa da kai"

Motsi me karfi yaji zuciyarshi tayi da Seda ya runtse idanu, a hankali ya buɗe yace
"thanks"

Kai ta gyaɗa, tace
"ko zaka yi wanka sir?"

Kai ya gyaɗa mata kawai, ta shiga toilet ta hada mishi ruwa me dumi ita dae taga turarukan wanka kala kala a bayin sede bata san wanne yake anfani dashi ba hakan yasa bata saka ba ta fito, ya miƙe yana dafe gini ya wuce nan ma jarumta kawai yake da karfin hali amma shi kaɗai ya san me yake ji..

Yana shiga ta hau gyara ɗakin, fes ta gyare cikin lokaci kankani, bata bari ya fito ya sameta ba ta fice daga ɗakin..

Abincin ƴan makaranta ta hau yi bata gama ba taji motsin shigowa, kuma bata ji hayaniyar yaran ba..

Da sauri ta ajiye abun hannunta ta leƙa se suka Haɗa idanu da kakkarfar mutumin sanye da wando da riga me yanayi da dogon riga baƙi da fari, se wani abu kaman mayafi da ya ɗaura saman rigar igiyar har wurin gwiwar shi, katuwar sarkar cross sanye a wuyan shi se Bible rungume a hannunshi na dama Ɗayan hannun kuma brief case.

Fitowa tayi a ladabce don bata san wanene ba tace
"u r welcome sir"

Kallonta yayi sama da kasa wannan ce kenan da Raed ke faɗa itace sabon nannyn yaran, aiko se ta bar gidan daga gani ma itace sanadiyar ciwon shi da ya tashi tunda a farkon barowansu Nigeria a duk sadda ya ga baƙin fata se ya shiga panic attack, ya zo da wata baturiya daga Amsterdam na Kasar Netherland da dama yawancin zaman shi a chan ne don hakan sallamar wannan dole.

Ba tare da ya amsa ta ba ya wuce zuwa room ɗin Raed, Seda yayi knocking kan ya buɗe yana shiga idanunshi suka faɗa bisa kanshi, da sauri ya karasa yana cewa
"Son!"

Tare da riƙe hannayenshi yana zama bakin gadon, 3 quarter ne a jikinshi da ya zazzage daga sama ya fitar da boxers ɗinshi fari Kal jikinshi ba riga yana jingine da gado yana duba phone ɗin shi ɗakin banda sassanyar kamshinshi me cike da wani ni'ima da sanyaya zuciya na musamman babu abunda yake ga sanyin Ac.

Murmushi ya saki yace
"father finally ciwona ya sa ka zo, Princesses will be happy today"

Yace
"drop that son! Me ya faru? What brings this illness back? Na tabbatar wannan baƙar fatar ce da ka ɗauko"

Kai ya girgiza yana tuna damuwarta da ciwon nashi wadda a rayuwarshi baze ce ya taba ganin makamancin tausayinshi a fuskan wani ba bayan nata, ya karanci ba karamin jimami take ba shi kuwa be san tsoronta na in ya mutu a tsukukin nan yana cikin babban hatsari bane, taimakonta da yayi kuma wadda bazata taɓa mancewa ba yasa ta ci alwashi me girma a kanshi..

"She is not father, I just had a dream abt my past!"

Yace
"then seeing her is the essence, na yi hiring nanny from Amsterdam a well reserved person ita zata cigaba da kula min da jikokina u should fire this one, and that's final.."

Da sauri ya ɗago ya kalleshi..

***

Ita kuwa ganin ya wuce kai tsaye yasa ta saka a ranta maybe dan uwansu ne, komawa kitchen ɗin tayi ta karasa duk wasu ayyukanta kan ta fito ta koma ɗaki.

Kasa bacci tayi a jiya da Tunanin wani irin rayuwa Raed yayi. Shi kuwa menene tarihin rayuwarshi haka? Wanene shi?

Kasa hakura tayi ta lalubi inda ta rubuta landline number ɗin Daadida ta saka kira..

Ringing na karshe aka ɗaga
"Assalamu Alaikum jikata..!"

Ɗan murmushi hidayat tayi tace
"Wa'alaikumussalam warahmatullah ina yini daadida?"

Daadida tace
"mu a wurin mu har yanzu kwana ne, Awa ɗaya da ƴan mintuna ya rage mu shiga yinin"

Murmushi hidayat ta sake tsohuwar akwai barkwanci tace
"to ina kwana"

Tace
"lafiya ƙalau Alhamdulillah ya kuke duka? Ya wannan sarkin miskilancin? Wai fushi yake dani, in kira in kira ya ƙi dauka ja'iri kuma wallahi ba zan fasa gayamai gaskiya ba ko mutuwa ze yi"

Hidayat ta ɗan yi murmushi tace
"yana kwance bashi da lafiya"

Daadida tayi salati ta sallame tace
"Allah sarki, Allah ubangiji ya bashi lafiya ya sa kaffara ne"

Hidayat ta amsa da
"Ameen"

Se ta ɗan yi shiru cikin shirya kalaman da zata yi akan tsari tace
"Daadida kin roke ni a kan tallafar rayuwar uban gidana kuma na ɗau alkawari, sede duk inda na duba babu wata mafita har se in na san wanene Muhammad Raed, yaya rayuwar shi take wani giɓi ne ya samu yake buƙatar plaster se na san ta inda kuskuren ya faro kan in yi tunanin hanyar bi wurin gyara"

Daadida ta sauke numfashi me nauyi tace
"Hidayat shi ba giɓi bane a rayuwarshi, tubali ne bashi dashi kinga toshewa da plaster ba ze taɓa yiwuwa ba in har ana so yayi karƙo se an rushe an sake sabon dakakkiyar tubali, ina nan ina muku Adu'a, ina sadaka ina saukar Alqur'ani da yardar Allah mafarkin da na jima ina yi a kanki nake saka ran tabbatarsa don haka zan faɗa miki wanene Muhammad Raed...."

#Vote
#share
#comment



                 🖤Gureenjoh🖤

KOWA YA GA ZABUWA...Onde histórias criam vida. Descubra agora